ABU MALEEK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABU MALEEK COMPLETE

ABU MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

Ajjiyar zuciya Abu Maleek ya sauke numfashi cikin wani irin ki蓷ima da fitar nutsuwa yace.
“Please Oumuu na, dan Allah kada ki barni, kiga abinda nake gudu ko?
Kinga abinda yasa na gujewa zaman Benin ko?
No one’s love me, ke 蓷aya nake da ita a yanzu, dan Allah Oumuu…..nahhhh!!! Open your eyes Zakin ke magana, Your professional footballer Oumuu, wallahi billahi i promise to you zanyi komai da kikeso,
Amma stay with me Oumuu dan Allah kada ki barni a wannan duniyar da kuma wannan gidan mai cike da rikici, tell them bana son sarautar nan,
Dan Allah Oumuu ki tashi i love You so much I’m nothing without you Maaamahh”
Ya fa蓷a lokacin da idanunsa sukai wani mugun jaa suka sauya kala, jijiyoyin kansa sukai bala’in tashi tsaye, yayinda ya kejin shima tamkar numafashi ne yake tafiya, a yanzu ya tabbatar tsananin son da ya kewa Oumuu-Ayman yafi 茩arfin tunaninsa,
Yana mata son da ko Maminsa baya yiwa wannan son,
Sone tsaftatacce mara algus,
Tun yana 茦arami Oumuu-Ayman ce take masa komai, a wajanta yake kwana yake tashi, a jikinta yake kwanciya, shoulder 蓷inta itace gurbin zubar Hawayen sa,
Gashi yanzu wata sabuwar 茩addarar na son rabasu, wani sabon shafi na sabuwar 茩addarar rayuwarsa zai bu蓷e.
A hankali ya kifa kansa a tsakanin shoulder 蓷inta, a wannan lokacin ko hawaye ya kasa domin rabon da hawaye ya zuba daga cikin idanunsa ya manta, sai ajjiyar zuciya da yake saukewa kawai,
Wata 茩yak茩yawan mi茩a Oumuu tayi kafin a hankali ta samu zarafi bu蓷e bakinta dai-dai kunansa, a gigice ya bu蓷e idanunsa jin abinda tace, a hankali kuma ta 茩ara 茩asa da muryarta tace.
“Jalaluldeen, Zaki na, Cucuu na! Ka nutsu kasan abinda kake, rayuwa bata Tabbas nasha fa蓷a mak….,”
Saurin yin shiru tayi Saboda wani irin fisga da numafshinta yay, kafin wata kumfa ta fito daga cikin bakinta,
茦ara ri茩eta yay a jikinsa sosai kafin jin yadda Jikinta ya saki baki 蓷aya,
Cikin dauriya tace.
“Cucuu na, Amanar Hawwa’u a hannunka, ka zama mai Hqr ko zaka share kowa Banda ha茩茩in matar daya rataya a wuyanka Cucuu, I’m going to my home now, zan tafi inda mahaifinka ya tafi kafin Lokacin ku yayi,
Bana ba茩in cikin mutuwa ta, sai farin ciki domin zan mutu ne dalilin kare taka rayuwar, Nagode Allah da nayi hanzarin kawo maka naka Abincin, kafin na dawo an sauya min Abincin ta hanyar da bazan gane ba, komai na Amincin iri 蓷aya ne babu bambanci, shiyasa ban fahimta ba,
Anyi tunanin naka Abincin ne wannan dalilin aka sanya goba ciki, i love so much Cucuu na,
Nai farin ciki domin Ubangijin bai 蓷auki raina ba sai da ka tabbata a matsayin OBA! Allah ya tayaka ri茩o..”
Runtse idanunta tayi saboda a yanzu number ta gaba 蓷aya iya wuya ne, idan kuma ya tafi baya dawowa,
Idanunta ta bu蓷e tare da 蓷aga hannunta, da sauri Julde ta 茩arasu kusa da ita tace.
