ABU MALEEK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABU MALEEK COMPLETE

ABU MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

“Uhm! Iskanci ko ina ba dole mutum ya lalace ba idan yana kallon wannan shirman”
Ya fa蓷a yana saurin sauya channel daga telemondo zuwa zee world, lumshe idanunsa yayi a hankali kana ya shiga sauke ajjiyar zuciya, kafin a hankali ya bu蓷e idanunsa tare da sauke ganinsa akan wani mutum dake fuskar t.v,
Yanayin shigarsa mutumin ya tabbatar da cewa sarki ne, 茩ara ware idanunsa yayi sosai, ganin yadda yake zazzaga mazifa, yayinda matansa suke gefe da alama kuma shine da gaskiya.

Idanunsa ya mayar 茩asan t.v haka nan ya samu kansa da duba sunan film 蓷in ganin an sanya Johda and akbar yasa ya tabbatar da cewa mijin shine Akbar matar kuma Johda amma sauran matan fa?? Jalaluldeen Muhammad Akbar ne ya zare ta kobin hannunsa lokacin daya samu labarin 蓷an gidan Mahmanga wacce ya kewa kallon uwa ya shigo palace 蓷in ya kashe masa babban amininsa kuma 蓷an uwansa..

Haka Abu Maleek ya wanzu a parlon yana kallon Film 蓷in Johda and akbar yana nan zaune har aka gama episode 蓷in ranar aka tsaya a wajan da Akbar yake 茩ona kujerar Sarauta saboda ba茩in ciki da kuma tashin hankali, yace kujerar bata haifar masa da komai ba sai damuwa, ko burinsa yaga ya mallaki kujerar dan haka bata da wani Amfani shine ya sanya ya cilla mata huta.

Sauya channel yayi zuwa International channel wato (Aljazeera) Ajjiyar zuciya ya sauke tare dayin baya ya lafe saman kujerar tare da lumshe idanunsa,
Tunani ne fal ransa, haka nan kuma tunaninsa ya 茩ara ta’azzara tunda ya kalli Johda and akbar, wato sarauta banzar abace, musamman yadda yaga palace 蓷in su Akbar take, Masarauta iya Masarauta, amma kowa son zuciyarsa yake bi, mutane ka蓷an ne masu tsoran Allah,
茦ara fesar da iska yayi daga cikin bakinsa, wato zafin mulki sai ya sanya ka kashe 蓷an uwanka?? wannan tunanin Shine a ransa kafin ya ja table ya 蓷ura fararan 茩afafuwansa yana jan tsaki a cikin ransa yace.

“Shima Akbar yayi ha蓷a ma, mata uku kamar wani maye, Queen Johda, Queen Rukayyah, Queen Salima”
Ya fa蓷a yana sanya hannunsa tare da shafa sajan fuskarsa yana 蓷an fidda numfashi ka蓷an.

Oumuu-Ayman ce ta shigo cikin Babban Parlon hannunta ri茩e da wata 茩warya mai kyau anyi mata zanan tambarin sarautar, tunda ta shigo idanunta ya sauka a kansa yana zaune ya lumshe idanunsa tare mi茩ar da 茩afafuwansa a saman table,
Wajansa ta nufa tana sakin Murmushi tana zuwa ta ajjiye 茩waryar hannun nata a saman wani table 蓷in daban, kafin ta juya ta nufi cikin wani wanda da alama kitchen ne, plate ta 蓷auka ta zuba masa alkali da bakilawa, sai kuma wani da zuba masa tarkacan fruits domin yau abincin Masarauta take son yaci.

Bayan ta gama jera masa komai a table 蓷in ne ta nemi waje kusa dashi ta zauna tare da fa蓷in.
“Zaki your breakfast is ready”
Idanunsa ya bu蓷e a hankali ya kalleta sai kuma ya 蓷auke idanunsa tare da kawar da abinda yake ransa, table 蓷in ya tsorawa idanu kafin da sauri ya kalli Oumuu-Ayman tare da fa蓷in.

“Oumuu what is this??? Nifa ba wannan ba”
Ya fa蓷a yana marai-raice fuska tare da langwa蓳ar da kansa gefe guda alamar shi ba’ai masa dai-dai ba,
Idanunta ta 蓷auke daga garesa bayan tayi masa wani irin kallo sai kuma tace.
“Abinda za kaci yau kenan, na tsara maka time table na duk abincin daza kaci, Breakfast, lunch, dinner, bayansu duk abinda aka baka ban yarda kaci ba”
Ware idanunsa yayi sosai kamar bazai magana ba sai kuma yayi baya yana fa蓷in..

“Gaskiya Ni bazan iya cin wannan abun ba, mene wannan abun a du茩un茩une kuma??”
Sosai abin ba 茩aramin mmki ya bata ba, musamman yadda taga yana narke fuska hakan ya tabbatar mata da gaskiyar abinda zuciyarsa yake fa蓷a,
Tana jin yadda yake mita tai masa banza haka ta bashi Alkalin tauna 蓷aya yayi yace shifa sam bazai ci ba,
Sai ma ya motsa fuska yayi tare da Mi茩ewa tsaye yana fa蓷in.

