
Allah Ubangiji ya nuna mana Monday lafiya馃槏馃馃徎 idan nai kuskure feel free bawai ka zagen ba dan Allah, 蓷an Adam ajizi ne,a kullum muna yiwa Ubangiji laifi bare 蓷an Adam馃槶
SARAUTAR MARUBUTA
1/11/22, 07:08 – Buhainat馃槤: 95-96
Tai baya luuu zata fa蓷i Junaid yay saurin tare ta, da wani irin hargitsastsan kallo take bin kirjin ko Wannan su, a hankali kuma cikin ru蓷u ta fara bin zanan Taswirar dake 茩irjin ko wannan su,sosai tai mamakin ganin zanan Taswirar yana da bambanci da wacce take jikin Ar蓷o da kuma wacce take jikin Abu Maleek, Murmushi Muhammad Jalal yay yana wani 蓷an lumshe idanunsa kamar yadda Abu Maleek keyi Salimerh ya kalla yace.
“Mamaki ko? Ban san ki ba, i have no idea akan who are you, amma ke har kin samu damar farautar abinda yake ba naki ba? Kin samu damar da zaki kwashe dukiyar da ko mahaifiyar ki bata da iko a kanta balle kuma ke? Uhm kamar nasan da haka, hanyar fitar da kaya ta 茩ar茩ashin 茩asa a Alaafi guda biyu ce, ko kin samu Taswirar jikine Abu Maleek akwai inda zaki 蓳ata a hanya, domin an cire zanan 茩ofa biyu na 茩ar茩ashin 茩asa, kina tafiya hanyar zata bau蓷e maki, Wow! The you know what? Zaki koma hanyar Zanan Taswirar jikina, ita kuma bakinsa yadda zata fitar dake waje ba, hakan yasa zaki 蓳ata 蓳att, ki 茩asa dawowa Alaafi kuma ki 茩asa fita wajan gari, hakan na nufin zaki 茩are rayuwarki ne a cikin 茩ar茩ashin 茩asa” Shiru yay yana sauke numfashi yana jin yadda kansa ke masa ciwo kafin a hankali ya dawo da dubansa ga Malamin Alaafin yace.
“Ka sauya min fuska, kasa anyi min juyan tunanin Mutumin da bashi da imani ko 蓷aya a ransa, ko iya haka na Barka Ubangiji zaimin sakayya dakai, na amince maka na yarda da kai na baka dukkan amanata amma kai watsi da hakan ka ruguza farin ciki na, bana 茩aunar fuskar daka sanya aka samin Kamilalliyar fuskata tafi wannan da take jikina, kamar yadda ka sani mu biyu mahaifin mu Jalal ya haifa, da Tunde da kuma ni Muhammad, nine babba amma ko da nayi aure ban samu haihuwa da wuri ba, sai ya zamana Tunde ya rigani haihuwa ya haifi Sharefddeen, Tunde ba yaji he’s very stubborn wannan dalilin tun kafin yay aure yabar 茩asar, sai da yay auran muka samu labari, lokacin Mahaifin mu ya rasu, Ni kuma naci gaba za ri茩e kujerar sarautar Kanzaf, bisa taimakon Otun da Agba Akin, da Mai Babban 蓷aki, sai kuma 茦war茩wara ta Roomana” shiru yay yana jin wani hawaye na kawowa fuskarsa cikin dauriya ya kalli Salimerh yace.
“You killed my wife, me tayi maki? Akan kawai biyan bu茩atar ki? She’s so nice, friendly Educated ina da tabbacin komai kika ce kina so zata baki, kin kashe min matata ba tare da laifin komai ba, 茩ilan abinda take gudu kenan shi ne yasa ta maida kanta matsayin 茩war茩wara, akwai 茩yakkyawar fahimta tsakanin matata da brother na, akwai wasan 茩anin miji yana girmama ta sosai, shiyasa take kula da shi amma kalli yadda kika kasheta,ta hanya mai muni you killed my wife Salimerh” ya fa蓷a yana zubewa a wajan tare da fashewa da kuka, jikin Abu Maleek ne ya 蓷auki rawa ko ina na jikinsa tsuma yake, duk da cewa ya samu lafiyar 茩wa茩walwarsa amma zafin zuciya ya riga daya samu gurbi a cikin zuciyarsa..
