ABU MALEEK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABU MALEEK COMPLETE

ABU MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

馃槼akwai cakwakiya kenan ur opinions indeed
1/1/22, 19:00 – Aisha Adam: BOOK 3
59-60
Kafa蓷un ta, cikin sauri ya zame ta daga jikinsa, tare da mi茩ewa tsaye yana fesar da iska daga cikin bakinsa,
kafin a hankali ya Lumshe idanunsa, ko cake 蓷in da yazo 蓷auka bai 蓷auka ba ya nufi babban Parlo yana ha蓷a numafashi waje guda,
Yana fita Oumuu-Ayman na shigowa hannunta ri茩e da wata ba茩ar jaka mai kyau, kallonsa tayi taga ya kifa fuskarsa a jikin armchair 蓷in da yake zaune akai.
Ba tare da tace masa komai ba ta 蓷auke kanta ta nufi bedroom 蓷in daya fito,
Tana zuwa ta samu Julde zaune a saman carpet kusa da bed 蓷in Abu Maleek, idanunta da rayuwar hawaye sai ajjiyar zuciya take saukewa,
Cike da mamaki Oumuu-Ayman ta kalli Julde kafin ta 茩arasa gareta tace.
“Daughter kuka? Ke dawa kike kuka?”
Bu蓷e baki tayi da niyyar gaya mata cewa Ballowo 蓷inta ne ya yarda da ita, kuma ya cije ta sai kawai tai Shiru domin bata jin zata iya fa蓷awa Oumuu-Ayman hakan,
Hakan ta samu kanta da fa蓷in 茩arya abinda bata ta蓳a yi ba tace.
“Oumuu fa蓷uwa nai”
Cikin tausaya ha蓷i da so da kuma 茩auna Oumuu-Ayman tace.
“Ayyah! Da baki tashi ba ai, sorry sannu ko daughter?”
Jinjina kai kawai Julde tayi kafin Oumuu-Ayman ta mi茩ar da ita cikin rashin sakewa da kuma sabuwar kunyar Oumuu-Ayman daya kama Julde ta runtse idanunta tare da ha蓷e Jikinta waje guda,
a haka Oumuu-Ayman ta taimaka mata ta shirya cikin wata ha蓷a蓷蓷iyar black 蓷in body short wacce ta tsaya iya kar laps 蓷inta, fararan cinyoyinta duk a waje,
ba 茩aramin kyau tai ba,
Musamman jikin rigar daya kasance da red 蓷in Stones masu she茩i,
Sai wani red 蓷in band da aka ha蓷e mata gashi dashi,
hannunta Oumuu-Ayman ta kama zuwa Parlo,
Da sauri ta saki wata wahalalliyar ajjiyar zuciya wacce har sai da Oumuu-Ayman ta juya ta kalleta,
sosai taga 茩irjinta na mugun 蓷agawa,
Julde kama wata harbawa Zuciyarta tayi wacce bata ta蓳a jin irinta ba,
ga wani sanyi da jikinta yay a haka Oumuu-Ayman ta zaunar da ita a kusa da inda Abu Maleek zaune har yanzu kuma kansa a kife yake.

Abu Maleek kam tunaninsa ne ya tsaya cak, yayinda gaba 蓷aya 茩wa茩walwarsa ta toshe baya iya gane
Ta茩a mai mai abinda yake wanzuwa a cikin zuciyar tashi,
Yana jin wani sabon yanayi mai kama da sabo da kuma kasantuwa na kawowa kwanyar kansa ziyara,
Gaba 蓷aya memory kansa ya kasa tantance masa irin abinda ya keji.

Ajjiyar zuciya ya sauke a hankali kuma cikin damuwa ya 蓷an kwa蓳e fuskarsa cikin yanayin na rashin sanin makama
Da kuma abinyi ya manna tafin hannunsa a saitin zcyarsa dake tsananin buga masa cikin zuciyarsa yake fa蓷in.

“Uhm why Jalaluldeen?? Ba haka zuciyanka yake ba, mene yasa kake son wahalantar da zuciyarsa dama 茩wa茩walwarka,
Akan tantance abinda yake damunka ya kuma kawo maka ziyara
Stop this nonsense okey!”
Ya 茩are maganar zucin yana fidda numfashi mai zafi kafin a hankali kuma
Ya ware idanunsa tare da gyara zamansa sosai ya shiga sha茩ar wani sihirtaccen 茩amshi dake ratsa cikin hancinsa,
Yana saukar masa da wata kasala, zuciyarsa da 茩wa茩walwarsa da tilastawa gangar jikinsa abinda bai niyya ba,
Yayinda ya kejin
Wani irin zubewa yaji tsigar jikinsa nayi kafin ya hankali ya 茩ara manna hannunsa dake
Saitin zcyarsa yana murzawa a hankali.

Marai-raice wa Julde tayi kafin a hankali ta 茩ara matsawa inda take jin fitar Numfashinsa,
Cikin wata kalar kasalalliyyar murya tace.
“Ballowo”
Shiru yay mata duk da cewa ya jinta sai ma 茩ara runtse idanunsa da yay.

Fuska ta kwa蓳e tana tura
Bakinta gaba kafin cikin damuwa ta kuma kiran sunansa.
“Ballowo!! Ballowo kayi magana kaji”
Idanunsa dake rufe ya ware tare da mannawa a ganinsa a saman fuskarta.

