ABARI YA HUCE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABARI YA HUCE COMPLETE

ABARI YA HUCE COMPLETE HAUSA NOVEL

Jikin Mairo ya kara yin la’asar, amma sai ta dasa wa ranta ta rabu da wadannan yaran ta yi abin da ya kawo ta. Ta ajiye litattafanta ita ma ta tube uniform tasa na hostel irin wanda taga sun sanya, ta nufi famfunan da ta ga ana alwala, ita ma ta yi ta nufi masallacin da ta ga ana shiga da sauri ta samu jam’in sallar azahar.
Da aka fito yunwa ta addabe ta, ta soma tunanin ta je ta kwada kwadon kwaki sai ta ji wata senior na fadin a fita ‘dining’ za’a rufe hostel. Ta dinga maimaita kalmar ‘dining’ a ranta, ko mene ne? Ta ga dai kowa fita yake yi sai ta bi bayan wasu yara ba tare da sun san binsu ta ke ba, har zuwa wani katon dakin cin abinci inda ta ga dalibai a zazzaune kowa da filet dinshi ana ta cin abinci.
Yawun bakinta ya tsinke, ta bi layin da ake bi a karba ita ma ta karba, jallof din shinkafa ce da yankan nama biyu da soyayyar ayaba (plaintain) sala uku. Ta zauna ta ci ta koshi, ta sha ruwa ta yi hamdala ta mike ita ma ta nufi hostel ta kwanta a gadonta don ta huta zuwa la’asar.
Da aka yi sallar la’asar kuma suka koma aji zuwa karfe shida. Haka dai ta yi ta bin abin da ta ga ana yi, har lokacin barci.

A sannan ne ta samu damar kwashe kayanta da ke cikin (Ghana Must Go) ta jera a loka, kamar yadda ta ga kowa ya yi. Yaran nan makotanta suka fito da wani irin abu cikin kwali da ba ta taba gani ba suna ci, suna korawa da lemon gwangwani suna hira da Turanci, suna kallonta, ita da kullin kayan kuli-kulinta suna ta dariya. Duk ta bi ta sha jinin jikinta, amma ba ta daga kai ta kalle su ba, ta jika ramarta cikin ‘yar robarta ta ajiye akan lokarta tana jira ta jiku ta kwada da kuli.
Tana ganinsu har lekowa suke da kai suna leka robar ta, amma ragowar jama’ar da ke dakin ba ruwansu da ita, kowa gararin gabansa yake yi. Ta rasa dalilin wadannan yara na sa mata ido da wulakanci a gare ta, daga baya ta fuskanci daya sunanta Nabilah, daya kuma Kausar.
Ta kwada ramarta ta ci ta koshi, ta sha ruwa ta kwanta a katifarta da ko zanin gado babu. Ta rufa da zanin atamfar Innarta, wadancan yaran kuwa irin bargonta da hedimasta ya cinye suka rufa da shi. Hatta filon ya dauke ya cinye saboda rashin tsoron Allah irin nasa. Aka yi (light-off) na gabadayan hostel din, ta shafe jikinta da addu’o’i ta kwanta.
Washegari da aka yi sallar asubah ta ga kowa yana bin layin wanka, don haka ita ma ta bi ta yi wankanta ta yi sallah a masallaci tare da Imam. Daga nan aka tafi aji.
Suna shiga aji ta ga mutanenta sun dauke bencin gabadaya sun maida shi wurin da ba kowa sun zauna, sun kuma kira wata yarinya sun zaunar da ita a wajenta. Ta rasa inda za ta zauna, ta koma karshen ajin ta sanya littafinta daya a kasa ta zauna akai. Zamanta da kamar minti biyar Uncle din ajin ya shigo. Yana ta jefa ido ya hango Mariaman da ya kwana ya tashi da tunaninta jiya, amma bai ganta ba.
Gabadaya ajin aka mike, ita ma sai ta mike kamar yadda suka yi, suka hada baki gabadaya suka ce “Good morning Uncle”.
