
*AUTHOR'S NOTE*
BANA SAURI CIKIN WANNAN LITTAFIN, BA KUMA GUDU NAKE BA, YADDA KO GANI KO KARANTA SHI A HAKA, DOMIN INA DA TABBACIN ZA’A KAWO GA苼AR DA A YINI GUDA BAZA KUJERE BA IDAN MACE MAKU BABU POSTING, LITTAFIN ACE BOOK 1 2 3 NE, HAKAN KAWAI ZAI TABBATAR MANA TAFIYA CE MAI 茒AN NISA, AMMA GARE NI IDAN INA TYPING SAM BABU NISANTA, A HAR KULLUM KUNA KARANTA LITTAFI NA DA SIGA BIYU, ILIMIN CIKINSA, DA KUMA FA茒AKARWAR CIKIN SA, I’M NOT PERFECT AMMA DOLE ZAN CE MAKU AKWAI HIKIMA CIKIN WANNAN LITTAFIN NA ABU_MALEEK KADA KO KARANTA DOMIN JIN DA茒IN KU, DOMIN AKWAI SANDA ZAKU NEMI DA茒IN KO KARASA SAI ZALLAR 茦UNAR ZUCIYA DA KUMA TASHIN HANKALI, ME ZAI FARU? MENE A LABARIN? NO ONE’S KNOW DOLE SAI NI.
DAN HAKA NAKE CEWA KO GYARA ZAMA KANA KO KAKKA苼E ZANI.
SHARE PLEASE AS SO MUCH AS YOU CAN HABIBATIES, KUYI SHARE FISABILILLAHI SABIDA ALLAH馃槏馃槏馃憦馃徎
1/1/22, 18:59 – Aisha Adam: 馃寛馃寛馃寛馃寛
ABU_MALEEK
馃寛馃寛馃寛馃寛
NA
NA’IMA SULAIMAN SARAUTA
Nimcyluv
BOOK 1
PAGE 3-4
“Jikin King Tunde Muhammad Jalal ya tsananta, babban tashin hankalin yadda yake ta kiran sunan Queen Roomana”
Dam dam dammm zuciyar Mai Babban 蓷aki ta bada sauti,
Cikin tashin hankali da kuma tsoro ha蓷i da zullumin daya gama ratsa zuciyar mai Babban 蓷aki,
Ta sanya tafin hannunta tare da dafe gishintuta shiga sharfe zufar da yake karyo mata,
Baya tayi ka蓷an tare da fesar da numfashi ha蓷i da kallon,
Hadima Zubaida cikin jarumta tace.
“Kije ki kira Oumuu-Ayman ta sameni a tirakar King Tunde,
Sannan ki kiramin OTUN (Galadima), shima ya sameni a tirakar King Tunde”
Cikin ladami da girmamawa Hadima Zubaida ta sunkuya har 茩asa tace.
“Fa蓷e taki cikawa tawa,Mai Babban 蓷aki”
Kai kawai Mai Babban 蓷aki ta jinjina,
Shekarunta sun ja, amma komai na rashin tsoran Allah da kuma son zuciya 茩ara bayyana yake,
A cikin Alaafin (Masarauta).
Hadima Zubaida na shirin fita Mai Babban 蓷aki tai saurin fa蓷in.
“A tsananta tsaro a shashin, ki tabbatar babu wanda ya san da maganar ciwon na King Tunde,
Hatta matarsa kada ki fa蓷a mata, sannan ko sirikan gidan nan kada suji wannan labarin mai tarwatsa zuciya,
Ki sani fitar wannan al’amarin yana nufin rushewar Wannan Masarauta wacce ta kafu shekara da shekaru,
Ki kiyaye da wannan Hadima Zubaida, duk abinda yaje ya dawo kiyi kuka da kanki”
茦ara sunkuyar da kai Hadima Zubaida tayi cikin son bawa Mai Babban 蓷aki girmanta na mahaifiyar King Tunde tace.
“Ubangijin Al’arshi yana kallon komai,
Kuma yana ji yana gani, idan har maganar ta fita dukkan hukunci daya dace aimin ni Hadima Zubaida na aminci”
Tana fa蓷in hakan ya juya da sauri domin zuwa sashin Oumuu-Ayman.
Ajjiyar zuciya a karo na barkatai Mai Babban 蓷aki ta 茩ara saukewa,
Zuwa yanzu abubuwa sun fara mata yawa,
Tana son samun mataimaki Tabbas,
Amma yaushe? Ta ina? Wace zata zama hasken da zai yaye duhun dake cikin Alaafin?
Shine abinda har yanzu bata sani ba,
Yadda shekarunta suka ja hakama Oumuu-Ayman ba komai zata iya ba,
Jigon gidan biyu ne, gashi an wayi gari babu Queen Roomana,
茒aya 蓳angaren wanda ya kasance haske da kuma tauraron gida 茩addarar sa ka蓷ai da ishesa,
茦addarar kuma da ita ce sanadiyyar faruwar dukkan wani mugun tuggu dake cikin Alaafin,
Mi茩ewa tsaye tayi tana runtse 茩afarta wacce take mata,
Tsananin zafi da kuma zugi domin kwana biyu,
Ciwon 茩afar ya dawo mata sabo fill har bata iya taka 茩afafuwan ta,
Tana dogara sandar zallar azurfa ta mai she茩i ta nufi Parlo idan Kuyanginta suke jiranta.
A can tirakar King Tunde kowa Oumuu-Ayman ce zaune a gefe guda, sai Otun da kuma Hadima Zubaida.
