ABU MALEEK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABU MALEEK COMPLETE

ABU MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

Washe gari
Tsaron cikin Alaafin ya tsananta matu茩a, haka kawo lokacin babu wanda yake da labarin abinda yake faruwa,
Kowa ya tambaya Meke faruwa ana bashi bayanin cewa sabida bikin ODUN EGUN da Za’ai shiyasa aka fara shiri tun yanzu!
Sabida bikine da ake yinsa duk shekara wanda ake gayyatar,
Manyan sarakuna da kuma manyan mutane,
Biki ne dake nuna wa jama’ar Kanzaf cewa 茩warai da gaske Oba (sarki) da jama’ar cikin Alaafin suna lafiya,
Rashin yin bikin kuma yana nuni da cewa akwai wani,
Gagarumin abu dake faruwa a cikin Alaafin wanda hakan zai iya tada hankalin jama’ar Kanzaf.
Wannan dalili yasa gaba 蓷aya Hankalin Mai Babban 蓷aki da kuma Otun da Oumuu-Ayman ya tashi matu茩a,
Domin sunyi imani cewa mutum 蓷aya ne zai iya zama ya gudanar da wannan bikin al’adar ba tare da an samu wata matsala ba,
Amma su gansu basu da tabbacin cewa zai amsa kiran king Tunde 蓷in ko kowa?
Rabonsa da cikin Alaafin (Masarauta) yanzu kimanin shekaru wajan 20 kenan,
Yaya ya koma? Ya yake yanzu no one’s know!
Gaba 蓷aya suna zaune a saman babban danning table wanda a 茩alla yake da kujeru wajan 20 ciff, wanda sukaiwa table 蓷in 茩awanya,
Bisa al’adar mutanan cikin gidan ne duk ranar juma’a tare suke zama yin breakfast, lunch, and dinner!
Yanzu ma suna zaune Mai Babban 蓷aki ce a babban kujera, gefenta kuma Queen Ayoola ce, daga 蓷aya gefen kuma Oumuu-Ayman ce.
Sai kuma sirikan gidan wanda suke cikin ka蓷ai ci da kuma kewar mijinsu,
BOLA, sai kuma KUBRAAH, sai kuma Aremos (prince’s) Adams, Shakiru, Sharefddeen, Femi, kana Salimerh.
A hankali kowa keyin breakfast 蓷insa baka jin 茩arar komai saita Spoons knives and forks!
Boola ta 蓷an ja Ajjiyar zuciya tana ta juya Arish 蓷in dake plate 蓷inta ta gagara cin komai,
A tsanake Mai Babban 蓷aki tace.
“Kilosh猫le Boola?”
Marai-raice fuska tayi a hankali kuma hawaye ya sakko daga cikin idaniyyarta zuwa kan farar 茩yakkyawar fuskarta tace.
“Allah ya 茩ara maki lafiya da kuma yawan rai, abubuwa sun fara min yawa, babu miji babban tashin hankali yadda ake nemi Mami aka rasa!
Yanzu da wanne kalar baki za muyi wa Jalaluldeen bayani? Wanne hali Mami ke ciki tana ina ta mutu ko tana raye babu wanda ya sani”
Runtse idanunsa sosai Adams yay yana jin zcyarsa na tafasa ainun, wane zata rainawa hankali,
Bayan a jiya ya gama fahimtar komai cewa Jalaluldeen ya sanya aka sace Queen Roomana (Mami) sabida cimma bu茩atarsa,
A hankali jikinsa ya 蓷an shiga rawa kana a zafafe kuma ya hanka蓷e plate 蓷in gabansa yana mai jin yadda zuciyarsa ta cika da tsanar Jalaluldeen.
Mai Babban 蓷aki bayan Adams tabi da kallo tana mai son karantar yanayinsa amma ta kasa.
Cikin tarin mamaki na sauyin yanayin Adams da juya dubanta ga Boola tace.
“Kuyi addu’a, in sha Allah! Babu abinda zai faru da yardar Ubangiji tana cikin kariyar Allah, ita 蓷in haske ce koda an rasa ta Tabbas Ubangiji zai kawo mana madadinta wacce zata kula da komai na cikin Alaafin Tabbas”
A tare Queen Ayoola da Aremo Shakiru suka kalli Mai Babban 蓷aki cikin son kawar da abinda yake ransu a tare abin kamar ha蓷in baki suka furta.
“In sha Allah!”
Sharefddeen kam abincinsa kawai yake ci yana mai tunanin abubuwa da dama.
Rarraba idanu Kubraah ta fara kafin cikin nutsuwarta ha蓷i da kamewa tace.
“Ina Maleek ne?”
Dam zuciyoyinsu suka buga a tare musamman Oumuu-Ayman, wacce tuni zufa ya gama wanke ta kanta a 茩asa,
Hannunta mai 蓷auke da spoon ya shiga rawa sabida tsananin ta’ajjujin tambayar ta Kubraah domin sam ba tayi tunanin hakan ba a kuma dai-dai wannan lokacin..
Cikin rashin sanin amsar kuma daza su bawa Kubraah ne yasa a sukwane Oumuu-Ayman ta 蓷aga hannunta daga cikin plate 蓷in tare da mi茩ewa tsaye,
A hankali cikin nuna cewa tana da cikakken hankali da kuma tarin nutsuwa ta nufi shahinta,
Ganin haka yasa Mai Babban 蓷aki gyaran murya a hankali tace.
“Ki Sanarwa Hadima Zubaida cewa ina nemanta yanzu da gaggawa”
Mai Babban 蓷aki ta fa蓷a tana kallon hanyar da Oumuu-Ayman tabi.
Da “to” Oumuu-Ayman ta amsa tana mai yin gaba abinta,
Kubraah ganin babu wanda ya amsa ta yasa taja bakinta tai shiru,
Shakiru wani kasalallan Murmushi ya saki yana mai jan gemunsa da hannunta,
A ransa yake fa蓷in.
“A juri zuwa rafi da tulo..”