“Oumuu wannan ai a ciki zai tsaya kawai aiyi wani kamar maciji, uhm”
Ya fa蓷a yana shigewa cikin part 蓷insa kai tsaye kuma bathroom ya huce ya 蓷aura alwala jin ana kiran sallar zhur, bayan ya fito ne ya samu Oumuu zaune da Julde tana bata Abinci,
daga kallo 蓷aya da yayi musu bai sake ba ya nufi 茩ofar baya kai tsaye ya shige masjid.

Julde ta 蓷an kwa蓳e fuska tare da fa蓷in
“Oumuu to baya magana ne wai shi??”

Ta fa蓷a tana shagwa蓳e wa, kamar zatai kuka.
Murmushin kawai Oumuu tayi domin ta da蓷e da fahimtar Julde matan nan masu surutu, gashi kuma Ubangiji na neman ha蓷ata da miskilanci miji wanda gane masa sai addu’a.
Fresh milk ta bata tana fa蓷in.
“Yana magana mana,ba kiji muna hira dashi ba”
Rau rau haka idanunta suka kawi ruwa kafin ta tura baki gaba tace.

“Oumuu to ni mene yasa ba yayi min? Ko dan yaga bana gani ne, Allah Oumuu yanzu ji nake dama iduna zai bu蓷e naga Ballowo nasan ba wani kyau ne dashi ba”
Wani irin Murmushi Oumuu-Ayman tayi kafin ta 蓷aga Idanunta a sanyaye ta kalli bakin 茩ofa,
ha蓷a ido sukai da Abu Maleek wanda yake tsaye jinjine da 茩ofa ya a har蓷e hannayensa waje guda,
Kallon yadda ya ha蓷e fuska tayi waje guda kafin ta 蓷auke idanunta tana danne dariyar dake shirin kwace mata tace.

“Eh gaskiya bai cika wani kyau ba, gashi nan da manyan idanu,
da gashi har wuya kamar wani buzu,
sai tsayi da fa蓷i kamar basamude,
kai abinda zai wanda ya gani”
Oumuu-Ayman ta fa蓷a tana sakin wata lafiyayyiyar dariya mai ban sha’awa,
Abu Maleek kam cika yayi fam sai bakin yarinyar daya tsorawa idanu ko yawo bata ha蓷iya sai 蓷an ban zan surutu kamar ako.

Julde dake sauraran abinda Oumuu-Ayman take fa蓷a ne yasa ta karyar da wuya tace.
“Ayyah, kenan shi yasa baya magana? Oumuu Kice yana kulani mana”
Ta fa蓷a kamar zatai kuka,
Daga bayansu sukaji ance.
“Ni zan kulaki idan shi ya茩i, har labarai zanna baki ai”
Washe baki tayi fararan ha茩uranta suka bayyana har wani haske suke fiddawa kafin tace.
“La!! Yayan Ranar ko Oumuu, shi kam yana da kirki”
Da mamaki Oumuu-Ayman ta juya tana kallon Adams mene ya sanya masu tsaron flat 蓷in Abu Maleek suka basshi ya shigo? Idanunta ta 蓷auke daga kallon Adams kana ta mi茩e tsaye tare da shigewa bedroom 蓷in da Julde take kwana,
Tayi hakan ne kuma domin ta ha蓷awa Julde ruwan haka, dalilin kuma hakan zai sanya ta janyeta daga wajan Adams.

Da idanu kawai Abu Maleek yake kallon 蓷an uwansa Adams da ita kanta Julde mamaki ya kamasa, ganin yadda Adams 蓷in yake ta jan Julde ta surutu,
Hakan nan yaji zuciyarsa babu da蓷i ransa ya 蓳aci ga wani mugun haushin yarinyar daya cika masa zuciya,
Mai makon ya shigo sai kawai ya fice tare da nufar Lambu.

Adams kam duk abinda Abu Maleek yana sane dashi, yana son ya Fahimci mene hala茩arsa da Yarinyar amma ya kasa fahimtar hakan, saboda yadda fuskar Abu Maleek take a 蓷aure hakan yasa bai fahimci komai ba.

Gyara zama yayi idanunsa akan Julde yace.
“Uhm what’s your name? I mean menene sunanki beauty?”
Shiru tayi sai kuma tace “Naji 茩amshin turaren Ballowo shi ne ya shigo?”
Ta fa蓷a tana narkar da fuska, da rashin fahimta yace.
“Ballowo?? Waye haka kuma?”
Cikin siririyar muryarta tace “Oumuu tace sunansa Jalaluldeen amma ana ce masa Abu Maleek to Shine Ballowo ai”
Shiru yayi yana nazari kafin ya 蓷an cije baki yace.
“Nagane, ba shi bane 茩amshin turarena kikaji”
Girgiza kai tayi Idanunta na kawo ruwa tace.
“Allah shi ne gashi nan naji zuciyata yana harbawa, kuma sai yazo waje kawai na kejin hakan”
Ta fa蓷a Idanunta cike da hawaye, wani abu mai 蓷aci Adams ya ha蓷iye domin jiya kawai da yaga yarinyar tayiwa zuciyarsa mugun kamo, da 茩yar ya iya bacci daya rufe idanunsa ita yake kallo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button