Zame hannunsa yay daga cikin na Julde a hankali yake tafiya zuwa inda Da茩ile take wacce ta kasa koda mutsi, yana zuwa ya sanya hannunsa tare da 蓷auke ta da wani ba hagon bari, 茩arfin marin yasa tai baya da sauri zata fa蓷i Junaid ya sake ri茩e ta.
Jiki na rawa Abu Maleek ya 茩ara 蓷aga hannunsa tare da sauke mata wani marin jiki na rawa kuma ya ri茩e wuyanta tare da sha茩e ta, wani irin nishi ta fara Idanunta ya shiga fitowa.
Ganin hakan yasa Junaid fa蓷in “Abu Maleek ka sake ta please na ro茩e ka, nasan tayi abinda ya cancanci kisa, amma kayi min alfarma saboda cikin dake jikinta” da sauri Queen Roomana ta kallesa jin Abinda yace a hankali kuma tace..
“Wanne ciki kuma? Cikin daya da蓷e da bin rariya lokacin data fa蓷i tun baya, ka kuma manta lokacin da tayi jinya ko ita tace maka tana da ciki”
Baki ya saki cikin rashin fahimta yace “kamar yaya? Bayan ina da tabbacin akwai ciki a jikinta” Murmushi Queen Roomana tayi kafin tace “to gata nan ai, Jalaluldeen sake ta sai tayi masa bayani” Abu Maleek baya gane zan can, idanuna kawai 茩yakkyawar fuskar Oumuu-Ayman suke hasko masa da wani irin 茩arfi yace.
“Kin cuce ni, you blackmailed me, kin kashe min uwa mahaifiya, sai yanzu na fahimci soyayyar da Maaamahh take min ba iya ta mai raino na bace, Zallar soyayyya ce ta uwa da 蓷an ta, sai yanzu na fahimci abinda kalamanta suke nufi na S…J..K tana nufin na kula da macuciya kuma ma yaudariya Salimerh, tana nufin na kula da ha茩茩in daya rataya akai na, na zama gata,da farin cikin Matata Julde, tana nufin bayan ni akwai wani tarbiyyar sa na hannun Allah tana hannu na, na kula da maraicin Khaleluddeen, kina tunanin kin rusa farin ciki daman ai ban bu蓷e ido akan cewa ita ce mahaifiyata ba, look! Kalli can waccan itace mahaifiyar Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal itace uwa ga Abu Maleek, na tsane ki ban sonki Ma茩iyi na bayyana kansa ke kuma sai kika zo min a mace, suffar mutanan 茩warai ki nuna soyayya a gareni ashe ba haka bane,kin 茩ara sanya min tsoran mata, matata itace 茩awata, itace Abokina, itace farin ciki na itace sirrina”
Ya fa蓷a kuka na kwance masa mutuwar Oumuu-Ayman ta dawo masa sabuwa.
A hankali Muhammad Jalal yake kuka zuciyar nayi masa zafi, yana jin zazzafar Kunyar sirikar tasa, Yaywa Julde abubuwa da yawa ya musguna mata, ya batta da yunwa.
A hankali Mai Babban 蓷aki ta mi茩e tsaye ta nufi wajan Ar蓷o kuma Muhammad Jalal tana zuwa ya ring mahaifiyarsa yana fa蓷in.
“Mama” rungomesa Mai Babban 蓷aki tayi tana bubbuga bayansa.
A hankali Queen Roomana ta kalli Julde wacce take tsaye Idanunta har yanzu zubar da hawaye yake, cikin dauriya tace “to kika bari dai mijinki yay kisa kema zaki rasa shi” da sauri ta girgiza kanta hawaye na 茩ara zubu mata, da sauri tai wajansa, lokacin Salimerh ta fara ficewa daga hayyacinta cikin sanyin murya tace..
“Let her go”
Cak ya tsaya yana maida numfashi yana sakinta kuma ta fa蓷i a wajan tana mai da numfashi, cikin sauri ya juya ya rungome Julde yana mai 茩ara sakin wani kukan..