Ya ce, “Morning class, how are you all?”
Suka sake hada baki gaba daya suka ce “We are fine Uncle”. Sannan ya yi umarni da a zauna.
A sannan ne ya hangota makure a can layin karshe kamar mujiya, kuma a dandaryar kasa. Bai ce komi ba ya bude rajista ya yi kiran lambar kowa, ya amsa, sai a karshe ya ce “No. 40”. Shiru ba a amsa ba, a lokacin ya gane lambar Mairo ce, sai ya ce, “Mariama daga yau ke ce no.40”.
Ta ce “To”.
Ya rufe rajistar ya dinke fuska sosai, ya ce
“Kausar!”
Ta amsa, “Yes Uncle”.
Ya ce “mene ne dalilinki na janye benci ki hana Mariama zama?”
Ta yi shiru ba ta amsa ba.
Ya dubi dalibar da suka zaunar a wajen, “Ke Laila ina wajen zamanki? Me ya kawo ki nan?”
Ta yi saurin mikewa ta koma wajenta.
Ya ce “Kausar fito nan”.
Ta fito tana gatsina ita a dole ga ‘yar masu kudi. Saura kadan ya zabga mata mari, sai dai ya yaki zuciyarshi ga yin hakan, ya ce ta fita waje ta yi kneel down, har zuwa lokacin break.
Ta cika ta yi fam, kamar balam-balam, dama ga ta buleliya. Ta zobara baki, ta ce “Ai ba ni kadai na janye bencin ba, har da Nabilah”.
Nabilah ta ce “Wallahi Uncle babu ruwana, ita ce ta ce wai ba zata zauna da billager ba”.

Bai yi mamaki ba, sai ya bude murya yana tambayar ‘yan ajin “Shin dama akwai banbanci tsakanin musulmin kauye da musulmin birni?”
Suka ce “A’ah Uncle”.
Ya ce “To me ye laifin wannan yarinya da kuke kyamarta?”
Wasu daga ciki suka hau matsawa suna cewa “Ta zo ta zauna a kusa da mu”.
Amma Uncle sai cewa ya yi, babu inda zata zauna sai bencin su Nabilah, don haka idan Nabilah da Kausar baza su zauna tare da Maryama ba, sai dai su koma gidan ubansu.

Mairo dai na sauraron ikon Allah. Tana tunanin yadda ta ke abar so a wurin Innarta da Babanta, amma wai yau ake takaddama akan inda za ta zauna sabida ita an ga alamar ba ta da arziki.
7/28/21, 10:59 AM – Buhainat????: 30

A lokacin ta ji wata zuciya na shigarta (determination) akan rayuwa. Ta alkawarta wa ranta idan ilimi na kawo arziki, to zata neme shi ko don ‘ya’yanta. Za ta nemi ilimi har sai ta ga karshensa, idan har ana gani. Ba zata so a yi wa danta irin wannan wulakancin ba. Uncle ya lura Mairo kuka ta ke yi, sai zuciyarsa ta karye. Don haka tunda ya gama kiran lambar sai ya fita, bayan ya tabbatarwa Kausar kada ta sake ta bar kneel down din da yasa ta har sai ya dwo.
Malamin maths ya shigo ya fara ba su darasi, Mairo ta tattara hankalinta akan malamin gabadaya, ba ta damu da hararar da Nabilah ke mata ba. Ya gama ya fita, sai ga Uncle ya dawo wanda kuma shi ne yake daukarsu darasin Turanci.
Yana koyarwa, amma rabin hankalin sa na kan Mairo. Ya lura sabanin ragowar ‘yan ajin, Maryama ta ba shi dukkan ‘attention’ dinta, da wani muradi cikin kwayan idanunta. A zahiri wannan yarinya bakauyiya ce lakadan, amma ga dukkan alamu, ba haka Allah Ya yi nufin barinta ba.
