ABU MALEEK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABU MALEEK COMPLETE

ABU MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

Ar蓷o ne a gaba Abu Maleek na bin bayansa a hankali cike da Zallar nutsuwarsa irin ta 拼ar 拼an sarakai, wanda jinin sarauta ya gama ratsa su,
Wata bukka mai kyau wacce aka cikata da kayan ado irin nasu na Fulani, Ar蓷o ya sanya kansa cikin Bukkar, Abu Maleek kam tsayawa yayi cak,yana mamakin ta inda zai shiga bukkar gaba 蓷aya bukkar a tsakiyar cikinsa ta tsaya, baya tunanin cikin bukkar ma zai Wada cesa, waro manyan gajiyayyun idanunsa yayi waje ganin yadda Ar蓷o ya sunkuya sosai kamar zai dafa 茩asa kafin ya samu ya shiga cikin bukkar, cije lips 蓷insa yayi yana fesar da iska daga cikin bakinsa, a hankali cikin kuma 茩asaitacciyar muryarsa mai cike da kamala ya ware softness lips 蓷insa masu taushi da 蓷an kauri cikin 茩asa da murya very slow yace.
“Goodness”
Ya fa蓷a yana janye idanunsa daga kan Bukkar, Ar蓷o dake ciki ne yaji Shiru ba茩on mahaukacin nasu bai shigo ba, ya sanya shi le茩o dakai ganin Abu Maleek yayi a tsaya hakan ya sanya yace.
“Ai shaii ka rarrafa ka shigo”
Ar蓷o ya fa蓷a yana mai tsare 茩irjin Abu Maleek da kallo saboda wani ba茩in zane daya hango, kwance a saman faffa蓷an 茩irjin nasa,
Ganin hakan ya sanya Abu Maleek ha蓷e rai kafin ya 蓷auke idanunsa yana fa蓷in.
“Wicked and stringy man”
Ya fa蓷a a fili amma Murya 茩asa, Murmushi kawai Ar蓷o yayi ba tare da yace komai ba,
A hankali ya sunkuya sosai, cikin rashin Sa’a kansa ya bugu da gefen bukkar, kwa蓳e fuska yay sosai kamar zai sanya kuka, a hankali cikin Muryar ta蓳a ra yace.
“Auchhhiii! Daman salon mugunta akai wannan guntuwar abar, an san ai ba茩i zasu iya zuwa, mtwss!”
Ya fa蓷a yana 茩arasa shiga cikin Bukkar duk ya marai-raice fuska kamar zai kuka, ganin ya shigo yasa Ar蓷o fita tare da 茩warya a hanunsa, Not too long ya dawo da 茩waryar cike da kindirmo mai kyau, wanda yake zalla babu algus,
Kindirmon yabi da kallo kafin a hankali ya ha蓷e 茩afafuwansa waje guda, bai son Kindirmon sabida sam bai yarda da tsaftar mutanan garin ba,
Amma idan ya茩i sha bai san abinda zai samu nan gaba yaci ba.

Zama Abu Maleek ya gyara tare da 蓷aukan ludayin Dumar ya sanya cikin 茩wayar kindirmon da aka kawo masa, ganin yadda Kindirmon yake da haske sosai ga wani irin kyau da yayi masa a idanu, ya sanya a hankali cike da nutsuwa ya 茩ara na蓷e 茩afarsa kana ya 蓷ebi Kindirmon yakai bakinsa, da sauri ya ja idanunsa ya rufe saboda wani da蓷i da kuma gar蓷i daya ratsa cikin kunnuwansa, shan Kindirmon kuma ya taso mata da duka yunwar daya keji a haka yaci gaba da sha, sai da yasha fiye da rabi kana ya ajjiye,
Murmushi Ar蓷o yayi yace.
“Birnin Bera kace ko, haii daga wannan rugar sai Birnin Bera tafiyar kwana guda ce rakk, amma ha蓷arin tafiyar yafi na shekara guda”
Kallonsa Abu Maleek yayi sai kuma ya 蓷an ta蓳e baki, yana tsotse la蓳蓳ansa wanda har yanzu da蓷in Kindirmon ya茩i barin saman harshansa,
Lumshe idanunsa yayi harga Allah matsu ya samu maganin ya koma Benin kana ya ga King Tunde Muhammad Jalal ya samu lafiya daga nan kuma sai koma Madrid baki 蓷aya, ya samu ya huce dukkan gajiyarsa a can!.