Shiru tayi domin a lokacin ta fisa dauriya cikin lallashi ta dinga shafa kansa ba tare da tace komai ba..
Junaid ne ya kalli Salimerh yace “kin barni cikin duhu ina cikin dake cikin ki?” Idanunta ta rufe hawaye na zubu mata tace.
“Lokacin da naje duba akwatin dana 蓳oye a cikin swwiming pool 蓷in Abu Maleek na tarar babu, cikin gigita na dawo side 蓷ina lokacin baka nan, tashin hankalin da yay min yawa ne yasa nan take jini ya fara zuba a jikina, nasha wahala sosai ina wannan halin ne kuma Hadima Akin ta shigo ita ta saman a lokacin cikin dake jikina tuni yabi jini tunda ba 茩wari yay ba, hakan yasa na bu茩aci ta 蓳oye suma ban su sukaji ba, dalilin ciwon da nayi har asibiti ne yasa likita ya fa蓷a masu 蓳ari nai, nasan Queen Roomana ba zata ta蓳a cewa komai ba shi yasa ban damu da ita ba, damuwa tai min yawa sosai, hakan yasa na shirya wata akwatin da niyyar idan Abu Maleek ya biyo mu zan masa dole akan ya bani dukkan wasu kadarori daya samu da kuma abubuwan company 蓷in sa, da gifts na Daimond, a zurfa daya samu, idan yaban ni kuma zan sake sa, tunda bani da kayan da zan fitar daga cikin Alaafi, banyi tunanin abin zai juye har haka ba,dan Allah 蓷an uwana kayi min rai kaimin afuwa ka haife min sharri she蓷an ne” wani mari Julde ta sauke mata tace..
“Sharrin she蓷aniyya dai, bari kiji tun lokacin dana sanya idanuna akanki nasan cewa baki da gaskiya, koda gubar da kika zuba aka kawowa Mijina ita wallahi noting will happen to him saboda ina iya ganewa ina kuma fahimta, bashi da ikon ya yafe maki,domin rai kika kashe kin kashe mana farin cikin mu idan Kinje Court zaki bayani za kuma ki girbe abinda kika shuka stupid”
Tunda ta fara magana Abu Maleek yake kallon ta,yana jin kalar da蓷i na ratsa masa dukkan zuciyarsa ga wata nutsuwa ta musamman na sakko masa.
Kuka Queen Ayoola ta saki tace.
“Ban ta蓳a nufar kowa da sharri ba, sai Adams dana fa蓷a masa cewa Jalaluldeen ne ya 蓷auke Roomana na fa蓷a ne kuma nima kawai saboda isan inda take amma wallahi babu abinda naiwa kuwa, na haifi yara ban haifi halinsu ba, dukkan abinda akai Maku kune kuka jawa kanku,gwamma Sharefddeen yana da hujjar yi amma ke mene taki hujjar keda mike AGOLA, wacce baki da mara ba sa TSINTACCIYA a gidan”
Shiru ne ya biyo baya Junaid kam kasa cewa komai yay, yana son matarsa sosai, amma yasan dole hukuncin kisa ya hau kan ta.
Bola ce ta gyara zama tace.
“Munji komai amma wanene ya daki Abu Maleek a wannan ranar? Kai kuma Jon wuro mene ya faru a rungar ku bayan barin Zubaida?”
Shakiru ne ya sunkuyar da kansa 茩asa cike da Kunya yace.
“Nine, domin a wannan ranar gaba 蓷aya mu ukun muka fito ana tsaka da ruwan sama, Abu Maleek ya fito daga sashin Queen Roomana zuwa sashin Oumuu-Ayman, ni kuma tsananin kishi ne ya sanya na aikata hakan, musamman daya zamana Abu Maleek ya fini kyau ko nace ya fimu komai na rayuwa, a wannan lokacin kishin sane ya cika min zuciya, koda na aikata kuma nai ladama itana astagafirullah a rai na”
Jinjina kai kowa yay kafin Jon wuro yace.