Gaba 蓷aya Babban shashin wanda ya kasance shine sashin Oba watu sarki ya cika da masu tsaro ko alamun fara’a babu a fuskarsu bare ka tabbatar cewa idan kazo zasu barka ka shiga,
Mai Babban 蓷aki ce ta 茩arasa shiga ciki yayinda kuma,
Kuyangunta suka tsaya can nesa da Babbar 茩ofar shiga tirakar ta King Tunde,
Tana shiga Oumuu-Ayman ta Mi茩e tsaye sabida nuna girmamawa,
Cikin sabon tashin Hankalin daya samesu bayan wanda suke ciki,
Mai Babban 蓷aki taja Jikinta can gefe kusa da King Tunde tana fa蓷in.
“Kilosh猫le?” (Meke faruwa)
Cikin jan wahala da kuma tsananin a zabar da King ya keji a cikin zuciyarsa ya sanya tafin hannunsa,
Dake 蓷igar da gumi yace.
“A nemu Queen Roomana duk inda take,
Kada a bari a rasata, Tabbas jikina yana bani akwai wani abu,
Ban san mene shi ba, ban kuma san yaushe ya faru ba,
Amma Queen Roomana itace hasken Alaafin”
茒auke kai Oumuu-Ayman tayi sabida hawayen daya sakko daga cikin idanunta,
Babu abinda yake tayar mata da hankali irin rashin Queen Roomana,
Babban abin fargabar har kawo yazo babu wanda ya fa蓷awa,
Jalaluldeen sabida tsoran abinda zai yi,
Tana tsananin son Jalaluldeen so mai yawa musamman idan ta duban mummunar 茩addarar data hau kansa,
Gyara zama Mai Babban 蓷aki tayi tace.
“Babu abinda zai faru da Queen Roomana, ka kwantar da hankalinka, na tabbatar ko babu Queen Roomana akwai hasken da zai zo cikin Alaafin yay fatali da duhun da yake cikinta,
Tabbas nayi imani da hakan lokaci kawai muke jira”
Ta 茩are maganar tana tasbihi a ranta,
King Tunde kallon mahaifiyar tasa yay yace.
“Wanne haske ne wannan wanda ya wuce na Queen Roomana?,
Bana jin akwai wani haske da zai yi iya yaye wannan duhun dake cikin Alaafin”
Murmushi Mai Babban 蓷aki tayi tace.
“Da kasan zaka samu Queen Roomana? Ko kuma kasan zaka samu MALEEK yaro mai fikira da hikimar gaske, to mafarki na bazai ta蓳a gayan 茩arya ba,
Sai dai bansan lokacin da mafarkin zai zama gaskiya ba”
A can waje kam wata mai matukar kama da Hadima Zubaida ce ta nufi cikin sashin Kinga Tunde,
Yayinda gaba 蓷aya kayan jikinta irin na Hadima Zubaida ne babu wani bambanci,
Hannunta 蓷auke da 茩wayar zumar da aka ha蓷awa King Tunde ta nufi wajan,
Sanin cewa kowa yasan ita 蓷in itace Babbar Hadima kuma Amintacciyar King Tunde yasa babu wani shamaki aka bu蓷e mata tafkekiyar Kofar glass 蓷in ta shiga ciki tana mai sakin tattausan murmushi.
Tana shiga ta samu ta silale ta shige cikin wata 茩atuwar akwati wacce duk yadda kakai da fahimta baza ka ta蓳a fahimtar abinda yake faruwa ba,
茦ara 茩asa kunne tayi sabida jin Oumuu-Ayman tana fa蓷in.
“Maleek yana raye, sam bai mutu ba, kawai rayuwarsa tana cikin hatsari,
Kuma shine ka蓷ai 茩arfin guiwar mu, shine last hope 蓷in mu,
Shine zai sanya mu tuni 茩aryar da take 蓳oye shekara da shekaru”
Oumuu-Ayman ta 茩are maganar tana sakin tattausan murmushi domin ita ka蓷ai tasan abinda yake zuciyarta,
King Tunde ya ja numfashi yana 茩ara kallon Oumuu-Ayman da kuma Hadima Zubaida wacce take tsaye gefe guda yace.
“Bikin (ODUN EGUN) saura sati biyu,
Bana jin cewa zakai wannan lokacin ina raye,
Amma a tabbatar cewa ko na mutu sai a gudanar da wannan bikin, domin shine zai tabbatar wa da al’ummar Kanzaf Alaafin tana cikin 茩oshin lafiya,
Ban yarda a binne gawata ba har sai an gabatar da wannan bikin al’adar”
Cikin sabon tashin hankali Oumuu-Ayman tace.
“Meke faruwa dakai ne King Tunde? Ka sanya zuciyoyinmu cikin zullumi, ka sanya zu茩atan mu cikin juyayi”
Murmushin ba茩in ciki king Tunde yay kafin yace.
“An samin goba cikin abincin sha na, ina jin zafi da ra蓷a蓷in ta, jikina kamar ana hura min wuta haka na keji, babu mai magance min wannan cikin sai Aremo JALALULDEEN TUNDE MUHAMMAD JALAL”
Shiru sukai sabida tashin hankali gaba 蓷ayansu zufa ke karyo masu,
Fake Hadima Zubaida dake cikin akwati wacce tai pretending kamar itace Hadima Zubaida ta gaskiya,
Tai saurin fitowa tana rufe bakinta domin,
Dukkan abinda ya dace ta samu labari akai yanzu taji komai,
Da sauri ta juya ta fita fuskarta cike da farin ciki da kuma da蓷in samun nasarar da tayi.