Ya kammala darasinsa ya ba da aiki ‘Essay Writting’ mai take guda uku, ya ce kowacce ta zabi wanda za ta iya yin sharhi a kansa. A rubuta a kawo masa washegari. Hankalin Mairo ya tashi, domin dan ilimin nata bai kai nan ba. Magana ce ake so su rubuto da harshen Turanci akalla shafi daya da rabi na littafi.
Aka kada kararrawar fita break, amma Mairo ba ta yi niyyar fita ba. Ta kurawa aikin ‘assignment’ dinta ido tana tunanin ta inda za ta bullo. Ba ta ankara ba ta ji wani sassanyan kamshi na dukan hancinta da kuma alamun zaman mutum a bencin gabanta. Ta dago a hankali tana kallonsa, Uncle ne.
Ya ce “Yaya dai Maryama, kowa ya fita cin abinci, amma ke ban ga alamar kina da niyyar fita ba?”
Ta sadda kai cikin kankanuwar murya ta ce
“Ina tunanin yadda zan yi aikin da ka bayar ne”.
Ya yi murmushi ya ce “Aiki ne kuwa mai sauki, amma ga wanda ya gane tambayar. Wacce tambaya kika dauka a ciki?”
Ta sunkuya tana kara nazarinsu, ta ce “Ina ganin ta daya za ta fi mun saukin amsawa, tunda daga karkara na ke, ‘Yadda ake bikin sallah a karkararmu”.
Ya yi murmushi, ya ce
“Ni kuwa sai na ga tambaya ta biyu zata fi dacewa da ke ‘Ranata ta farko a sakandire’, za ki kawo ‘points’ sosai wanda zai taimaka ki yi ‘scoring’ maki mai yawa. Kinga sauyin abubuwa da dama, a zuwanki babbar makaranta. Haka ne ko ba haka ne ba?”
Ta yi murmushi, wanda ya lotsa kumatunta hagu da dama. Akwai wani asirtaccen kyau a tare da Mariama, wanda rashin gyara da rashin gogewa ya boye shi. Yarinya ce kamar diyar Larabawa, sai dai fatarta a dafe ta ke, kamar an shafa mata shuni, wanda kai tsaye ya banbantata da sauran yaran makarantar.
Ta ce “Haka ne Uncle. Na gane cewa, ashe mu ba mutane ba ne, ababen kyama ne ga wasu jinsin al’ummah. Abin dariya ga wadanda Allah Ya yiwa falalar rayuwa. Ban san cewa ni ‘yar talaka ba ce sai yanzu, tunda kuwa ban taba neman abin da zan ci na rasa ba, sai na dauka iyakarta ke nan. Ashe akwai masu shi fiye da ni, amma idan da ace ni ce a matsayin mai shi din, ba haka zan yi wa mara shi ba!”.
Mamakin kalaman karamar yarinya kamar wannan ya kama shi. Sai dai ya kula magana ta ke tun daga karkashin zuciyarta, ba wai tunaninta ba ne.
Ya ce “Mariama!”
Ta dago ta dube shi, amma ba ta amsa ba.
Ya ce “Ina son ki sa wa ranki cewa, ba duka mutanen da kika tarar halinsu daya ne ba. Kowa da kika gani a duniya da irin halayyarsa. Wani yasan darajar kansa, yasan ta mutane, wani bai san darajar kansa ba, bai san ta mutane ba. Wani yasan darajar kansa bai san ta mutane ba.To wannan ba cikakken mutum ba ne, kuma shi ne wanda Allah Ubangiji Ya yi alkawarin dankafar da shi a duniya da lahira sabida girman kansa. Da zarar ka yi tunani ko ya ya cewa, kai wani ne, to kai ba kowa ba ne a wurin Ubangiji.
