ABARI YA HUCE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABARI YA HUCE COMPLETE

ABARI YA HUCE COMPLETE HAUSA NOVEL

Duk inda ranshi yake idan ya yi dubu, to ya baci. Ba ta taba yi mishi musu a rayuwarshi irin na wannan lokacin ba. Ya rasa abin da zai mata YA HUCE… Gaba daya ya soma tunanin bokon da ya barta tana yi ne ya sanya ta raina shi… Wannan ne karo na farko da ya kai kararta wajen Habibu tun bayan aurensu. Habibun ya ce, ya kawo mishi ita.

Daga ita sai Yaya Habibun a babban falonshi, don Amirun da ya kawota bai zauna ba ya wuce ofis wajen Daddy. Dina na kicin tana kacaniyar shirya abinci.
Habibu ya ce
“Mairo me nake ji haka? Wai mijinki bai isa ya sa ki abu ki yi ba?
Idan ke ba kya son ‘ya’yan, to shi yana so. Muma muna so, me kike nufi da ba zaki yarda a yi miki aikin ba?”
Ta fashe da kuka, ta ce
“Da da ne ya ce na yi abin da yake so, ai zan yi ne, ba tare da kowa ya ji ba. Amma ni ma yanzu ban san me yake nufi da ni ba. Babu magana mai dadi tsakanina da shi sai hantara. Kuma yadda ya ke nunawa kamar ta karfi yake so na haifo mishi dan, sannan ni gaskiya tsoro nake ji, lafiyata kalau inje a jagwalgwala min mahaifa”.
Habibu ya ce
“Likitoci ba za su yi miki karya ba Mairo. Maganar canzawarshi sai ki yi mishi uzuri, yanayin rayuwar kenan, wata rana a sha zuma, watarana a sha madaci! Ba kullum ne mutum yake kasancewa cikin dadin rai ba!”.

Da kyar Habibun ya rarrashe ta, ta yarda za su je ayi aikin. Ranar litinin Dr. Ma’u ta yi mata aikin.


Tsawon shekara guda har da doriya, babu wani bayani, wato ba abin da ya sauya bayan yin aikin. Babu ciki ba alamarsa.
Dai-dai lokacin da ta kammala rubutun ‘project’ dinta na kwalin master, sabida kwazon da ta nuna kai tsaye suka ba ta gurbin zama daya daga cikin malamansu, wato ‘lecturing’ a jami’ar Abuja.
Mairo ta debi kudi masu yawa, ta dankawa Yaya Habibu aka soma ginin makarantar firamare da sakandire a kauyen Gurin-Gawa. Sannan ta dauki sauran gaba daya ta mallaka mishi halak-malak, bayan ta warewa Baffa nashi kason.
Habibu ya saida gidanshi na kasar America da wasu manyan kadarorinsa ya tada kafadar (Habib Bank) wanda ke gaf da durkushewa. Cikin taimakon Allah sai al’amuran suka soma dai-daita. Amma a ranshi ya dai karbi kudin Mairo ne kawai bai ce mata komi ba, sai dai cikin ranshi ya kudurce juya mata zai yi.


Hanan Abdulwahab, diyar kanin Hajiya ce, wato Uncle din Amiru da ke garin Gaya. ‘Yar kimanin shekaru ashirin da hudu, kyakkyawa ce matuka, kuma tana da irin tsagin su Amiru a gefen hagu da dama na fuskarsu.
‘Yan asalin garin Gaya ne su ma, don da Babanta da Hajiya ubansu daya. Mahaifinta tsohon soja ne, wanda ya rike manya-manyan mukamai a aikin soji, har zuwa matsayin da yake kai a yau, wato Major Genaral Abdulwahab Gaya.
Gaba dayan karatun Hanan tun daga firamare har jami’a ta yi shi ne a garin Lagos, inda mahaifinsu ya yi aiki a wancan lokacin. Daga baya da ya yi ‘retire’ suka dawo garin Kaduna da zama, inda suke zaune a halin yanzu.
Direban Hajiya Mr. Kademi ne ya je ya dauko Hanan daga filin jirgi, wadda ta sauka karfe hudu dai-dai na yammacin ranar ta Laraba.
Hajiya ta yi mata kyakkyawar tarba bayan ta rungumeta tana lale da diyarta. Kamar yadda Hajiyar ta nemi izinin mahaifin Hanan di n kan ya barta ta zo ta yi mata kwana biyu.