Wata irin lamintaccen kallo ya shiga aika mata, cikin nutsuwa kuma yake bin jikinta da kallo,
Tun daga kan fararan yatsunta na 茩afa wanda akaiwa adoo da
Red 蓷in jamfarce Hakan yasa suka 茩ara haska kyawawan yatsun nata.

Kafin ya dawo da kallonsa saman cinyoyinta, wata irin mi茩ewa gashin dake 茩wance a 茩irjinsa sukai,
Yana jin yadda nipples 蓷insa suke masa wani irin 茩ai茩ayi wanda bai ta蓳a ji ba,
Idanunsa ya Lumshe dan baya jin zai iya 茩arasa kai idanunsa sauran surar jikin nata.

“Ballowo”
Ta 茩ara kiran sunansa a sanyaye cikin wata kuma dad蓷an Murya mai 蓷auke da zallar shawaga蓳a, wacce take 茩ara
Sanyawa yaji gashin 茩irjinsa na wani irin rawa tare da mimmi茩ewa,
Idanunsa ya 茩ara warware kafin yace.

“Uhm”
Ya fa蓷a can 茩asan ma茩oshinsa yana 茩ara ware fitinannun idanunsa akanta,
Murmushi tayi tace.
“Zuciyata zata fa蓷u, ka daina zama kusa dani”
With much surprised ya shiga Kallonta can kuma ya numfasa kamar bazai magana sai kuma yace.

“To ta fito mana,shine kike wani tsare ni da wasu juyayyun idanunki”
Ya fa蓷a yana taune lips
Kafin tai magana,
Oumuu-Ayman ta shigo hannunta ri茩e da try 蓷in
Breakfast wani table ta 蓷auka ta ajjiye masu kafin ta kalli Abu Maleek tace.

“Zaki Mai Babban 蓷aki na nemanka, tare da Hawwa’u, Nima can zani ga breakfast idan kukai sai ku taho tare, please banda cin zali”
Ta fa蓷a tana mi茩awa Julde plate 蓷in chips sai egg and cheese sandwich.

Shiru yay yana gyara zamansa kafin ya 蓷auki spoon ya fara tsakalar Fried plantains and yam egg stew sai 茩amshi take,
Mi茩ewa Oumuu tayi tsaye tana fa蓷in.

“Please banda cin zali Amana na bar maka ita”
Bai ko kalli Oumuu-Ayman ba, cikin rashin da蓷in yanayin da yake ciki yace.
“Uhm tafi da ita mana”
Gaba Oumuu-Ayman tayi tana fa蓷in.
“Ban niyya ba, Allah Jalal ranka zai 蓳aci”
“Uhm”
Kawai yace domin tunda yaji ta ambaci Jalal yasan babu maganar wasa a cikin kalamanta.

Kai tsaye Oumuu-Ayman sashin Mai Babban 蓷aki ta nufa,
Lokacin kowa yana zaune gaba 蓷aya Aremos suna zaune, hadda Junaid da Salimerh, sai Queen Ayoola da Bola tare da Maleek.

Shiga Oumuu-Ayman tayi kafin ta nemi waje can gefen Mai Babban 蓷aki,
Salimerh kam Murmushi kawai take ta matsu da ganin,
Yarinyar da ake magana, hakan kuma yasa ta 茩ara jin sanyi komai na Abu Maleek yana gab da 茩arewa, soon za’a gane ma茩iya kuma suji kunya.

“Oumuu-Ayman ina yaran naki ne? Ina son muyi magana likitana yana kan hanya kwana biyu 茩afar duk ta daman”
Mai Babban 蓷aki ta fa蓷a tana ta蓳a 茩afarta.

Murmushin da baya yankewa Oumuu-Ayman tayi a saman fuskarta kafin a hankali cikin girmama tace.
“Suna hanya, in sha Allah”
Jinjina kai Mai Babban 蓷aki tayi tana 茩ara shafa rope 蓷in hannunta.

A can 蓳angaren Abu Maleek cin abincin kawai yake ba 蓷an da蓷i ba,
Time to time hakan sauke ajjiyar zuciya tare da juyawa ya
Kalli Julde wacce take cin Abincin a hankali kamar wacce bata son ci, sai juyawa spoon take, a hankali ya janye idanunsa
Kafin ya ajjiye spoon 蓷in hannunsa ya 蓷auki gorar ruwa mai sanyi ya 蓳alle murfin ya manna bakin gorar cikin nasa,
Sosai yasha ruwan kana ya ajjiye yana fesar wata zazzafar iska daga cikin bakinsa.

Mi茩ewa yay a nutse da niyyar barin wajan yaji ta saki 茩ara, da 蓷an sauri ya juya idanunsa ya zaro waje,
Ganin yadda chips 蓷in ya zube mata a fuska wajan idanunta, ga wani 茩aramin yaji ya ma茩ale a tsinin hancinta.

Lumshe idanunsa yay yana jin kukan na dukan tsakiyar kansa,
Cikin nutsuwa ya zame ya zauna a gefenta yana 茩ara narkar da idanunsa a kanta, ganin yadda fuskar tai jajir ne ya sanya a hankali ya mi茩a,
Tafukan hannayensa ya tsalle fuskar gaba 蓷aya,
Kafin a hankali ya sauke numfashi yana jin yadda zuciyarsa ke tsalle kamar zata keto tsakiyar 茩irjinsa ta fito.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button