FITAR RANA

FITAR RANA 2

Tun sassafe suka shirya suka bar garin jos suka dau hanyarsu wanda tadauƙesu tsawon awanni uku zuwa hudu ana tuƙasu,Jan ƙura irin nakan titin ƙauye wanda baiga darajar samun gyara ko kwalta ba shiya bule jikin bus din gwamnati daya sauƙesu a baki titin wani kauye acan kusa da garin kaduna ana ce dashi mararrabar saminaka, masu saida fresh fresh kayan lambu da fruits sun cikke bakin titi anata hada hadan kasuwanci da saida da sayarwa,anan motar tasu tsaya ta sauƙesu suka sassauka kusa da wani mai saida karas da ganyayyaki,tafe wasimé take cikin nitsuwa dauƙe da jakar kayanta tana bibiyar matar data zame mata tamkar uwa da uba a bainar duniya wacce take ƙira da innono kotace mata anono,anma asalin sunan matar Fatsuma,saidai anfi saninta da hajiya fatu mai tuwo sabida tsohuwar sana’arta ne dafa abinci tana siyarwa danta samu kudi,Allah ya dafa mata ta shahara a manyan ma’aikatar gwamnati da manyan makarantu a matsayinta na chief cook,wato shugaban masu kula da harkokin girke girke na manyan makarantu da ma’aikata,tun tanacin kuruciyarta take wann sana’ar har shekarunta yaja ta tsofe, fatu mai tuwo farace sol tana da murmurarren jiki,itana kowace,kowa yasanta da halayyar son ƙulla zumunci da kyautatawa, da iya taimakon mutane, da son tallafawa naƙasa da ita koda kuwa bata sanka ba,fatu bazaurace mijinta ya rasu,amma tana da danta kwalli daya tilo datake kiransa da suna”Qasimu” wanda aynxu har ya kammala karatunsa na jamia yay kudin rufin asiri yay aurensa a garin kaduna,inda ya ajiye mata daya da dansu kwalli daya namiji.

Tsawon lokaci tabarsu acikin aminci Suna rayuwarsu acan ita kuma ta shiga uwa duniya yawon gwagwrmaya akan abunda ta saba na taimakon yan uwa marasa ƙarfi da galihu da kuma sada zumunci da dangi da abokai.

Halayyarta na son mutane ya jawo take da mutanen data sani bila adadin, ta kuma shaƙu da dumbin mutanen ta akusan duk inda taje,bata da wani alaƙa ta jini kona yan uwantaka da hassan mahaifin wasimé,iyayensa yan gudun hijirane daga ƙasar somalia,baban sa da mamansa sun gudo ne,lokcin da tsohon cikin sa suka yada zango agarin ringin gani,da sukazo garin bamai kallonsu bare ajega taimakon su,wata rana kwasam saiga fatu.anan ta tsincesu a bakin gaɓa lkcin ciwon naƙuda ya turneƙe mahaifiyar hassan,ita tayi ruwa tayi tsaki ta taimakesu har aka haifeshi lpya, aka samai sunan sa Aliyu haidar,sukamasa inkiya da hassan.,sosai iyayen hassan suka shaku da fatu,alokaci ƙalilin suka saba,suka dawo tamkar wasu yan uwanjini sabida yadda tariƙesu take taimaka musu da zuciyarta daya take kuma taimakonsu da dukiyarta,Bayan watanni sha shida Allah yay ma mahaifyar hassan rasuwa,mahaifin sa kuma yabi bayanta randa ta cika kwana arba’ain da rasuwan,fatuce ta dauƙi dansu Aliyu ta cigaba da rainonshi tamkar danta na cikinta harya girma yay aure ya auro matarsa badiatu.Saidai izuwa yau kuma ga yadda qaddara ta juya tarihin rayuwarsu komi ya zamto tamkar wani mafarki.

Hannun wasimén taja suka shiga wani madaidaicin gida ginin block wanda baida wani tazara da bakin hanyar da suka sauƙa,kai tsaye innono ta kutso kai cikin gidan da sallama a bakinta”Asallama alaikum masu gidan suna nan kuwa? wata dattijuwar mata ce a tsakar gidan tana ƙalkale saman cementi da tsintsiyar laushi a hannunta, jin muryan innonon yasata dagowa da fara’a akan fuskanta tana cewa..wa’alaikin sallam oyoyo oyoyo maraba da xuwa anononmu,barkanku da isowa…innono ta sauƙe ajiyar xcya”laraba ina mutan gidan haka naji koina yadau shiru kamar wani makabarta,tana kkrin karban kayansu tace suna nan sun dan zaga yin ta’axiyane a makwafta amma yanzu zasu dawo, kushigo ciki kuzauna kusha ruwa,lale marhaba da zuwa..daga fadin haka ta wuce dakinta agaggauce cikin sauri ta aje kayansu sann ta dawo hannunta dauƙe da babban tabarma,akan cementin kofar dakinta ta shimfida musu suka zazzauna,kujerar tsakar gida taja itama ta zauna
“Sannu,Ina kwana? Wasimé ta furta da sanyin muryanta mai cike da alkunya tana satan kallon matar