“Bayan komai ya lafa na kisan da akai, wanda sukai saura daga cikin fulanin suka fara firfitowa daga wajan 蓳oyewer da sukai, a haka kowa ya ha蓷u akaita kukan rashin, Muido kam a wannan lokacin daman bai ko motsa ba, haka kuma muka rasa Shatuu (Zubaida) muna zaune da raguwar Naggen da suka rage wanda gaba 蓷aya mallakin Muido ne, kamar yadda Modibbo ya shaida min, a wannan ranar ne kuma Modibbo ya fita zuwa samu ruwa. Acikin ruwan ya samu jaririyar ko cibi ba’a yanke mata ba, cikin sauri ya kawota wajan Yakumbo, washegari kuma shirya muka kwashe dukkan kayan mu da bukkokin mu muka kama hanyar barin rugar, muna rafe muna yadda zago muna kuma kula da Hawwa’u Julde, a haka muka 蓷auki shekaru masu yawa har Julde tai wayo kafin mu 茩arasu wannan garin muka samu waje gurin nan ya zamana RUGAR MAHINJO, banyi mamakin yadda Ar蓷o yake baya Julde wahala ba domin bashi da imani ko 蓷aya yana son ku蓷i musamman daya fahimci duk Naggen da sukai saura nata ne, to Allah sarki ashe shima bayin kansa bane bai san abinda yake aikatawa ba” shiru ne ya biyo baya kowa abinda yake tunani a ransa daban, yayinda kuma rashin Oumuu-Ayman ya dawo sabo a zuciyar ko wannan su.
Lura da halin da Abu Maleek yake ciki ne yasa Julde kama hannunsa a hankali yabi bayanta, Queen Roomana, Adams, Mai Babban 蓷aki, Bola, Shakiru, Junaid da sauran su ga a 蓷aya mi茩ewa sukai domin lokacin sallar zhur yayi.
Bayan sun idar da sallar da Muhammad Jalal ya jasu ne suka shiga cikin bukka, Zallar madara aka tasu masu sai hucin zafin take tana 蓷umama musu.
A hankali suke tafiya cike da nutsuwa kana kallon su kaga cikakkun masoya masu masifar son junansu.
A ba茩in wata ga蓳ar ruwa suka tsaya a hankali Julde ta matsa kusa dashi ta bayansa, dukkan hannunta ta 蓷ura saman ququnsa tare da kwantar da kanta a bayansa, a hankali take shafa 茩irjinsa tare da murza 茩wantaccen gashin 茩irjinsa, cikin 茩asa da Murya tace.
“Love is something beautiful, and a feeling that one will like to carch. Love is the feeling that makes you feel alive, Ina sonka Ballowo, zuciyata tana maka sahihin so da 茩aunar da ita kanta bata san adadinsa ba, kowa iyaye suna zame masa gurbin farin ciki kuma Garkuwa ga rayuwa duk yaransu, amma ka zame dukkan abinda wata mace take bu茩atar samu a rayuwa, So a baki ba shine ba, a daraja kalmar da kuma wanda ake so Shine cikar SO shine aka bawa so dukkan ha茩茩insa, I love you so much Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal ina fatan zuciyarka zata suni kwatankwacin yadda nake SONKA“
Wasu hawaye ne suka sakko mata a hankali hawayen kuma ke sauka bayan, lumshe idanunsa yay yana jin zuciyarsa na wani irin fitinannan harbawa.
A hankali ya sauke Ajjiyar zuciya tare da sanya hannunsa ya jawo ta zuwa gabansa, kyawawan idanunsa masu 蓷auke da so da 茩aunar ta ha蓷i da masifaffiyyar sha’awar ta, kasa ce mata komai yay sai zamewa da yayi ya zauna a ga蓳ar kogin yare da zura 茩afafuwansa a ciki yana Ka蓷awa.
Idanunsa ya 蓷aga a hankali ya kalleta a taushashe yace “have a set” ya fa蓷a yana kama hannunta zama tayi kusa dashi tare da 蓷ura kanta a saman kafa蓷arsa cikin sauke ajjiyar ya kama hannunta yana murzawa tsakiyar tafin hannun nata yace.
“Kalli yadda kifi suke wasa a ruwan, kalli how happy da suke ciki uhm” Shiru yay tare da zameta ya 蓷ura ta akan cinyarsa yana shafa gashinta daya hargitse kafin a taushashe cikin wata kasalalliyyar murya mafi kaushi yace.
