ABU MALEEK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABU MALEEK COMPLETE

ABU MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani irin sound ya fitar kafin kuma cikin yanayi na son Taimakon ta ya matsa kusanta,
Yana 茩ara kusantu da ita garesa kafin slowly yay 茩asa da fuskarsa wajan Tata, ganin tana Shirin kai hannunta wajan idanunta ne ya sanya,
Yay saurin kama hannunta yay baya dashi tare da matsa kusa da ita sosai cikin wata rigar
Kamilalliyar Muryarsa mai amo yace.

“Wait, ina ke maki zafi?”
Cikin kuka ta narkewa jikinsa tace
“Ballowo ido na, da kuma nan 蓷ina yaji Bafiiii suke wayyoooo”
Jinjina kai yay kafin yace “It’s okay, allow me to see muga”
Shiru tayi tana jin yadda ya 茩ara manna tsakiyar tafin hannunsa a saman fuskarta kafin kuma
Ya 蓷an sanya hannunsa ya bu蓷e idanunta, da sauri tayi kansa ta cukukuye shi saboda tsananin azabar da taji.

A karo na farko tun ha蓷uwar su, da kuma dawowarsa daya saki wani irin lafiyayyan murmushi wanda zai iya firgita dukkan wata macan da tayi katarin gani,
Tsadaddan Murmushi wanda kafin a gani sai an sha wahala.

Murmushi daya haifar da bayyanar wasu irin kyawawa kuma jerarrun teeths 蓷insa, ha蓷i da wani teeths gave na gefe,
Ga wani ha蓷a蓷蓷an dimple wanda yake a iya 蓳angaren kumatun sa na dama.
Fa蓷in kyan da Murmushin yay masa 蓳ata baki ne.

Hannunsa ya sanya ya tallafa ta sosai, kafin a hankali yay 茩asa da bakinsa saman kunanta yace.
“Su Kululuuu manya, kina son jikin mijinki ko?”
Da wani sauri ta 蓷ago da jikinsa tace.
“Ni ba mijina bane, bayan Oumuu tace kai Hamma na ne”
茦uri yay mata kafin yace.
“Meye Hamma?”
Turo bakinta tayi gaba kafin tace “Yayana mana, ai kai kayi 茩ato da zama mijina ko Ballowo”
Kallonta yay Yana jin wani abu mai kama da fargaba na riskarsa.

Bai ce komai ba sai fuskarta da yake kallo, jin hakan yasa ta mi茩a hannunta cikin Sa’a kowa hannunta ya sauka akan fuskarsa, wajan 茩wantaccen sajansa wani irin shafa sajan tayi kafin tace.

“Ballowo wannan abun naka yana da蓷in ta蓳a wa”
Ta fa蓷a tana shafa la蓳蓳ansa kafin kuma ta tura yatsarta cikin madaidaicin bakinsa, ajjiyar zuciya ya sauke yana matse ta sosai a jikinsa yana jin yadda wani sanya yake masa yawo a jiki,
Da sauri kuma tace.
“Wayyoooo Hancina yaji ka cire min”
Idanunsa ya bu蓷e ile kowa abin yajin ne manne a tsinin hancinta, baya jin zai iya 蓷aga hannunsa.

Hakan ya sanya ya 蓷an matsar da fuskarsa sosai wajan fuskar ta,
Kana ya manna la蓳蓳ansa a tsinin hancin nata,
Wani irin maraitaccen numfashi mai kama da 茩ara suka sauke a tare,
Wani irin kyarma da 蓳ari jikin Julde ya fara lokacin da la蓳蓳an Abu Maleek suka sauka fatar hancinta.
Kafin da 茩arfi taja numfashi tana jin yadda numafashi yake gab da barin gangar Jikinta,
Abu Maleek kam lumshe idanunsa yay kafin ya 茩ara sauke numfashi, wani irine Amintaccen si蓷a yaywa tsinin hancin nata, kafin a hankali ya 蓷ura da wani lamintaccen tsotsa inda ya tsotse abin yajin kana ya 蓷iye zuwa cikinsa.

Kauda fuskarsa yay kafin ya 蓳alle medicine 蓷inta yace “uhm haaaa” ma茩ale kafa蓷a tayi kafin cikin muryar shagwa蓳a tace.
“Ni ban son magani Allah amai nake”
Kallonta kawai yay a zuciyarsa yace “Uhm akwai aiki, mitsitsiya da ita sai salo, fitinanniya kawai”
A fili kuma ya 蓷an ya motsa fuska yace.
“Chocolate ne ohyyyah bu蓷e muga”
Jin ya ambaci chocolate yasa ta bu蓷e bakinta da sauri ya watsa mata maganin kafin ya manna mata gorar ruwan a bakinta, cikin sauri ta shanye maganin tana kuka,
Mi茩ewa yay kana ya kama hannunta har yay gaba sai kuma ya tsaya yana kallon kayan jikinta, bai ce komai ba ya juya not too long ya dawo ri茩e da wata abaya mai tsayi.

Ba tare da yace komai ba, ya matsa kusa da ita ya kama hannunta tare da yin sama dasu kana ya zura mata rigar idanunsa 茩uri a tsakiyar cibinta, da sauri kuma ya zura mata abayar ba tare daya kalli jikinta ba.

