
A can wajan ruga kowa tuni Ar蓷o ya sanya aka buga tambura na sanarwar, kafin kace me dukkan jama’ar dake cikin Rugar maza da mata yara da manya sun halarci kiran Ar蓷o,
Bayan kowa yazo ne Ar蓷o ya gyara zamansa tare da fuskarta jama’ar Rugar yace.
“Kamar yadda muka sani a al’adance idan mane ma sukaiwa yarinya yawa, akwai wata hanya domin kawo mafita da kuma samun sau茩i wajan ware mutum guda wanda ya amsa sunan Jarumi da zai zama miji ga wannan Yarinyar haka ne?”
Gaba 蓷aya suka amsa da
“Eh”
Gyara zama yayi yace “akan maganar Julde ne, Yaro Labbo yaga Julde yana so, ga wannan yaro nawa Barkido yaga Julde yana so, kowa kuma ya cancanci a bashi a auranta, bisa wannan dalilin ya sanya za muyi abinda muka saba a al’adance, ma’ana zamu gabatar da SHA茒I tsakanin ma nema biyun, wanda ya samu nasara shikenan ya zamu auran wannan yarinya”
Gaba 蓷aya sukai na’am da zan can Ar蓷o kafin 蓷aya daga cikinsu yace
“Yau she ne za’a gabatar da SHA茒IN?”
Ar蓷o na Mi茩ewa tsaye yace.
“Babu jira ai, dukkan mane man su shirya gobe za’a gabatar da komai”
Wani Murmushin jin da蓷i Barkido yayi yana mai Mi茩ewa tsaye tare da shigewa bukkar Adda Manga (Senior sister) domin ta fara shigarsa daman ya da蓷e da shiri saboda zuwan irin wannan ranar, shima Labbo wajan iyayensa suka nufa nan kowa ya fara shiri,
Abu Maleek kam dake bacci mai san meke faruwa ba, yana jiyo hayaniya sama虏 dai amma baya fahimtar komai,
A wannan ranar babu wanda ya kwanta bacci gaba aka fara shirin sha蓷i sai tsuma samari biyun ake wanda suka kasance ma nema aure ga Julde wacce itama bata san abinda ke faruwa ba, ta bukka tana bacci yatsarta sanye cikin bakinta.
A can Alaafi kowa yammaci ne mai 蓷auke da wata sassanyar iskar dake Ka蓷awa, alamu ne dake nuna cewa yanayin damuna zai fara, duba da yanayin yadda samaniya ta cika da gajimare mai duhu da kuma jaa, gaba 蓷aya weather ta sauya sai iska ake garin yayi kyau sosai ga wasu kukan tsuntsaye dake tashi a hankali.
Junaid ke tafiya cikin kuzari da kuma izza, yana sanye da black 蓷in shadda mai kyau,
Sosai fuskarsa ta fa蓷a蓷a da Murmushi tunda yaji sa茩on cewa an bashi auran Salimerh duk sanda ya shirya ya fito, dalilin fitowar sa ma tun jiya yake kiran Number bata answering shiyasa ya yanke shawarar zuwa ya sameta.
Yan tafe bayi da barori na gaishesa, a haka ya isa cikin sashin Queen Ayoola tana zaune saman wata lallausar kujera mai kyau, ga hadinkai sai fifita suke mata duk da uban sanyin dake tashi a parlon nata,
Ga wasu kuma na matsa mata 茩afafuwansa ta, wasu kuma ma jera mata kayan motsa baki,
A bakin 茩ofar parlon ya tsaya tare da neman iso, wajan Queen Ayoola,
Ba jima aka bashi damar shiga, bakinsa 蓷auke da sallama ya shiga,ganin mai shigowar ne ya sanya Queen Ayoola yin wani 茩awataccen Murmushi tare da bawa Junaid umarnin shiga, bayan sun gaisa ne Junaid yace.
“Mai Kanzaf da Alaafi baki 蓷aya Salimerh fa?”
Cikin jin da蓷i maganar ta Junaid tace.
“Tana sashin Bola, kaje mana”
Mi茩ewa yayi yana fa蓷in “godiya nake, na barki lafiya Jagorar Alaafi”
Da Murmushi tabi bayansa da kallo, kai tsaye kuma shashin Bola ya nufa, bayan anyi masa iso ne ya shiga,
Suna zaune a parlo suna cin abinci idar da sallar su kenan ya shiga,
MALEEK dake zaune saman sofa yayi saurin tashi yana sakin kuka tare da nufar inda Bola take zaune,
Murmushi yayi yace.
“Maleek ka girma till now bak daina gudun mutane ba?”
Bola da ajjiye spoon 蓷in hannunta tare da Mi茩ewa bayan tasha ruwa tace.
“Ai na rasa irin Maleek, bashi da yarda gaba 蓷aya”
Ta 茩are maganar ta kama hannunsa tare da nufar side 蓷in ta,
Salimerh abinci ta keci a hankali ganin bata da niyyar yi masa magana yasa shi mi茩ewa tare da jan kujera ya zauna yana mai kallon fuskarta yace.
“Congratulations Madam!”
Juya idanunta tayi tace
“For???”
Murmushi yayi tare da fara cin abincin plate 蓷inta yace “uhm soon zamu zama miji da mata”
Daga yaci gaba da janta da Shira.