“Farin cikin kifayen nan bazai ta蓳a tabbata ba sai suna cikin wannan ruwan, a duk sanda 蓷aya daga cikin su yabar ruwan to tabbas adadin kwanakin rayuwarsa ne ya 茩are” shiru yay a hankali kuma ya tura hannunsu cikin rigarta cikin nutsuwa yake shafa lafaffan cikinta wanda yake a manne da mara, lubb tayi jikinsa tana jin wani irin da蓷i da nutsuwa na ratsa mata zuciya.
Cibiyarta ya murza da sauri ta lumshe idanunta tana 茩ara narke masa kafin taja wani sauti mai 蓷auke da bu茩atuwar mijin nata, shiru tayi irin shirun nan na bani da mafita sai abinda akace.
“Uhmm 苼allo….” Saurin kifa fuskarta tayi a tsakiyar cikinsa lokacin da ya kifa hannunsa a saman brest 蓷inta, wata Sassanyar iska ya sauke kafin yace.
“You’re my life Naaa… nahhhh, ni kece cikon rayuwarta I hope you understand that I will ove you untill the end, because .you are notjust my girl. But you are also my best friend, akanki nasan cewa nima cikakken namiji ne mai zuciyar soyayya, Abu Maleek da zuciyarsa duk naki i love You too”
Kallonsa tayi hankalin gira ya 蓷aka mata yace.
“YES! I know you love me, And i love You more and More Jidderhh, if Anything happens to you wallahi I’ll die mutuwa zanyi” wani kalar Murmushi tayi taji duk yunwar da take ji ya kau,a hankali ta gyara zaman ta a cinyarsa fuskarta dai-dai saman nashi tana kallonsa, a hankali yake jifanta da wani irin kallo na so da 茩auna yana yawo da narkakkun idanunsa akan fuskarsa.
Hannunta ta sanya tana shafa sajan fuskarsa a hankali ta 蓷ura yatsunta akan la蓳蓳ansa tana shafawa tace.
“I love You Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal” a hankali shima ya 蓷ura hannunsa a saman fuskarta yace.
“I love You Hawwa’u Julde Muido” lumshe idanunta tayi kana ta bu蓷e tana 茩ara shafa masa la蓳蓳ansa tace.
“Ina son ka My heart will forever beat for you My King”
Narke mata fuska yay murya a raunace yace.
“My heart,my soul, my everything will forever beat for only you Naa.. nahhhh Hawwa’u”
Kasa daurewa tayi sharr sharrr hawaye suka shiga bin fuskarta cikin Muryar kuka tace.
“My feeling love you, and my. heart just far you. I will love you forever. I miss you 鈥榤ydear”
Murmushi yay tare da mi茩ewa tsaye bayan ya zareta a jikinsa, a hankali a sanya hannunsa a cikin aljihun wandonsa wata 茩arar box mai tsananin kyau ya 蓷auko.
Zubewa yay a gabanta tare da bu蓷e box 蓷in ya zaro ha蓷a蓷蓷an ring 蓷in da yake ciki sai she茩i yake.
Hannunsu ya mi茩a ya kama nata yana dur茩osa gabanta akan gwiwoyinsa yace.
“You’ll be with me forever and ever Naa… nahhhh?” Da sauri ta 蓷aga masa kanta tana toshe bakinta saboda kukan da tazo mata, hannunta ya kama kamar a India ya sanya mata ring 蓷in idanunsa na zubar da hawaye yace.
“Jalaluldeen Loves you Queen Hawwa’u Julde Muido, I promise to love you, And love you,And too love you regardless of anything and everything Queen Hawwa’u Julde Muido, Jalaluldeen LOVE’S YOU”
Kukan ne ya kwace mata kawai ta fa蓷a jikinsa ta 茩an茩amesa tana sakin wani irin gigitaccen kuka bayanta kawai ya shiga shafawa.