“Ba haka mukai dake ba, Oumuu-Ayman ba cemin kikai zaki tafi ki barmu baki 蓷aya, kada ki karya wannan Al’茩awarin Oumuu, kefa jaruma ce, to dan Allah ki tausayawa maraicin mu ki zauna tare damu,
Oumuu mene yasa zaki tafi ki barni da nauyi mai girma akai na?? Mene ya sanya? Eh”
Ta 茩are maganar cikin 蓷acin rai tare da sanya hannunta ta shiga dukan Oumuu da alama tuni ta fice daga hayyacinta ganin haka yasa Oumuu-Ayman sakin wani amintaccen Murmushi, wani zallar annuri na fita daga fuskarta, a hankali ta kalli Abu Maleek,
A wannan lokacin ba zata iya magana ba, sai hannunsa data mana akan na Julde tare da ha蓷e kawo nan su waje guda,
Wani haske take hangowa a goshin ko wanansu,
Yalwataccen Murmushi ta sauke kafin a hankali tace.
“Allahamdulillah”
A hankali kuma idanunta suka fara yin sama, bai san ya mutuwa take 蓷auke Mutum ba, amma daga kan mahaifinsa ya fahimci mutuwa yadda take, bai ji zafi da kuma ra蓷a蓷i a lokacin da Tunde ya rasu ba,
Saboda a wannan lokacin akwai Oumuu-Ayman, ganin Oumuu-Ayman kusa dashi kuma ya kure dukkan wata damuwar dake ransa,
A wannan lokacin kuma zafi da kuma ra蓷a蓷i sun samu wani irin halattaccen gurbi a zuciyarsa,
Yayinda Oumuu-Ayman kuma ta tafi cikin farin ciki da salama da wani annuri saboda ta tafi tabar Jalaluldeen a hannun Julde hannun da bazai ta蓳a cutar da wani Mutum ba,
Bare kuma Abu Maleek,
Ita daman rayuwar haka take baki 蓷aya, dukkan zuciyar da take cike da imani da kuma tausayi da rikon amana, ha蓷i da ri茩o da addini, ranta bazai ta蓳a muzanta wajan 蓷auke sa ba, samaniya da mutanan cikinta a kullum mara ba, suke da irin ran Oumuu-Ayman!
(Nima Na’ima sulaiman Sarauta) Ubangiji ka amshi raina cikin kwanciyar hankali, da nutsuwa da kuma salama da kuma Dukkan musulmi.

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” shine abinda mutanan wajan kawai suke fa蓷a, babu wanda baiji mutuwar Oumuu-Ayman ba, sai wanda yake da sanya hannu a rasuwar nata, mutuwar data girgiza dukkan al’umar dake cikin Alaafin, Barori, Hadimai, Fadawa, Hadima Zubaida kam ko motsi ta kasa, abubuwan masu yawan gaske sunyi mata ca!!! Akanta, hatta Sarkin Kilisa yaji mutuwar Oumuu-Ayman har hawaye ya zubar, kasantuwar duk wanda ya rasu a nan cikin Alaafin ake binnesa yasa nan da nan Alaafi ta cika.
Abu Maleek, da Julde tun lokacin da Oumuu-Ayman ranta ya gama barin gangar Jikinta suma jinsu da ganinsu yabar gangar jikinsu,
A gigice Bola tayi kan Abu Maleek ita da Salimerh yayinda kuma Adams ya nufi kan Julde, hannunsa ya sanya da niyyar 蓷auke ta, amma bisa mamakinsa hannunta sar茩e yake cikin na Abu Maleek, yin duniya ya kasa bisa dole gaba 蓷ayansu aka nufi sashin Abu Maleek dasu, ana kaisu kuma,
Salimerh ta kira Dr dukkan su Drip aka sanya masu tare da wata injection na tsayin 48hours,
Suna kwance kusa da juna kamar gawarwaki.
Daga nan kuma guards 蓷in Abu Maleek suka sanya tsaro mai 茩arfin gaske a sashin Abu Maleek babu mai shiga da fita sai Dr da kuma Mai Babban 蓷aki.

After 2days
Misalin 4:20 na yammacin juma’a, rana mafi farin ciki ga dukkan Musulmi yayinda ranar ta zama ranar tarihi ga Hawwa’u Julde!