Wajan 11:30 Mai Babban 蓷aki na zaune saman ladduma idar da walaha 蓷inta kenan Hadima Zubaida tayi sallama bayan ta nemi isu wajan Hadimar Mai Babban 蓷aki wato Hadima Akin.
Zubewa tayi gaban Mai Babban 蓷aki tana mata kirari kamar yadda ta sama,
A taushashe cikin son 茩ara jan kunan Hadima Zubaida tace.
“Zubaida ina mai 茩ara jan kunanki game da wannan sabon al’amarin, mu hu蓷u muka san da wannan maganar, ni Oumuu-Ayman sai King Tunde da kuma Otun (Galadima),
Idan maganar rashin lafiyar king Tunde ta fita da kuma 蓷aya maganar wacce tafi komai muhimmanci a gare mu ta rashin mutuwar MALEEK ta fita, Tabbas kada kiyi tunanin zan goyi bayan ki,
Dukkan abinda ya faru ki kuka da kanki”
Cikin gamsuwa da maganar Mai Babban 蓷aki Hadima Zubaida ta jinjina kanta tace.
“Raina fansa ne ga Alaafin, dukkan abinda zai cutar da jama’ar cikinta kuma ina ya茩i dashi, na aminci da dukkan hukuncin da Za’ai min idan har wannan Maganar ta fita”
Murmushi jin dadi Mai Babban 蓷aki ta saki domin ta aminta da Hadima Zubaida sosai fiye da jikokinta.
“Ke nemu min Amintacciyar kuyangar Jalaluldeen yanzu”
Da makaki Hadima Zubaida tace.
“Ai Jalaluldeen bashi da wata Amintacciyar kuyanga, rabonsa da Nigeria yanzu kimanin shekaru ashirin kenan ciff”
Da sauri kuma Mai Babban 蓷aki tace.
“Ai haka ne, daman na kiraki domin naja kunanki ne”
Murmushi Hadima Zubaida tayi sabida rikitar tsufan Mai Babban 蓷aki, danma tana jajir cewa,
Cikin 茩asa da kai tace.
“Ai kin fa蓷an”
Kallonta tayi sai kuma tace.
“Au toh! Toh! Shikenan, kawo min zuba yanzu da madarar shanu mai zafi, ki ha蓷a da Algaragis”
Mi茩ewa Hadima Zubaida tayi ta nufi babban kitchen 蓷in Mai Babban 蓷aki ta a shirin shiga ciki Mai Babban 蓷aki tace.
“Ki ha蓷o min da Algaragis”
Hadima Zubaida tai Murmushi tace.
“Ai kin fa蓷a min”
Jinjina kai tayi tace.
“Toh! Toh! Shikenan”
Ha蓷o mata komai tayi kana ta kawo mata wajanta tare da Mi茩ewa tace.
“Na barki lafiya Mai Babban 蓷aki Allah ya 茩ara lafiya”
Jinjina kai kawai Mai Babban 蓷aki tayi ba tare da tace komai ba,
A hankali kuma ta sanya hannunta mai cikakkiyar lafiyar ta cire Inibi guda 蓷aya mai sanyin gaske tai Bisimillah tare da sanyawa a bakinta.
A can 茩ofar sashin Mai Babban 蓷aki kowa cikin nutsuwa Hadima Zubaida take tafiya harta isa sashinta domin hutawa,
Kai tsaye gaban babban mirror’n dake ma茩ale a jikin bangon parlon ta kalla.
A hankali kuma ta fara 蓳a蓳蓳aka dariya har haya茩i na fita daga cikin bakinta,
Tana gama dariyar ne kuma ta tsuke fuska tare da sanya hannunta ta cire fake fuskar data ma茩ala irin ta Hadima Zubaida,
Nan take fuskar…..

SHARE FISABILILLAHI DAN ALLAH
1/1/22, 18:59 – Aisha Adam: 馃寛馃寛馃寛馃寛
ABU_MALEEK
馃寛馃寛馃寛馃寛

     NIMCYLUV

BOOK 1
PAGE 7-8

Idanun Coach 蓷in ne suka fito waje sabida tsananin azaba ha蓷i da ficewar hayyaci,
Ba 茩aramin sha茩a Abu_maleek ya yi masa ba,
Sabida ko bu蓷e idanu ba ya iyawa, A.m kam cikin rashin sanin abinda yake aikatawa yay cilli da Coach 蓷in gefe guda,
Yana sakin numfashi tare da fesar da iska, gaba 蓷aya blue 蓷in 茩wayar idanunsa ta rine tai jajirrr tamkar gauta!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button