Sun baje a falon Hajiya suna labari, Hanan ta ce.
“Ina labarin brother, yanzu yaran shi nawa ne Hajiya?”
Hajiya ta kyabe baki, ta ce.
“Babu ko daya”.
Hanan ta yi murmushi, ta ce.
“To ai kin san Turawa ne, watakila ba su shirya fara tarbar ‘ya’yan ba”.
Cikin rashin walwala Hajiyar ta ce.
“Ke raba ni da abin haushi, kada ke ma ki bata min rai yanzun nan. Turancin yaci abu kazan ubansa. Ba wani tsarin iyali, juya kawai ya je ya auro”.
Kwanan Hanan biyu a gidan, amma ba su hadu da Amiru ba, sabida sanda yake shigowa gaida Hajiyar da safe ita ba ta tashi daga barci ba, sabida dai Hanan ‘yar hutu ce ta karshe.
A rana ta uku ne da ya shigo Hajiya ta je har dakin da ta sauka wanda ya kasance dakin su Rayyah ne kamin su yi aure, ta tasota ta ce ta zo su gaisa da Yayanta. Ta ba ta wani farin kwalli ta ce, ta zizara a idonta, ta yi duk kokarin da zata yi ta tabbatar sun hada ido.
Hanan ta cika da mamakin mene ne dalilin Hajiya na yin hakan? Sai dai kuma ba ta jin zata iya kin bin umarnin Hajiyar.
Tsaye ya ke a baranda yana amsa kiran Habib cikin wayarshi, a lokacin da Hanan ta fito falon. Ya juya baya hannunshi daya dafe a bayanshi, yayin da ya yi amfani da dayan wajen rike wayar.
Hanan ta tsura mishi idanu, wani al’amari mai karfi na fizgarta. Rabonta da Amiru tun wani zuwa da ya yi Kaduna gaida mahaifinta a lokacin yana Washington. Zuwa yanzu ya kara girma da haiba. Duk wasu kamanni na ingarman namiji ya mallake su, kuma kyakkyawa na karshen-karshe. Ya zama ‘giant’ mai wani irin kyawun halitta na burgewa da ban mamaki. Irin mazan da ba kowacce lafiyayyar mace ce zata iya dauke ido a kansu ba.
Gwiyoyinta suka yi sanyi, kuzarin jikinta ya kare, wata irin soyayyar Amirun na tsirga zuciyarta. Ba ta iya ta dauke ido a bayanshi ba har ya juyo.
Da farko kallo daya ya yi mata, amma ya rasa dalilin da ya sanya ya kasa dauke idonshi a kanta. Don sai ya ganta kamar Mairo, idanunta, bakinta da karan hancinta duk sun rikide sun koma na Maironshi sak! Har ya ke jin yafi son wannan Mairon, akan wadda ya baro a gida.
Sakon Hajiya ya yi aiki sosai, ya hada wata matsiyaciyar soyayya, mai wuyar fassarawa.
8/8/21, 1:23 PM – Kawata: 55

Tsayin watanni biyu Alh. Abdurrahman na jinyar tilon dansa, ya na kwantar masa da hankali ta hanyar bashi misalai da al’amuran rayuwa kala-kala. Don ya yaye wa kanshi damuwar daya sanyawa zuciyar shi. Yana kuma karantar abubuwanda ke faruwa a cikin gidanshi musamman Hajiya A’isha daya digawa gundumemiyar ayar tambaya. Sabida yadda ta fita hayyacinta da rashin lafiyar Amiru, sai surutai take mai tonawa kai asiri, wani zubin ta hada da su Nina tace su suka angizata, ta zazzagesu tayi musu mugun kalami tana cewa sun cuce ta.
Bai tambayeta komai ba, kuma bai tambayi Amiru mai yasa ya saki Mairo ba. Wanda rayuwar sa ke hannun Allah. Dr. Fred yana zuwa gida akai-akai yana kula dashi. Ya ki yarda a maida shi New-York. Yace da Daddy in ma mutuwarce, to yafi so ta dauke shi a dakin da yayi rayuwa da Mairo.

A yau Ambasadan Malaysia yazo ganin sa, ta dalilin Habibu da Amiru Daddyn Dina da Alhaji Abdurrahman suka kulla abota. Alh. Abdurrahman yayi masa kyakkyawar tarba, shikansa saida ya zubda hawaye ganin halin da Amirun ke ciki. Ya koma Malaysia cike da alhini inda ya tarar da Mairo da tata sabuwar matsalar har yau ba sauyi.
A wannan satin da surutan Hajiya suka ishi Alh. Abdurrahman, yayiwa ‘ya’yan shi mata gabadaya waya, na ciki dana waje, yace yana so su hallara a ‘family meeting’ ranar asabar mai zuwa. Sannan ya kira Alh. Abdulwahab Baban Hanan shima yace yana so Hanan tazo ranar asabar. Alhaji Abdulwahab wanda ke cike taf da fushin sakin da Amiru yayiwa Hanan sati daya da aure ya gintse fuska yace
“ince ko lafiya? Bayan an riga an saketa?”
Daddy yace lafiya kalau, ‘meeting’ zasu yi tare da ita. Ya gaya mishi bai san abubuwanda suke faruwa a gidan ba, yana so ya sani ne, inda halin gyara ayi gyara. Yace Hanan zata zo albarkacin ka, amma babu batun gyara. Don dama Hanan tana da mai sonta tuni, mutunci da ‘yan uwantaka aka diba aka bawa Amiru. Tunda kuma yace baiyi, to Allah ya hada kowa da rabonsa na ALHERI.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button