ABU MALEEK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABU MALEEK COMPLETE

ABU MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

Abu Maleek na ku蓷i kada ki karanta bada izini na ba, kiji tsoran Allah idan kina bu茩ata kiyiwa wannan number mgn 08119237616
1/1/22, 18:59 – Aisha Adam: Nimcyluv 27-28
“Ga maciji nan”
ya fa蓷a cikin 蓷an 蓷aga Murya yadda za taji abinda yace, kai tsaye kuma magen ta sauka saman kanta,jelar magen tayi kwance a wuyanta,
Wani kalar numfashi Julde taja saboda laushi da kuma sanyin jikin magen daya ratsa fatar Jikinta,
Tsoran da yayiwa Julde yawa ne ya sanya ta fita cikin hayyacinta tun daga wannan Numfashin data ja bata sake motsawa ba, balle taja wani Numfashin,
Sosai take da jin tsoro abu ka蓷an ke firgitar da ita, sweet da itama ta firgita, da sauri ta sauka a jikin Julde ta bu蓷e baki tare dayin 茩ara kana ta nufi wajan Abu Maleek da gudu, tana zuwa ya dur茩osa ya 蓷auke ta tare da rungome ta, yana shafa bayanta a hankali, kana cikin ransa yace.
“Bana fa蓷a maki ba? Gashi nan tsoro ya hanaki magana”
Ya fa蓷a yana shigewa cikin bukkar gaba 蓷aya bai lura da halin suman da Julde ta shiga ba.
Barkido dake can tsaye yayi saurin 茩arasawa inda dake tare da dur茩osawa, inda take ganin bata numfashi ya sanya ya 蓷an firgita, da sauri kuma ya mi茩e babu jimawa ya dawo 蓷auke da ruwa a hannunsa,
Yayyafa mata ruwa yayi, cikin Sa’a kuma ta sauke ajjiyar zuciya tare da sanya kuka ta 茩o茩arin Mi茩ewa tsaye Jikinta sai rawa yake.
“Julde, nine Barkidon ki”
Ya fa蓷a yana yana 茩o茩arin ri茩e hannunta, zamewa tayi ba tare data bashi damar ri茩e hannun nata ba, cikin shagwa蓳a fuska tace.
“Shine ya tsorata ni yayi tafiyarsa ko?”
Barkido da bai fahimci maganar taba yace.
“Waye kuma? Me yayi maki?”
Ya tambaye ta, yana mai 蓷an juya sai dai baiga kowa ba, turo baki tayi tana sakin ajjiyar zuciya kafin a hankali cikin Muryar rauni tace.
“Wannan ba茩on mutumin, Allah bashi da kirki gashi da miskilanci”
Cike da tausayawa Barkido yake kallonta ganin duk ta tsorata har bata iya 蓳oye tsoran dake zuciyarta, gashi nan ya fito ya bayyana sosai a saman fuskarta,
茦asa yayi da murya yace “Ayyah kiyi ha茩uri kinji? 茦ilan bai sani ba”
kwa蓳e fuska tayi tace “Allah nima sai na rama, nasan ramawa yayi”
Jimm Barkido yayi zuciyar nayi masa zafi sosai, kafin ya ha蓷iye abinda ya keji yace.
“Kin san shi ne? Me kikai masa da har zai rama yanzu?”
Ya tambaye domin zuciyarsa bata aminta da maganar ta ba,
Hannayenta ta watsa masa irin ohuu 蓷in nan sai kuma tace.
“Ihu nayi masa akai fa, kuma ai tsolo ruwa inaji”
Jinjina kai yayi alamar gamsuwa, kafin ya gyara zamansa sosai yace.
“Julde ina son muyi magana, nasan ba lallai ki fahimta ba, amma dole zan fa蓷a maki, kafin nan ina 茩ara baki hqr akan abinda nai maki, nasan Ubangiji ne ya rama maki, ta hanyar sanya mini soyayyyar ki mai tsanani a Zuciyata, wallahi Aradon Allah ina sonki kuma Auranki na kayi”
Maganar taji kamar ba zata, tasan cewa bata ilimin soyayyya bata san yaya take ba, dan haka bata kawo wannan tsarin rayuwarta, ita idan aka barta da ranta da lafiyarta da kuma abinda lafiyarta zata samu, ya wadatar da ita, sai kuma ilimi bata 茩aunar zamanta a cikin jahilci,tana bu茩atar samun 拼anci kamar kowa, duk ta san abune mai wahala ta samu wannan saboda lalurar rashin ganinta.
Ganin tayi shiru ne kuma ya sanya Barkido yaji zuciyarsa ta buga baya fatan yayiwa Julde dole akan ta susa, yasan Tabbas zai sameta saboda shi 蓷in jarumi ne zai iya jure dukkan wata bulala da Za’ai masa a wajan sha蓷i.
“Kina jin tsoro na ko? Saboda abinda muka aikata a gareki? Ban san komai ba Julde duk abinda nayi sanyani akai, ban kuma san dalilin daya sanya Ar蓷o yace nayi hakan ba, kiyi hqr ina 茩ara baki hqr amma ina sonki da gaske, zan baki farin ciki bazan ta蓳a bari wani ya cutar dake ba”
Shiru tayi tana nazarin kalaman sa saboda Allah ya bata 茩wa茩walwa duk da cewa bata gani amma tana iya fahimtar kalaman mutum har ta fahimci inda zan can ya dusa,
Ajjiyar zuciya ta sauke kafin tace “zaka sani makaranta? Ina sonyi karatu sosai domin na samu hanya mafi sau茩i wajan kare rayukan jama’a da kuma gano inda mugwayen mutane suke”
Abu Maleek dake can bayansu yana 蓷an shan mango a hankali yana jin gaba 蓷aya zaman garin ya ishesa, ya 蓷an ta蓳e bakinsa saboda yana jin abinda suke fa蓷a kasancewar yana da saurin ji kamar maciji, cikin ransa yace.
“Daman kalar zaran dole sai kalar yadin, kayan Shirme sai shirmammu”
Ya fa蓷a yana jan tsaki tare da juya zuwa cikin bukkar,
Barkido 茩ara kallon Julde yayi sosai kafin yace.
“Karatu kikeso?”
Da sauri ta 蓷aga masa kanta tana zare yatsarta daga cikin baki, Murmushi yayi yace.
“Na maki al’茩awarin indai kika aure ni ko mene kikeso zan maki, wannan al’茩awarin na 蓷auka”
Washe 茩ana nan jerarrun dafaffun ha茩uronta tayi cikin sanyin murya da kuma 蓷an farin cikin daya shigeta tace.
“To Shikenan”
“Kin Aminci zaki auran?”
Ya fa蓷a yana mai kallon saman 茩irjinta tare da sauke ajjiyar zuciya, kafin tayi magana yaji daga bayansa ance.
“Jarumtar ka itace zata tabbatar cewa ka dace da auranta ko kuma a’a, ka daina saye zuciyarta domin zaka cutar da ita, saboda ba kai ka 蓷ai kake sonta ba ka mari 茩arfinka ya baka ita”

