Sheikh Zakzaky ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da BBC Hausa ta yi da shi.
Ya bayyana abinda zai yi musu idan su kayi ido huɗu
Da aka tambaye sa ko me zai yi idan su kayi ido huɗu da shugaba Buhari da gwamna El-Rufa’i, sai ya kada baki yace:
Zan ce musu su kammala ayyukan da su ka fara ne, su cika ladan su, na son kashe ni
Malamin ya kuma musanta zargin da ake musu na cewa a lokutan muzahara, mabiyan sa na sanya mutane cikin ƙunci ta hanyar tsare hanyoyi, inda yake cewa ba tsare hanya su ke yi ba, amfani su ke yi da ita kamar yadda kowa ke da yanci da damar yin amfani da ita.
Ya ƙara da cewa duk tsawon shekarun da su ka kwashe shi da matar sa a gidan yari su ne suka ciyar da kan su, saɓanin abinda gwamnati ke cewa itace take ciyar da su.
An tsare Zakzaky da matarsa a gidan kaso
Idan baa manta ba dai, Sheikh Zakzaky da matarsa Zeenat, sun shafe shekara shida a tsare a gidan kaso bisa zarginsu da laifuka da suka haɗa da tayar da hankali da kuma kafa gwamnati cikin gwamnati a Jihar Kaduna da ke a arewacin Najeriya.
Sheikh Zakzaky ya ƙara da cewa yana da fata da burin komawa Zariya a nan gaba domin ci gaba da ayyukansa da yake yi a baya, musamman idan lafiyar jikinsa ta samu.
Asali LabarunHausa
[ad_2]