A hankali ta shiga bu蓷e idanunta wanda sukai mata nauyin gaske, cikin nutsuwa kuma ta gama bu蓷e idanunta,
Kafin ta 蓷aga hannunta da sauri ta juya saboda jin hannunta a cikin na mutum,
Da sauri ta sauke ajjiyar zuciya, tare 茩ara juyawa sosai, sai a lokacin ta 蓷an fahimci drip ne a hannunta, idanunta ta sauke akan hannunsa dake cikin nata,
Wasu kyawawan gashi ne masu kyau a kwance saman fatar hannunsa sai 茩yalli suke,
茦uri taiwa hannun kafin a hankali ta kalli nata, dashi da ita ta rasa gane wanda yafi wani haske, ita hasken ta har wani yellow yake,
Yayinda nasa kuma har wani jaa yake, kurayan jijiyoyin hannunsa ana ganinsu sosai kamar ka ta蓳a jini ya zuba,
Sai wani zufa dake tsastsafo wa a tsakiyar tafin hannunsa,tana ratsa cikin hannunta,
A hankali ta fara sama da idanunta domin sam ta kasa tuna lokacin da suka kasance a 蓷aki guda, kan gado 蓷aya, hannunsu sar茩e dana juna.
茦yakkyawar fuskarsa mai cike da ilhama ta tsurawa idanu, ya wani mugun fa蓷awa sai wani masifaffan kyau daya 茩ara, a hankali ta mi茩a hannunta cikin nutsuwa kuma ta kifa hannunta a saman fuskarsa,
Ajjiyar zuciya mai 茩arfi ya sauke saboda sanyin tafin hannunta daya ratsa masa fatar fuskarsa,
Yarr-yarr kuma haka tsigar jikinsa suka zubewa tare mimmi茩e, kallonsa tayi cike da so da kuma 茩auna, kafin a hankali ta sanya yatsarta a saman sajansa ta shiga shafawa, tana 蓷an murzawa, tun ba yanzue ba sajan nata yake bala’in birge ta,
茦aramin yatsarta ta 蓷an manna saman jajayen la蓳蓳ansa masu kauri sai she茩i suke, idanunta ta lumshe tana jin wani irin kasalallan yanayi mai wahalar fassaruwa a cikin zuciyarta yana ratsa dukkan ga蓳o蓳in jikinta,
A hankali ta 蓷an shafa la蓳蓳ansa dai-dai lokacin daya 茩ara sakin ajjiyar kafin kuma ya bu蓷e bakinsa a hankali cikin magagin bacci yace.
“Come back! Come to me Maaamahh!!, Kada ki barni Oumuu na”
Dummm! Haka zuciyarta ta buga da 茩arfin gaske, kafin jikinta ya shiga rawa bakin na 蓳ari tace.
“Oumuu”
Sai kuma ta toshe bakinta jin wani kuka na shirin zubu mata, kafin ta matsa kusa dashi sosai tana matse idanunta tare da mayar da kukan da yazo mata,
Cikin tausayin halin da zasu kasance ita da Ballowo 蓷inta ta rankwafa dai-dai kansa cikin wata raunatacciyar murya mafi raunin gaske tace.
“Munyi rashi Ballowo, amma wannan rashin ni nayi sa, na maka al’茩awarin zan maye maka gurbin Oumuu, zan zama fiye da Oumuu-Ayman a rayuwar ka, Ina sonka Cucuu”
Ta fa蓷a tana kwantar da kanta a faffa蓷an 茩irjinsa,
A hankali ta 茩ara manna kanta a 茩irjinsa tana sauraran bugun zcyarsa dake fita dai-dai da nata,
Yayinda wani irin rauni da kuma zafi hadi da ra蓷a蓷i ke ratsa mata dukkan wata 茩ofa ta cikin Zuciyarta,
Mafi yawancin raunin kuma akan Ballowo 蓷inta ne.