Washe gari bayan tayi shirin tafiya Makaranta ta nufi Sashin King Tunde Muhammad Jalal, tana zuwa ta samu Oumuu-Ayman zaune a gefe tana masa sannu, zama tayi cikin damuwa tace.
“Yaya jikin nasa yanzu Oumuu-Ayman?”
“Jiki Allahamdulillah Salimerh”
Ta fa蓷a a hankali gudun kada hayaniya ta damesa, Shiru tayi tana kallon Mahaifin nata, kafin tace.
“Wai wanne irin ciwo ne haka? Ace har yanzu babu sau茩i”
Ajjiyar zuciya Oumuu-Ayman ta sauke tace
“to yaya za’ai da ikon Ubangiji Auta? Muci gaba da addu’a Allah ya dawo da Zaki lafiya”
“Ameen” tace Idanunta na sauka a bakin King Tunde Muhammad Jalal ganin wani farin yawo na fita daga cikin bakinsa yasa a hankali ta sanya yatsarta ta shafo yawon ganinsa yana yau茩i ne ya sanya tai saurin kai yatsar bakinta, wani 蓷aci taji ya game bakinta da sauri ta Mi茩e tsaye tana fa蓷in “Garin meriz??? Innalillahi wa’inna ilaihir Arjun gubar 茩une jini”
Rugar Mahinjo
A hankali yake bu蓷e idanunsa wanda sukai masa nauyi, bakinsa 蓷auke da addu’a,
A hankali kuma ya yun茩ura tare da tashi zaune,
Hakan nan yay yake jinsa wani iri jikinsa yayi masa nauyi yana bu茩atar motsa jiki sosai,
Idanunsa ya 蓷aga ganin Ar蓷o ya shigo ga kuma ki蓷a dake tashi a Rugar, tun kallon farko da yayiwa Ar蓷o bai sake kallonsa ba.
“Kamar dai julal ya bayyana, what the fork” ya fa蓷a yana jan numfashi duk abi an cika mutane da ihu, Kallonsa Ar蓷o yayi kafin yace.
“Wasan motsa jiki ne”
Da sauri ya bu蓷e idanunsa kamar bazai magana ba sai kuma yace.
“Uhm ball or what?”
Ya fa蓷a yana Mi茩ewa tsaye tare da yin waje domin jikinsa duk ciwo yake masa, yana fita kowa ya mutane da yawa sai ki蓷e-ki蓷e ake.
Bayansa Ar蓷o ya biyo yace “ko kana so ne?”
Lumshe idanunsa yay tare da bu蓷ewa Ar蓷o yace.
“To muje na gabatar dakai”
Gently yabi Ar蓷o jiki babu 茩wari, Barkido ne da Labbo a tsakiyar filin kowa jikinsa da guro jikinsu sai rawa yake, ga wata zabgegiyyar bulala a hannun Barkido da alama shine zai fara dukan Labbo, kana ganin bulalar kasan tayi shekaru a ji茩e saboda yadda ta kumbura,
Ar蓷o ne yace.
“An samu 茩arin ma nemi, yanzu jaruman namu guda uku ne”
Jin haka yasa Labbo tsorata da kuma firgita, a hankali ya dinga janye jikinsa kafin kace me ya nausa cikin jeji domin tsira da ransa, domin labari yazo masa hadda kitsan kibari aka saka wa bulalar Barkido,
A hankali Abu Maleek ya dawo tsakiyar filin a ransa yace “bana fa蓷awa Oumuu na girma ba, bari naiwa wannan duka zan bata labari”
Ya fa蓷a yana cije baki, Barkido ne yace “kai baka san komai akan wannan abun ba, kada kayi a sarar ranka, ka janye ka bar min kamar yadda 蓷ayan ya gudu”
Abu Maleek damai san kan abun ba ya kalli Barkido yana mai 蓷an tsotsar la蓳蓳ansa kafin yace.
“Uhm ba’a sauya min ra’ayi, idan nace zan yi to zanyi kada ka cikani da ihu kayi abinda ya dace”
Ran Barkido ne ya 蓳aci a ransa yace “za kaci Ubanka yanzu mahaukacin banza kawai”
Ya 茩are maganar yana fincike rigar jikin Abu Maleek nan da nan surar jikinsa ta bayyana mai cike da haiba, ga zanan ya fito ra蓷au gwanin sha’awa, 茩uri Ar蓷o yayi masa da ido, a na haka aka bawa Barkido umarni,
Gyara tsaiwa yayi sosai tare ri茩e bulala hannunsa da kyau, babu zato babu tsammani Abu Maleek yaji an zabga masa bulalar a tsakiyar bayansa, runtse idanunsa yayi saboda tsananin azaba da kuma ra蓷a蓷in daya shige sa a lokacin guda,
Kafin ya dawo daga gigin dukan Barkido ya 茩ara shimfi蓷a masa wata bulala a tsakiyar bayansa zuwa tsakiyar kansa, dun茩ule hannu Abu Maleek yayi tare da langwa蓳ar da kansa gefe guda cikin a zababban zafin daya ratsa masa jijiyar kansa ya bu蓷e bakinsa yace.
“O’ohhhh”