Matar tay murmushi ta dubeta ganin ta kyakkwaya saitaji ta shige mata har cikin ranta a bugu daya, tace lpya lau yan mata masha Allah,daganan wasime bata kara ce uffan ba ta maida kallonta ƙasa ta kuma nitsu sabida bata taɓa xuwa wani waje ba arayuwanta duk sai tanajin kanta daban,matar tana satan kallonta tana washe baki cikin rada tace,uhumm innono kar ace nayi azarbabi karde wannan ƴar itace amaryan namu?Kyabe baki innono tayi murya ƙasa kasa tana murmushi tace”Kede laraba da son jin gulma,aikya barni in huta kafin a tsunduma cikin sana’a ko,dariya matar tayi mai dan ƙara”kinsan goshi amare baya boya,masha Allah yarinya shar a ƙauyen fulani wann ai amaryace,innono ta kyabe baki”..ni ynzu ina naga ta gulma yunwa fa nakeji ni banko ƙarya ba ,laraba ki hanzarta ki kawomin abinci kyaji duk wani shauran bayani daganan,miƙewa matar tay cikin tsokanarta ta wuce kitchen ta soma kkrin kawo musu abun taɓawa,lafiyayyan tuwon dawace da miyar kuka taji manja da busasshen kifi yanzun nan dama ta kwashesu ba ako yi rabo ba,a dan tray din silver ta saka musu tare da ruwa snn ta ajeshi agabansu
,nan da nan da innono suka sauƙa akai itada wasiménta datake cin abincin a hankli kamar bazata ci ba,kafin nan mata, da yan yara yara har sun daddawo sunciƙƙe gidan da surutansu,tray tray na tuwon nan an sakoshi agaba anajan lomomi
Ana hira,yara yan fici fici irin bini in bika nan kawai in ka kirga zasu iyakaiwa ashirin,iyayen ne a tsakiya su hudu casss kowaccce ta haɗe uwar ciki da teba, kallo daya zaka musu kasan ƙunika akeyi agidan gadan gadan,banda sa’oin juna da wanda suka ba juna watanni akwai wanda aka turasu ƙaratun allo acan yobe state,”Anono anono surutu ne da hatsaniyan tade tade ya cikke tsakar gidan,manya da yara Kowa na burin ta saurareshi,sai can da magidancin gidan ya shigo sannan kowa ya nitsu aka dan sarara daga nan Wani shiru gidan ya dauƙa, dan Kaf yaran gidan sun watse kowa ya fita neman nakai,aka bar manyan sukadai agida tareda wasimé data laɓe agefen innono tayi shiru tanajin tattaunawarsu wanda mafi akasari akanta ne.

Ta gama lura kamar aure ake shirin yi mata ba itama,ita ko ajikinta dan bayau ta soma ji ko ganin aure ba,zaman su a sansanin fulani yasata fahimtar komi,daga ya mace takai shekaru 9 xuwa sha 11 to a al’adance ma ta isa ayi mata aure,halan itama takaine,taga duk kawayenta nacan ma an bijiro da maganan aurensu duk dama bata san menene shi auren ba amma haka dai suke cewa.

Dattijon dayake bayani bazai wuce shekaru 60 ba, yace wa matayen sa da suke zazzaune agefensa akan da su shirya tarban ɓaki dan Lokacin isowar waliyann angon kawai ake jira angama shirye shiryen komi afannin amarya,Innono tacigaba da masa godiya tana saka masa albarka da tare da danta Qasimu daya amince a aurawa jikarta dahiru aure da wasimé,”

Dama can angaya mata danta Qasimu yay sa’ar aure duk dama tasan ƙabila ya auro amma ta lura kamar matarsan tana iya bakin kokarinta wajen yin musu adalci,sosai innono taji dadi da suka bata hadin kai ta bawa jikarta dahiru auren wasimé badon komi ba kodan sabida ta inganta rayuwrta na nan gaba.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button