Sabida haka a yadda kika dau kan naki a ba kowa ba, ci gaba da hakan. Amma kada ki yarda da cewa, sai wun fi ki ne. Ido biyu gare su, kunne biyu, kafafu biyu, hannaye biyu, ke ma su gare ki. To akan me za ki yi tunanin sun fi ki? Wanda ya fi ki kawai shi ne wanda ya fi ki tsoron Allah!”.
Jikinta ya yi sanyi, ranta ya yi fari. Tana dubanshi da kyawawan idanunta, ta ce “Uncle kana nufin ni ba abun kyama ba ce?”
Ya girgiza kai “Ko daya Maryama. Da za ki daure ki fidda su a gabanki ki yi karatu sosai ki dinga gyara kanki, sai kin fi su kyan gani. Ko a yanzu haka kin fi su, gyara suka fi ki. Ba kawa kika zo nema ba, ilimi kika zo nema, irin wanda suka zo nema. To akan me za ki damu da su? Ai abu daya za ki damu da shi, shi ne ki dage ki ga cewa ba su fi ki kokari ba”.
Ta yi murmushi ta ce “Uncle kana da kirki, sai na ke jinka kamar Yaya Habibu. Shi ma haka yake yi min irin maganganunka. Da zai zo ya ganni a makarantar nan, ban san irin farin cikin da zai yi ba”.
Ya ce “Yaya Habibu yana ina yanzun? Ni kuwa inje in gaya masa, ga ki a babbar makaranta”.
Ta washe baki ta ce “Ayyah, yana da nisa, yana karatu ne a kasar waje, amma komi nake yi sai in yi ta ganin kamar yana kallona, sabida shi ne ya dage, ya sani a makaranta”.
Ya ce “Ni kuwa gani na dage da yardar Allah sai kin yi karatun da Yaya Habibu zai dawo ya yi alfahari da ke, amma hakan ba zai yiwu ba sai da goyon bayanki Maryama, wanda ba komi ba ne da ya wuce perserbearance (jajircewa) da ba da himma”.
Ta sake yin murmushi har kumatunta suka lotsa, ta ce “Na gode Uncle, kuma na yi maka alkawarin I’ll persebere”.
Ya yi mata tafi guda daya ya ce “Good Maryama, ina neman alfarmar ki rike ni a matsayin Yaya Habibu”,.
Wani farin ciki ya bayyana a fuskarta, ta ce “Kenan ka yarda na rinka kiranka da Uncle Habibu?”
Murmushi ya yi, “A’ah, UNCLE JUNAIDU. Sunana Junaidu Galadanchi”.
Ta ce “Galadanchi?”
Ya ce “Eh, kin santa ne?”
Ta ce “A’a, ban taba ji ba ne. Garinku ne Galadanchi ko sunan Babanka ne?”
Da alama Maryama matambayiya ce, kuma matambayi ba ya bata. Hazakar yaro na da alaka da yawan tambayarsa (curiosity).
Ya ce “Galadanchi karamar unguwa ce a cikin birnin Kano. Sai dai tarihinta mai girma ne ga Kanawa. Duk wani Ba-Kano ya san Galadanchi, sannan mu ‘ya’yan cikinta muna alfahari da ita da kasancewarmu ‘ya’yanta.
A Galadanchi ne aka fara samun Dr. a ilimi a jihar Kano. Haka idan kika bi tarihin manyan ‘yan bokon Kano, da mayan malaman Jami’ar Bayero, wadanda suka fito da jihar Kano a tsakanin jihohi ‘yan uwanta, to duk ‘yan Galadanchi ne. sannan gasu da kyau, ga Alkur’ani da Tajwidi a cikin kansu”.
Ta ce “Ina fatan wata rana, in ziyarci Galadanchi”.
Murmushi ya yi “Insha Allahu za ki je Galadanci Maryama. Yanzu dai jeki ci abinci kamar sauran dalibai, idan kun fito ‘pref’ da yamma sai ki rubuta aikin gobe ki kawo mani”.
Ba musu ta mike ta nufi kofar fita. Bai daina kallonta ba har sai da ta kule ya daina ganinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button