Kafin gently ya zareta daga jikinsa tare da tallafo fuskarta, slowly ya manna tashi fuskar akan nata yana sauke mata fitinan huci daga bakinsa, red tongue 蓷insa ya fidda tare da manna a saman zara-zaran eyes lashes 蓷inta cikin nutsuwa ya shiga shanye hawayenta ta tass yana jin yadda take sauke ajjiyar zuciya, bakinsa ya manna a goshinta ya sauke mata wani sassanyan kiss a wajan, kafin ya zare jikinsa yace.
“Look! I got you something” idanunta ta bu蓷e wani 茩aton kifi ta gani a hannunsa yana motsi, da sauri ya ma茩ale sa tace.
“Cucuu tsolo ina” Murmushi Yay mata yana lakace mata hanci yace.
“Eyee! Za kizo kice za kici ne kin manta last time ko lokaci kina 拼ar 茩wailar ki” Murmushi tayi masa tana ganin har kifin ya mutu ya ha蓷a hutu ya gasawa, idanu kawai ta bisa dashi hakan ya tuna mata da farkon ha蓷uwar su, kallonta yay yace “Ohyyyah come here” wajansa ta 茩arasa yawon ta har tsiyaya yake tana zuwa ya tura mata yace “Eat” kwa蓳e fuska tayi tace “kai fa” yana ka蓷a mata harshansa yace “You first then me” bata tsaya jiransa ba hannu baka hannu 茩warya ta fara ci.
Da idanu kawai yake binta yana mamakin yadda ta kecin kifin wanda ko magi babu cikinsa, tana ci kamar wai zai kwace mata sai da ta kaji dan kanta ta cire hannunta tana kallonsa, ganin yadda ya kafeta da narkakkun idanunsa yana sakin wani irin fitinannan Murmushi yasa ta tura baki gaba, shafa sumar kansa yay zuwa sajansa cikin wata kasalalliyyar murya yace.
“Uhm sannu da aiki sannu cinye du” dariya tayi tace “Allah yunwa na keji fa 苼allowaaaaa” hararar wasa yay mata kafin ya ta蓳e bakinsa yace. ” I knw your problem yarinya ba yin kanki bane” idanunta ta juya masa tare da matsawa kusa dashi ta kwanta saman cinyarsa tace “to laifin waye Mijina?” Hannunsa me kyau 蓷in yasa yaja hancinta yace “Nawa mana, na yi maki ciki ai shike saki kuka zama sarkin ci kamar garan” lumshe idanunta tayi sosai tana fatan Allah ya sanya haka ne.
茦uri tayi masa da idanu tana kallon Zallar kyansa da tarin haibarsa uwa uba nutsuwarsa da kamewa, gira ya 蓷aga mata yace “ya dai My Queen?” Murmushi tayi kafin a hankali ta manna masa bakinta a kumatunsa ta bashi light kiss tare da fa蓷in.
“Kana da kyau Mijina” bai kulata ba domin yasan neman magana take, a hankali yaci gaba da cin kifin yana 蓷an lumshe idanunsa, ganin yay mata banza yasa tai 茩wafa a hankali ta 蓷aga hannunta tare da sauke shi a saman mararsa ta 蓷an 蓷aga rigar jikinsa.
A hankali ta shiga murza hannunta a saman mararsa tana 蓷an 蓷aga bakin wandonsa, idanunsa ya lumshe yana jin yadda tsigar jikinsa ke wani irin tashi tana zubewa, a hankali kuma yake jin hannunta duk cikin wandonsa, wata kasalalliyyar ajjiyar zuciya ya sauke yana wani irin fidda numfashi tare da matseta sosai a jikinsa a hankali kuma jikinsa ya shiga wani irin rawa dalilin saukar hannunta da yaji ta cafke masa Jalal 蓷insa tana wani irin murza ta, kifin dake bakinsa ya fitar da sauri yana mai fisge hannunta daga cikin wandon.
Da sauri ya rungume ta yana lumshe idanunsa jikinsa na wani irin rawa ya tura kansa a tsakiyar kanta yana fidda numfashin wahala..
A hankali kuma ya fara jin nutsuwarsa na dai-dai cikin irin da茩ushewar Murya yace.
