ABU MALEEK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABU MALEEK COMPLETE

ABU MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

Washe gari da sassafe sukaci gaba da tafiya ba tare da sunci komai ba,
Tunda suka tafi babu wanda yace komai, yana janye da ita da igiya wajan sallar Zhur sukaiwa Rugar Mahinjo tsinke,
Lokacin gaba 蓷aya kowa yana cikin Rugar ana hutawa tare kuma da tarin Alhinin rashin ganin Julde wanda tsirari daga cikinsu suke.
Cikin rugar Abu Maleek yabi da kallo yana kalla kuma yaji kansa ya sara da 茩arfin gaske, zuciyarsa ta harba da 茩arfi,
Hakan nan ya samu kansa cikin tarin fargaba kasancewar sa ba komai ne kai bayyana a fuskarsa ba ya sanya ko alamun tsoro bai nuna ba,
Fitowar Lami蓷o kenan daga cikin bukka idanunsa ya sauka akan Julde da sauri yace.
“Ar蓷o!! Ar蓷o!! War, War Ar蓷o”
Jin Muryar Lami蓷o ne ya sanya Jikinta ya shiga rawa nan da nan idanunta ya fara zubar da hawaye shkknan yanzu zasu kasheta, abinda take rayawa a zuciyarta kenan,
Yana yana cikin bukka hannunsa ri茩e da wata paper wacce babu wanda yasan da ita wajansa, sabida babu wanda ya iya karatu bare rubutu a cikin Rugar.
Yana tsaka da duba paper ne yaji Muryar Lami蓷o yana kwala masa kira da dukkan muryarsa, da sauri ya 蓳oye paper kana ya fito,
Abinda idanunsa suka gani ne ya sanya shi zare ido,
Julde a hankali tayi bayan Abu Maleek tana 蓳oye fuskarta domin a yanzu shi kawai take tunanin zai taimaka mata,
Gyara Ar蓷o yayi kafin yace.
“Ardon Allah 茩arya kake, shaiii kaci Ubanka ka biya mu Naggen mu, Lami蓷o kawo mana ita nan ka tara mana jama’ar gari”
Jin haka ya sanya Julde sanya ihu a gigice kuma ta sanya dukkan hannayenta a saman ququn Abu Maleek tare da 蓷ura fuskarta a tsakiyar bayansa ta 茩an茩amesa, da sauri ya runtse idanunsa sabida sarawar da kansa yayi masa ga wata halbawa da zuciyarsa tayi masa,
Kasa motsawa yayi da sauri kuma yasa hannunsa ya dafe kansa saboda yadda yaji Julde ta 茩ara….