Kai tsaye sashin Mai Babban 蓷aki ya nufa da ita,
Tana jin wani da蓷i na ratsa mata zuciya jin iska na shigarta tako ina,
Suna shiga kallo ya dawo gare su,
Bola kam idanu kawai ta tsorawa Julde wai wannan za’a ce itace Amintacciyar Hadimar Abu Maleek? Ta ina bayan wannan 茩yakkyawar yarinyar ko matar shugaban 茩asa sai haka,
茦wafa tayi lokacin da Oumuu-Ayman tace.
“Zonan Hawwa’u”
Ta fa蓷a tana ri茩e hannunta, Abu Maleek gefen Mai Babban 蓷aki yaje ya zauna yana 蓷an lumshe idanunsa.

Gyaran murya Mai Babban 蓷aki tayi kafin tace.
“Nasan da yawa ko baku tambaya ba, nasan dole a ranku za kuce Wacece Hawwa’u, to Allahamdulillah Hawwa’u Abu Maleek ne ya tsince ta, a hanyarsa ta dawowa nan gida, a rugar Mahinjo, hakan yasa ya taho da ita domin Taimakon rayuwarta,
Daga baya kuma na yanke shawarar zata zama Amintacciyar Hadimar sa, kamar yadda shima ya za蓳a, to zuwa jibi in sha Allah za’ai mata aikin ido, gata kuma za’a na蓷a tsarki”

Da sauri Shakiru yace.
“Waye Sarkin?”
Kallonsa tayi cike da nutsuwa da kuma karantar yanayinsa kafin tace.
“Zaka gani ranar”
Bola wacce take cike fam tace.
“Oumuu-Ayman na yiwa Abu Maleek komai da yake so, mene ya sanya kuma a wannan karan zai za蓳i wannan budurwar matsayin Hadimarsa? Gaskiya ni ban amince ba”
Ta fa蓷a Idanunta na aikawa da Julde harara wacce take ra蓳e jikin Oumuu-Ayman.

Murmushi Mai Babban 蓷aki tayi kafin tace.
“Daman ba amincewar ki ake bu茩ata ba, an fa蓷a maku ne domin ku sani”
Cikin wani irin yanayi Bola tace.
“Na amince ni ya mayar dani Hadimarsa zan iya yi masa komai ma dadin makauniyar nan kuma TSINTACCIYA”

Gyara zama Mai Babban 蓷aki tayi kafin ta juya ta kalli Julde,kana ta kalli Abu Maleek a nutse ta mayar da Idanunta kan Bola tace.
“Ina tunanin kamar nace Jalaluldeen shine ya za蓳i Hawwa’u matsayin Hadimarsa, kenan wannan 茩orafin mijinki za kiyiwa”
Ta fa蓷a tana nuna Abu Maleek, tsaye ya mi茩e cikin takunsa mai matukar 蓷aukan hankali yay waje hannayensa zube cikin aljihun.

Kuka Bola ta sanya tana fa蓷in.
“Rayuwata da Abu Maleek bata da amfani, rayuwar aure muke ko kuma rayuwar gaba da juna? Bafa ni na tilasta masa zama dani ba, mene ya sanya ya mayar dani abin wula茩antawa? Baya tunanin akwai sanda ha茩茩ina zai kamasa ne Eheee? Baya so na fine amma a kullum ya tuna ina rayuwa a Alaafi ne dalilinsa, i have my own family ina da gata da duk abinda yake tunanin yana dashi, if baya 茩aunar aure na he can divorce me, ba zan magana ba yana da right nayin hakan,
Ko cewa akwai ni dutse ne Eheee?? Ban san da蓷in jikina bane ko menene? Akwai ha茩茩ina a kansa na auratayya,
Ko kuma gantali zan fara ina neman mazan wasu?”
Mi茩ewa tsaye tayi tana sakin kuka kafin tai waje da sauri.

Da idanu gaba 蓷aya suka bita, Julde wacce tausayin Bola ya mamaye zcyrta tace “Oumuu to mene yasa take kuka? Ko akan Ballowo ne”
Shiru Oumuu-Ayman tayi ba tare da tace komai ba, Mai Babban 蓷aki kam mi茩ewa tsaye tayi ganin lokacin Sallah yayi kafin tace.
“Zaku iya tafiya, Oumuu-Ayman kibar Hawwa’u nan”
Tana fa蓷in hakan tai bedroom 蓷inta.

A hankali suka shiga ficewa, banda Adams da yake zaune yan manna idanunsa akan Julde,
Oumuu-Ayman ce ta kalli Julde kafin tace.
“Daughter ki zauna yanzu Hadima Akin zata kaiki bathroom kiyi alwala ki Sallah”
Da sauri Julde tace.
“Oumuu Ballowo fa, ni bana son zama nan kaina ciwo yake”
Kallon Julde Oumuu-Ayman tayi sosai kafin tace.
“Yanzu zai dawo nan Sallah ya tafi kinji ko”
Kai kawai ta 蓷aga ita kuma Oumuu-Ayman tai waje zuwa nata sashin ta.
Tana barin parlo ya sauke Ajjiyar zuciya yana fa蓷in “Munafuka!”
A hankali kuma ya dawo kusa da Julde yana kallonta yana jin kamar ya jata ya rungome ko ya samu sassaucin abinda ya keji a ransa cikin so da kuma 茩aunarta yace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button