Kai tsaye waje Ar蓷o yayi yana zuwa ya nufi wajan Lami蓷o ba tare da yayi magana ba, yaja hannun Lami蓷o zuwa wata bukka,
“Meka fahimta dan gane da wannan ba茩on?”
Ar蓷o ya tambayi Lami蓷o yana share zufar data karyo masa,
Gaba 蓷aya Abu Maleek ya gama firgita Ar蓷o da kwarjininsa, har baya iya tsayawa inda yake saboda tsoro,
Lami蓷o ne yaja numfashi kafin yace.
“Ban fahimci komai ba, amma dai kamar bashi da lafiyar 茩wa茩walwa, duba da yanayinsa da kuma shigarsa, ga kuma yadda kansa gaba 蓷aya ya茩i tsayawa waje guda”
Jinjina kai Ar蓷o yayi kafin yace.
“Haka ne,amma akwai lauje cikin na蓷i, mene ya kawo sa wannan garin? A cewar sa dai wai Birnin Bera zashi, amsar magani kuma babu wani magani da ake bayarwa, uhm! Kasan babu wanda ya ta蓳a shiga Birnin ya fito da ransa, saboda ha蓷arin da mutanan garin suke da shi, kasan mutanan tamkar kuraye haka suke, su kuma kalar tasu maitar a fili suke cin shan jinin Mutum, kuma da sun cijeka shikenan kai ma harbo wannan maitar”
Cike da gamsuwa Lami蓷o ya jinjina kansa kafin yace “haka ne, amma wannan mutumin kamar da sammu a jikinsa, ina kallonsa naji hankali na ya茩i kwanciya, ina ganin mu taimaka masa mu fa蓷a masa gaskiya zaifi”
Murmushi Ar蓷o yayi domin shi ya gama tsara Abinda zaiyi,
Juyawa yayi tare da nufar bukkar da Julde ke kwance har zai shiga sai kuma ya fasa ya juya yana mai sakin murmushi.

Cikin dare Abu Maleek yana kwance tunani fal ransa, idan ka ganshi zaka 蓷auka da gaske bacci yake amma idanunsa biyu,
茦ara yaji kamar na ringing 蓷in waya daga bakin bukkar, mamaki ne ya cika masa zuciya domin yasan babu yadda za’ai a samu waya a wannan garin, garin da ku service bashi dashi, gashi ya lura ko addini basu iya ba,
Ware fararan idanunsa yay yana da 蓷an kasa kunne muryar Ar蓷o yaji yana fa蓷in.
“Sir trying to remembered it, nayi 茩o茩arin ganin na aikata hakan but it’s difficult to me, gaskiya i can’t do that I’m sorry!”
Shiru yayi yana mai 茩ara juya gudun kada wani yazo ya riskesa a haka, jinjina kai yay kafin yace.
“That’s great job, any way duk yadda mukai I’ll get back to you”
Ya fa蓷a yana mai kashe wayar tare zuge ta zugen wandonsa, a cikin aljihun 3gauther ya sanya wayar kana ya shigo cikin bukkar,
Da sauri Abu Maleek yaja idanunsa ya rufe mamaki ya hanasa tunanin komai bare ya fahimta, Tabbas akwai abinda yake faruwa a wannan Rugar mene shi, yaya akai Shugaban Rugar Mahinjo ya iya sarrafa harshe haka? Da wannan tunanin bacci ya 蓷auke sa.