A hankali Abu Maleek ya sauke numfashi tare da fesar da iska, gently kuma ya bu蓷e idanunsa da sukai masa nauyi, gaba 蓷aya jijiyoyin kansa sun fito sunyi ra蓷a ra蓷a,
Ga wani azababban huci da kansa ke fitarwa,
Idanunsa ya sauke akan drip 蓷in, yana mamakin dalilin daya sanya aka sa masa wani drip,
茦amshin ha蓷a蓷蓷an turaranta ne ya kawowa hancinsa ziraya, da wani kasala ya lumshe idanunsa tare da yun茩ura wa, zai mi茩e tsaye cikin sauri ta 蓷aga kanta daga jikinsa dai-dai lokacin da yake jingina da jikin frame 蓷in gadon,
Fitanannu jajayen idanunsa ya narke a kanta yana kallon idanunta da sukai jaa ga wasu sabbin Hawayen da suke cikinsu, idanunsa ya fara yawo dashi a Jikinta har ya kawo kan 茩irjinta wanda duk rabi 茩irjin ya fito, 茩arara shatin nipples 蓷inta suna waje,
Shiru yay yana kallon tsarin Halittar 茩irjinta, brest 蓷inta rin wanda akewa la茩abi da mai kan tasa 蓷in nan, wanda abu ne mai wahalar gaske kaga sun zube,
Jin zucyarsa na 茩o茩arin rinjayar gangar jikinsa ne ya sa shi janye idanunsa tare da mayar da shi saman fuskarta, a hankali kuma ya sauke wani lamintaccen numafashi yana mai juya idanunsa, so yake ya tambaye ta mene yasa yake nan? Mene ya samesa.
Ganin kallon da yake mata ne yasa a hankali ta 茩o茩arin zamewa tare 茩o茩arin sauka da kan bed 蓷in,
Hannunsa ya mi茩a tare da ri茩e wrist 蓷inta, da sauri tai 茩asa da kanta saboda wani abu daya shiga yi mata yawo,
Abu Maleek kam halin da yake ciki ya huce bayani sai da a aikace, idanunsa ya lumshe kana ya bu蓷e su agajiye kafin ya bu蓷e bakinsa cikin wata irin kamilalliyar Muryarsa mai da蓷i, mai kuma tarin nauyi yace.
“Jidderhh!!”
Saukar Muryarsa haddasa lumshewar idanunta ba tare data shirya hakan ba, rufe idanunta kuma ya bawa hawayen da suke cikin idanun damar sakkowa, kasa amsa masa tayi sai Ajjiyar zuciya da take saukewa, ganin hakan yasa ya 蓷an zame hannunsa dake kan nata, a hankali ya zare drip 蓷in hannunsa, tare da tattaro raguwar 茩arfinsa ya matsa kusa da ita,
Lallausan hannunsa ya sanya a saman fuskarta tare da ran茩wafawa dai-dai fuskarta, har numafashin su na ha蓷ewa waje guda, kafin kuma ya 蓷an 茩ara matsota kusa dashi sosai, tare da sanya hannunsa a 茩uncin ta ya shafi hawayen idanunta cikin wata irin murya mafi kaushi a tattare da shi yace..
“How long you have been crying?? And where is your glass?”
Ya fa蓷a a taushashe kuma a nutse yayinda yake wasa da yatsarsa a saman fuskarta da zummar goge mata Hawayen,
Bisa tarin mamakinsa mai makon Hawayen ya tsaya sai kawai yaga ta fashe da kuka tare da fa蓷awa jikinsa ta ri茩esa sosai,
Lafiyayyiyar ajjiyar zuciya Cucuu ya sauke lokacin daya jita a jikinsa ganin yadda kuma take kukan sosai ne yashi 蓷an ha蓷e hannayensa a gadon bayanta duk da tsananin azabar daya keji a jikinsa bai hana ya 蓷anyi control na kansa ba,
Ya tattara dukkan hannunsa ya rungome sosai a saman faffa蓷an 茩irjinsa mai yalwataccen gashi, tare da sanya hannu ya fara shafa kanta zuwa bayanta,
Dai-dai kunanta ya 蓷ura bakinsa a hankali cikin wani gigitaccen salo ya fara sakar mata hucin dake fita daga cikin bakinsa, kafin a hankali ya 蓷anyi 茩asa da hannunsa zuwa ass 蓷inta ya zura hannunsa ta 茩asan rigarta,
Wani irin raunataccen numafashi suka sauke a tare, lokacin da tafin hannunsa ya ta蓳a asalin fatar jikinta,
Kafin ya 蓷an bu蓷e bakinsa ka蓷an yace.