Labbo ya fa蓷a yana dire sandar hannunsa, Mi茩ewa Barkido yayi kafin ya fuskanci Labbo yace.
“Idan batu kake na Jarumtar ka 蓷auka Julde ta zama tawa, idan kana magana 茩arfi ne kasan cewa wajan ka tarar, idan maganar saye zuciya kake wannan sa茩o ne daga zuciyar da take so zuwa zuciyar da akeso ina fatan ka fahimta?”

“Aradon Allah 茩arya kake, Julde Matana ce nine zan aureta, idan baka shirya ba ka shirya sha蓷i Arado jikinka zai fa蓷a maka”
Juyawa yayi ya kalli Julde saboda yaga yaya yanayin ta yake, tana nan zaune ta cure waje guda sai faman juya idanu take da dukkan alamu fata fahimci inda zan can yake ba,
茒auke idanunsa yay kafin ya juya ya kalli Labbo yace.
“Na da蓷e da shiryawa, ina maka fatan samun nasara”
Yana fa蓷in hakan ya juya zuwa cikin wata bukka, bin bayansa Labbo yayi da kallo, kafin ya maida idanunsa zuwa ga Julde dake zaune tana aikin tsotsar yatsarta,
Kamar zai mata magana sai kuma kawai ya juya tare da nufar bukkar Mahaifiyar sa.

Abu Maleek na shiga cikin bukkar kowa zamewa yayi tare da cire rigar jikinsa, Lumshe idanunsa yayi yana da蓳e baki kafin ya ware la蓳蓳anta cikin gajiyawa yace.
“Kaya duk wari, Uhmmm”
Ya fa蓷a yana cilli da rigar tare da sanya hannunsa ya saman 茩irjinsa ya shiga shafa 茩wantaccen gashin 茩irjinsa, tunani ne fal zuciyarsa a yanzu kuma tunanin Mami Shine yafi damun zuciyarsa, ina take? Wane ya 蓷auke ta? Mene ya sanya Adams cewa shi ne ya 蓷auke mahaifiyar su? Mene ya sanya yake zarginsa? Wannan tambayoyin sune suka tare a cikin zuciyar Abu Maleek, amma sam bashi da amsar su, gaba 蓷aya yaushe ya dawo garin ma? Tafin hannunsa ya sanya a saman goshinsa ya shiga 蓷an murza goshinsa a hankali yana sauke numfashi, taune le蓳ansa yayi yana zuciyarsa na tsananta bugu, a hankali ya sauke wata wahalalliyar ajjiyar zuciya tare da sanya hannunsa a dai-dai tsakiyar 茩irjinsa ya 蓷an matse wajan,
Idanunsa ne ya sauka a saman zanan dake 茩irjinsa har zuwa 茩asan cibiyar sa, lumshe idanunsa yay a hankali ya furta.
“Where are you Mami? Ina nothing without you, ya rabbi! Come to our family Mami”
Ya 茩are zan can yana 蓷an runtse idanunsa da wannan tunanin kuma bacci ya 蓷auke sa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button