Washe gari waje ya samu mai kyau ya 蓷an watsa ruwa a tsaye gudun infection,
Bayan ya shirya cikin wasu fararan kayan Fulani masu kyau, ya fito daga cikin Bukkar yana mai 蓷an fesar da huci daga cikin bakinsa,
Ar蓷o dake gefe yace.
“Har ka fito?”
Kallon Mutumin yayi a ransa yace “munafuki”
A zahiri kuma idanunsa kawai ya lumshe tare da bu蓷e su,
Gyara tsaiwa Ar蓷o yayi kafin ya kalli Abu Maleek yace.
“Haii ka bu蓷e kunne da kyau kaji ba茩o, babu wani magani da ake bayarwa a Birnin Bera, gaba 蓷aya mutanan garin masu shan jini ne, a tarihi ma babu wanda ya ta蓳a zuwa koda 茩ofar garin ne balle ya shiga, duk wanda yace kazo garin to bayanka ya keson gani Aradon Allah”
Kallonsa A.m yake domin yana son ya fahimci asalin Maganar, babu Abinda Ya gani a idanun Ar蓷o sai zallar tarin gaskiya tsagwaronta,
Juya idanunsa yayi kana ya mirgina kansa gefe yace.
“Are you sure?”
Ya fa蓷a yana cije bakinsa dan nan da nan yani kansa ya fara sarawa, sosai maganar ta dakesa, mene ya sanya akai hakan? Wane ya sanya Malamin Alaafin ya fa蓷i haka, lallai Tabbas biri yayi kama da mutum dalilin daya sanya kenan suka hana ya duba King Tunde Muhammad Jalal sabida suna tunanin zai iya fahimtar wani abu, Tabbas dole ya koma Benin ba tare da 蓳ata wani lokaci ba.

A can Alaafi Kanzaf kowa, tsaro aka 茩ara mai tsananin gaske, cikin Alaafin yayi shiru baka ganin komai, ko jin motsin wani face na securities, tsaron da aka 茩ara yafi na kullum, babu mai shiga babu mai fita, Al’amarin daya tayarwa da jama’ar Kanzaf hankali kenan,
Kana kuma ya sanya masu tsoro da tarin zullumi a cikin zu茩atansu,
Yau wajan sati guda kenan da tafiyar Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal kenan, tafiyarsa kuma ta haifar da tarin matsaloli wanda ba’a san ta inda suke kunna kai ba.
Salimerh ce zaune a saman bed 蓷in ta tana sanye da kayan bacci dark brown panjamas, masu kyau,
Waya ce ma茩ale a kunanta tana sauraran abinda Junaid yake fa蓷a mata,
Daga can 蓳angaren Junaid gyara kwanciyar sa yayi a hankali cikin 茩asa da murya yace.
“My princess kina son zuciyata ta buga saboda soyayyyar ki da tayi min yawa ko? I can’t control my self idan ina wajanki ko su kike ba aikata abinda ba Shikenan ba?”
Ya fa蓷a yana jan numfashi, girgiza kai Salimerh tayi kafin tace.
“Ba haka bane, ni aure a yanzu ta kurani zai, ina karatu akwai tarin abubuwan da yake gabana masu muhimmanci”
Uhm kawai ya iya cewa kafin yace.
“Kenan baki sona?”
Girgiza kai tayi tace “i love You, ina sonka Junaid but…,”
Ka tseta yayi da “if you really love me, then marry me”
“I’ll” da sauri yace “then when? Kinga stop pretending gobe zanwa Otun magana ya nemi Agba Akin (CHIROMA)domin a nema min Auranki, I’m tried My princess ki shirya zama matar Junaid soon”
Bai jira tayi magana ba, ya katse kiran yana mai mamakin yadda sam bata fahimtar son da yake mata,
Ajjiye wayar tayi domin ita sam babu maganar aure a tsarinta yanzu, tana big issues dalilin daya ta za蓳i karanta Law kuma 蓳angaren criminology justice.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button