ABU MALEEK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABU MALEEK COMPLETE

ABU MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya 茩are maganar yana sakin dariya, domin yayi hakan ne domin ya tun zura Abu Maleek, babu shakka kowa ha茩茩arsa ta cimma ruwa,
Abu Maleek daya ke jin maganar Ar蓷o kamar Almara, shi za’a ma ihu? “Uhm” kawai yace yana yin gaba domin zuwa cikin inda ake jiransa, tuni kuma jikinsa ya fara rawa.

Yana shiga ya gyara tsaiwarsa, tare da lumshe idanunsa,
Barkido dake tsaye ya 茩ara gyara tsaiwarsa yana mimmi茩a hannunsa, alamar dai shima a shirye yake da kar蓳ar dukan na Abu Maleek,
Kallon gefe Abu Maleek yayiwa Barkido yana fa蓷in
“zakaci gidanku, fuska kamar Salad”
Lami蓷o ne ya mi茩a wa Abu Maleek wata zabgegiyyar bulala sai 茩yalli take,
Hannun damansa yasa ya amsa a cikin ransa yake fa蓷in
“Bisimillah Rahmanir Rahim”
Ya fa蓷a yana gyara zaman bulalar a hannunsa, kallon Bulalar yayi sosai, kafin ya 蓷aga kansa ya kalli Barkido, nan take kuma yaji wani haushi da ba茩in cikin dukan da Barkidon yayi masa,
Hakan ya sanya ya 茩ara ri茩e bulalar sosai, a hankali kuma ya ware bakinsa cikin sarrafa harshe yace.
“Ya Rahmanu ya Rahim!”
Ya fa蓷a yana mai shafe bulalar da tafin hannunsa, a hankali kuma ya 蓷aga bulalar kafin cikin wani zafin nama ya saukewa Barkido bulalar a tsakiyar bayansa.

A gigice Barkido ya ware mitsi mitsi idanunsa tare da kame jikinsa waje guda, domin tashin farko Barkido idanunsa ya raina fata,
Bai dawo hayyacinsa ba yaci Abu Maleek ya sake sakar masa wata Bulalar, wacce ya sanya ya furta “Auchhhiii!”
Da 蓷an 茩arfi saboda tsananin zafin shigar bulalar da yaji ya ratsa masa dukkan wata ga蓳a ta jikinsa,
Abinka da cikakken namiji, kuma 茩a茩茩arfa, wanda ya saba motsa jikinsa ta hanyar yin gym kala-kala, Uwa uba kuma FOOTBALLER, shiya sanya ya zage dukkan 茩arfinsa yana laftar Barkido da dukkan 茩arfinsa, a ransa yana ambaton sunan Allah,
Barkido tuni idanunsa ya fara kawo ruwa, zufa ta wanke masa jikinsa sai tsuma yake,
Idanun Abu Maleek ne ya sauka akan wata bulala dake hannun Lami蓷o da sauri yasa hannu ya amsa, ya ha蓷a hannu da dama, ya shiga Laftar Barkido wanda tuni ya fara kurma Ihu yana yin baya,
Sosai Abu Maleek ya gigita sa, ya ru蓷a masa jiki da duka ganin babu sarki sai Allah yasa Barkido fa蓷in.

“Wallahi na bar baka ita, na yafe bana sonta ka rabu dani haka”
Ina sam A.m baya gane karatun bare yayi masa hadda, duk inda Barkido yayi sai ya bisa ya daka, ganin idan bai yi da gaske ba, sai iya rasa ransa ya sanya ya 蓷aga 茩afafuwansa, tare da arta ana 茩are ya nausa cikin jeji kamar yadda Labbo yayi.

苼oyayyiyar ajjiyar zuciya A.m ya sauke yana jin zuciyarsa wasai, bashi da wata damuwa wacce ta shafi wannan dukan domin sai da yayiwa Barkido duka wajan hamsin,
Fesar da numfashi yay yana 蓷an cusa hannunsa tare da hargitsa gashin kansa wanda ya kejin yayi masa nauyi sosai, saboda rashin saloon da bai ba.

Mutane da yawa sai da suka yi mamakin yadda Abu Maleek ya iya dukan Barkido, Ar蓷o wani lafiyayyan murmushi ya sauke kafin a hankali yace.
“Lami蓷o kirawo min Jon wuro, domin ya zama wakilin Wannan ba茩on, kai kuma ka zama wakilin Julde”
Jinjina kai Lami蓷o yayi kafin ya mi茩e ya nufi bukkar Jon wuro,
Babu jimawa suka dawo a tare fuskar Jon wuro ta fa蓷a蓷a da Murmushi.

Jalaluldeen can ya nema 茩asan wata bishiyoyi wacce 茩asanta yake 蓷auke da yashi mai sanyi ga ruwa na 蓷an tsastsafo wa ta 茩asan wajan,
Yana zama Sweet tazu ya shige jikinsa, kwa蓳e fuska yay yana 蓷ura ha蓳arsa a jikin sweet,
Kafin cikin 茩asa da murya yace.
“I’m tried sweet, ina son gida, i need to hug my Grandma, Oumuu, And my world my everything Dadyna, nayi kewar su sweet”
Ya 茩are maganar yana shafa gashin sweet 蓷in wanda ya 蓷an hargitse, saboda yawon da suka sha.