“Uhm!” kafin ya 蓷an 茩ara matseta a jikinsa yana 茩ara dai-dai-ta zamansa, cikin lallashi yake 蓷an buga bayanta kafin cikin wata lallausar Muryar mai cike da tausayin abinda ya sanyata kuka yace.
“Cry Na.. nahhhh!! Cry as so much as you can, I got you Okey…. Cry on my shoulder yi kuka Kuluuu!!..”
Shiru yay yana sauke numfashi kafin ya 茩ara manna bakinsa a kunanta yana wura mata dad蓷ar iskar bakinsa yana 蓷an lasar fatar kunanta cikin sigar rarrashi ya 茩ara manneta da jikinsa yace..
“You’ll not die Hawwa’u!!!.. and nothing will happen to you okey Na…nahhhh”
Ya fa蓷a lokacin daya mi茩ar da yatsarsa na tsakiya ya shiga yi mata yawo dashi a tsakiyar bayanta,
Kuka take har wani shu蓷ewa take kamar zata mutu, kukan da gaba 蓷aya tana yinsa ne dalilin Cucuu, bata san yadda zata masa bayanin Oumuu ta barsu ba, bata san kuka yadda zai fahimta ba,
He could feel yadda hawayenta suke ji茩a masa jiki ba, ga wani cizo da dake sakar masa na 蓷imauta.
Sun 蓷auki wajan 30seconds a haka kafin kukan ya sake ta a hankali ta zame jikinta daga nasa tana 茩o茩arin sauka saurin ri茩eta yay kafin ya tsura mata idanunsa masu kaifi, hannunta ya ri茩e kafin da 茩arfi ya matse hannunta da sauri tace.
“Ballowo”
Ta fa蓷a tana kwa蓳e fuska tare tura bakinta gama, la蓳蓳anta ya kalla da sauri ya janye idanunsa kafin ya manna hannunsa a saman fuskarta a hankali kuma ya 蓷ura hannunta a 茩irjinsa dake harbawa da 茩arfi yace.
“Kina son kashe Ni ko???”
Da sauri ta kallesa kafin tace “Ballowo kisa kuma? Ni a’a na zauna dawa”
Ta fa蓷a tana tura bakinta gaba, lumshe idanunsa yay kana ya jingina da jikin bango yana furzar da iska yace.
“To why are you crying?? Kamar dai wani ya mutu”
Innalillahi da sauri Zuciyarta ta buga tare da kallonsa tama rasa mene zata ce masa, yayinda wani Hawayen ke 茩ara sakkowa daga cikin idanunta,
Ganin haka yasa ya 蓷an mi茩a mata hannunsa yace.
“Come here”
Ya fa蓷a yana 茩ara jawota jikinsa cikin rashin sanin ta茩amai mai abinda yake damun duk zuciyoyinsu ya shafa kanta, domin shima ji yake kamar zai saki ihu…
Ajjiyar zuciya ya sauke kafin ya ha蓷a fuskarsu waje guda bakinsa dai-dai nata kafin kuka ya bu蓷e baki yace.
“Gayawa Ballowo 蓷inki mene? Shiru stop cry ok”
Ya fa蓷a yana manna bakinsa saman nata, da sauri ta runtse idanunta tana jin tsigar jikinta na tashi yayinda Jikinta kuma yay sanyi gaba 蓷aya, a hankali ya fidda red tongue 蓷insa tare da zurawa cikin bakinta gam gam ta rufe bakinta ta茩i bashi damar abinda yake son yi, ganin haka ya sanya ya bu蓷e idanunsa tare da kallonta muryarsa na rawa alamar kamar zai kuka yace..
“Na… nahhhh”
Zuciyarta ce ta harba domin bata saba ba sam, wannan very close 蓷in da sukai da juna ji take kamar numafshinta zai fita, kallonta yay domin tuni zuciya ta 蓷ebe sa, sakinta yay tare da sauka daga kan bed 蓷in ya nufi babban Parlo yana dafe kansa tare da fa蓷in.
“Oumuu!! Oumuu where are you Maaamahh!!”
Da wani irin sauri Julde tabi bayansa tare da fa蓷in.
“Ba Oumuu”
Da wani mugun sauri ya juya ya kalleta kafin a hankali ya sulale ya zauna saman kujera..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button