ABU_MALEEK NA KU茒I NE KIJI TSORAN ALLAH KADA KI TAFI LAHIRA DA ABINDA BA NAKI BA, IT’S 500 VIA 0116886423 SULAIMAN NA’IMA S UNION BANK 08119237616
1/1/22, 18:59 – Aisha Adam: Nimcyluv 27-28
“Ga maciji nan”
ya fa蓷a cikin 蓷an 蓷aga Murya yadda za taji abinda yace, kai tsaye kuma magen ta sauka saman kanta,jelar magen tayi kwance a wuyanta,
Wani kalar numfashi Julde taja saboda laushi da kuma sanyin jikin magen daya ratsa fatar Jikinta,
Tsoran da yayiwa Julde yawa ne ya sanya ta fita cikin hayyacinta tun daga wannan Numfashin data ja bata sake motsawa ba, balle taja wani Numfashin,
Sosai take da jin tsoro abu ka蓷an ke firgitar da ita, sweet da itama ta firgita, da sauri ta sauka a jikin Julde ta bu蓷e baki tare dayin 茩ara kana ta nufi wajan Abu Maleek da gudu, tana zuwa ya dur茩osa ya 蓷auke ta tare da rungome ta, yana shafa bayanta a hankali, kana cikin ransa yace.
“Bana fa蓷a maki ba? Gashi nan tsoro ya hanaki magana”
Ya fa蓷a yana shigewa cikin bukkar gaba 蓷aya bai lura da halin suman da Julde ta shiga ba.
Barkido dake can tsaye yayi saurin 茩arasawa inda dake tare da dur茩osawa, inda take ganin bata numfashi ya sanya ya 蓷an firgita, da sauri kuma ya mi茩e babu jimawa ya dawo 蓷auke da ruwa a hannunsa,
Yayyafa mata ruwa yayi, cikin Sa’a kuma ta sauke ajjiyar zuciya tare da sanya kuka ta 茩o茩arin Mi茩ewa tsaye Jikinta sai rawa yake.
“Julde, nine Barkidon ki”
Ya fa蓷a yana yana 茩o茩arin ri茩e hannunta, zamewa tayi ba tare data bashi damar ri茩e hannun nata ba, cikin shagwa蓳a fuska tace.
“Shine ya tsorata ni yayi tafiyarsa ko?”
Barkido da bai fahimci maganar taba yace.
“Waye kuma? Me yayi maki?”
Ya tambaye ta, yana mai 蓷an juya sai dai baiga kowa ba, turo baki tayi tana sakin ajjiyar zuciya kafin a hankali cikin Muryar rauni tace.
“Wannan ba茩on mutumin, Allah bashi da kirki gashi da miskilanci”
Cike da tausayawa Barkido yake kallonta ganin duk ta tsorata har bata iya 蓳oye tsoran dake zuciyarta, gashi nan ya fito ya bayyana sosai a saman fuskarta,
茦asa yayi da murya yace “Ayyah kiyi ha茩uri kinji? 茦ilan bai sani ba”
kwa蓳e fuska tayi tace “Allah nima sai na rama, nasan ramawa yayi”
Jimm Barkido yayi zuciyar nayi masa zafi sosai, kafin ya ha蓷iye abinda ya keji yace.
“Kin san shi ne? Me kikai masa da har zai rama yanzu?”
Ya tambaye domin zuciyarsa bata aminta da maganar ta ba,
Hannayenta ta watsa masa irin ohuu 蓷in nan sai kuma tace.
“Ihu nayi masa akai fa, kuma ai tsolo ruwa inaji”
Jinjina kai yayi alamar gamsuwa, kafin ya gyara zamansa sosai yace.
“Julde ina son muyi magana, nasan ba lallai ki fahimta ba, amma dole zan fa蓷a maki, kafin nan ina 茩ara baki hqr akan abinda nai maki, nasan Ubangiji ne ya rama maki, ta hanyar sanya mini soyayyyar ki mai tsanani a Zuciyata, wallahi Aradon Allah ina sonki kuma Auranki na kayi”
Maganar taji kamar ba zata, tasan cewa bata ilimin soyayyya bata san yaya take ba, dan haka bata kawo wannan tsarin rayuwarta, ita idan aka barta da ranta da lafiyarta da kuma abinda lafiyarta zata samu, ya wadatar da ita, sai kuma ilimi bata 茩aunar zamanta a cikin jahilci,tana bu茩atar samun 拼anci kamar kowa, duk ta san abune mai wahala ta samu wannan saboda lalurar rashin ganinta.
Ganin tayi shiru ne kuma ya sanya Barkido yaji zuciyarsa ta buga baya fatan yayiwa Julde dole akan ta susa, yasan Tabbas zai sameta saboda shi 蓷in jarumi ne zai iya jure dukkan wata bulala da Za’ai masa a wajan sha蓷i.
“Kina jin tsoro na ko? Saboda abinda muka aikata a gareki? Ban san komai ba Julde duk abinda nayi sanyani akai, ban kuma san dalilin daya sanya Ar蓷o yace nayi hakan ba, kiyi hqr ina 茩ara baki hqr amma ina sonki da gaske, zan baki farin ciki bazan ta蓳a bari wani ya cutar dake ba”
Shiru tayi tana nazarin kalaman sa saboda Allah ya bata 茩wa茩walwa duk da cewa bata gani amma tana iya fahimtar kalaman mutum har ta fahimci inda zan can ya dusa,
Ajjiyar zuciya ta sauke kafin tace “zaka sani makaranta? Ina sonyi karatu sosai domin na samu hanya mafi sau茩i wajan kare rayukan jama’a da kuma gano inda mugwayen mutane suke”
Abu Maleek dake can bayansu yana 蓷an shan mango a hankali yana jin gaba 蓷aya zaman garin ya ishesa, ya 蓷an ta蓳e bakinsa saboda yana jin abinda suke fa蓷a kasancewar yana da saurin ji kamar maciji, cikin ransa yace.
“Daman kalar zaran dole sai kalar yadin, kayan Shirme sai shirmammu”
Ya fa蓷a yana jan tsaki tare da juya zuwa cikin bukkar,
Barkido 茩ara kallon Julde yayi sosai kafin yace.
“Karatu kikeso?”
Da sauri ta 蓷aga masa kanta tana zare yatsarta daga cikin baki, Murmushi yayi yace.
“Na maki al’茩awarin indai kika aure ni ko mene kikeso zan maki, wannan al’茩awarin na 蓷auka”
Washe 茩ana nan jerarrun dafaffun ha茩uronta tayi cikin sanyin murya da kuma 蓷an farin cikin daya shigeta tace.
“To Shikenan”
“Kin Aminci zaki auran?”
Ya fa蓷a yana mai kallon saman 茩irjinta tare da sauke ajjiyar zuciya, kafin tayi magana yaji daga bayansa ance.
“Jarumtar ka itace zata tabbatar cewa ka dace da auranta ko kuma a’a, ka daina saye zuciyarta domin zaka cutar da ita, saboda ba kai ka 蓷ai kake sonta ba ka mari 茩arfinka ya baka ita”

Labbo ya fa蓷a yana dire sandar hannunsa, Mi茩ewa Barkido yayi kafin ya fuskanci Labbo yace.
“Idan batu kake na Jarumtar ka 蓷auka Julde ta zama tawa, idan kana magana 茩arfi ne kasan cewa wajan ka tarar, idan maganar saye zuciya kake wannan sa茩o ne daga zuciyar da take so zuwa zuciyar da akeso ina fatan ka fahimta?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button