Gyara zama Jon wuro yayi tare da kallon Ar蓷o yace.
“A matsayi na, na Uba a wajan Wannan ba茩o, ina nemawa 蓷ana Auran 拼ar ka Hawwa’u (Julde), ina fatan zaku bani wannan aure cikin girma da mutun ci ha蓷i da karramawa?”

Jinjina kai Ar蓷o yayi yana mai sakin murmushi yace.
“Ni kuma a matsayi na, na uba a wajan Hawwa’u, ina mai farin ciki sanar dakai cewa na bawa 蓷an ka auranta halak kuma malak”

“Allahamdulillah”
Lami蓷o ya fara kafin Jon wuro ya 蓷auki ku蓷i ya bawa Ar蓷o yasa hannu ya amsa, nan suka shaida auran Hawwa’u Julde, da kuma Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal, akan shaidu wajan mutum goma.

Tsakanin Julde da Abu Maleek babu wanda ya san abinda yake faruwa, sai da su Ar蓷o suka gama komai, sannan Ar蓷o da Jon wuro suka nufi inda Abu Maleek yake zaune shida sweet yana mata surutu ita kuma sai jela take 蓷agawa.

Suna zuwa suka nemi waje suka zauna, Jon wuro da yafi shekaru akan Ar蓷o ya fuskanci Abu Maleek sosai, tare da fa蓷in.
“Yaro na, Allahamdulillah! Kayi na sara akan abokin adawarka, ka shiga neman aure ba tare daka san komai ba, amma cikin ikon Allah gashi ka samu damar samun Yarinyar da ka shiga Sha蓷i a kanta”
With much surprise Abu Maleek yake binsu da kallo, Sha蓷i? Yaushe ya shiga sha蓷i? Wacce yarinyar suke magana? Wannan sune tarin tambayoyi da suke dan茩are a cikin zuciyarsa,
Jon wuro ne ya 茩are zama sosai ya fuskanci Abu Maleek cikin nutsuwa da kuma halin daddako yace.

“Tabbas wasan da Ar蓷o ya fa蓷a maka ba wasa bane haka kawai, sha蓷i ne wanda ake yinsa yayin neman aure, Barkido da Labbo sune suka shiga shiga cikin sha蓷in, kafin kai kuma ka shiga daga baya, shigarka kuma ya sanya Labbo fita, gashi kuma kayi nasara duk da cewa baka san, dalilin yin hakan ba, to Allahamdulillah a yanzu haka Hawwa’u ta zama matarka bisa jagoranci mu gaba 蓷aya, na zama wakilinka wanda na amsar maka auran a wajan Ar蓷o na bada Sadaki kuma da hannu na, Julde ta zama Matarka halak malak, kuma a yanzu zaka tafi da ita zuwa 茩asar ku”

Wata zabura Abu Maleek yayi, jikinsa na rawa ya shiga nuna Jon wuro da hannu cikin tsantsar 蓳acin rai da kuma tarin talaucin abinda sukai masa yace.

“What? Aure? Haaaa! Dawa 蓷in ni dai? Goodness saboda kun rasa yadda za kuyi da 茩aramar yarinyar ku shine zaku li茩a min ita? Uhm wallahi za kuyi dana sani bana sonta ko 蓷aya kamar yadda kuka li茩a min ita haka Nima zan mayar da ita baiwa, daman ai ba 茩aunar ta kuke ba, Wheel Nima haka kunga anyi 50% kenan”

Ya fa蓷a yana sakin wani zazzafan huci daga cikin bakinsa idanunsa ya ka蓷a yayi jaa, kana kallonsa zaka fahimci how sad he is,
Gaba 蓷aya ya birkice gargasa jikinsa duk ta mimmi茩e, Jon wuro kallonsa yayi domin yasan za’a rina,
Kuma tun yanzu ya fara tausaya Rayuwar Julde zata shiga hannun wanda baya sonta, amma zamanta a wajan zaifi da蓷i fiye da zamanta a wannan rugar,
Ar蓷o kam ko a jikinsa domin shi ko Abu Maleek zai tafi da ita ya yankata ya zubar da gawarta ko a jikinsa,
“Zuwa yanzu da Julde amana take a wajan ka, kasan duk wanda yaci amana Shida Ubangijinsa, bazan maka dole ka sota ba saboda so halitta ne, amma ina fatan wata rana ka zame mata garkuwa, bangon da zata jingina taji da蓷i, duk abinda ya samu da rayuwarta a yanzu kuma KAI NE SANADI, kayi ha茩uri ka zame mata Tubalin da zai gida rayuwarta, ko ba zaka so ta ba, ka kula da rayuwarta”

Yakai 茩arshen maganar cikin sigar rarrashi da kuma ban baki,
Abu Maleek huci kawai yake saukewa jikinsa duk rawa yake.
Da kallo kawai suke binsa ganin yadda naman jikinsa yake rawa, ga yadda jijiyar kansa ta fito sosai, hannunsa ya sanya ya 蓷auki Sweet tare da kallonsu yace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button