“Baki da tausayi My Queen” 茩ara shigewa jikinsa tayi tana dariya kafin tace “to me nai maka?” Bakinsa ya taune yana mi茩ewa tsaye da ita zuwa gefen ruwan yace “haka za kice? Kawai ki nemi zautar dani ki sani ihun da banyi niyya ba, haka kurum ba zan barki ki cuce ni ba yarinya dan nasan bazan iya komai dake a nan ba da kin gane kuranki ai” dariya tayi masa sosai yana kallonta yana jin da蓷i a haka suka wanke hannunsu kafin su dawo cikin Rugar.
Lokacin da suka dawo su Muhammad Jalal Ar蓷o sun idar da Sallah dan haka kawai sai Abu Maleek yay alwala shima yay Sallah tare da matarsa,a cikin bukkar suka zauna wanda tuni bacci ya 蓷auke Julde a saman cinyar Abu Maleek..
A hankali Queen Roomana ta shigo cikin bukkar hannunta 蓷auke da 茩wayar nono wacce aka tatso zama tayi tana fa蓷in.
“To Zaki yanzu ka zama mara kunya ko?” Kwa蓳e fuska yay tare da fa蓷in “Mami” harararsa tayi tace “Mami me? Ka wani 蓷auke matarka zuwa wani wajan ko Kunyar mahaifinka ba kayi tunda mu ka raina mu” langwa蓳ar da kansa gefe yay yace “Ayyah! Mami ba haka bane, tace wai yunwa ta keji fa” shiru tai masa gudun kada yace wani abun kuma.
Gyara zama tayi tace “zaka kwana tare da mahaifinka, Julde zata kwana wajan mahaifiyar ta, da safe jirgin mu zai tashi hadda shi Jon wuro zai zama Ar蓷on rugar Mahinjo, Lami蓷o zaici gaba da kula da Naggen matarka domin zamu koma har Zubaida ne” jinjina kansa kawai yay tayaya zai iya bacci babu matarsa bayin tsayin kwanakin da suka shafe basu tare da juna? To Tayaya zai iya bacci wajan Ar蓷o ma? Kallonsa Queen Roomana tayi tace “ta she ta” idanunsa ya 蓷aga ya kalli Mami kamar zai kuka haka ya fara 蓷an buga kumatun Julde, hankali ta bu蓷e idanunta kafin tai wani abu yay sauri cewa “Mami na magana” gudun kada taja masu abin kunya, da sauri ta tashi daga jikinsa wata kunya ta kamata sosai mi茩ewa Queen Roomana tayi hakan yasa Julde ta bita, suna fita Muhammad Jalal Ar蓷o ya shigo da wani irin sauri Abu Maleek ya mi茩e zai fita saboda wata kunyar mahaifin nasa ne ya kamashi, Murmushi Muhammad Jalal yay kafin a hankali yace “Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal wait” cak Abu Maleek ya tsaya a hankali kuma Muhammad Jalal (Baffa) ya jawo Abu Maleek jikinsa ajjiyar zuciya duk suka sauke kafin cikin shasshe茩ar kuka yace “Am sorry Baffa, Am sorry” bayansa ya shafa yace “ya isa, tun lokacin dana fara ganinka jikina yay sanyi na kejin kamar dai na sanka, har cemin akai na kashe ka amma naki, Haka kawai naji zuciyata ta aminta na baka Julde matsayin mata wannan dalilin yasa ka shiga cikin gasar har kayi nasara, Ina tsananin jin kunyar matarka Jalaluldeen na mata abu da yawa” girgiza kai Abu Maleek yay kafin yace “No! Baffa komai kayi baka da masaniya san yaka akai, ina da tabbacin kuma Queen zata yafe maka” Murmushi Baffa yay yace “I hope so…”
Sun jima a haka kafin su kwanta Abu Maleek na jikin Baffansa, Julde ba sun jima tare da Hadima Zubaida.
Washegari bayan sunyi sallah ko ruwa basu sha ba, suka fara shiri a nan ake shaidawa Muhammad Jalal Barkido yaje yiwa Julde fya蓷e sai fa蓷a cikin ruwa har yanzu ba’a same sa ba, sosai Baffan yaji babu da蓷i mutanan Rugar Mahinjo suka dinga kukan tafiyar Ar蓷o Jon wuro kuma ya tsaya akan komai, Baffa da Abu Maleek tare da Adams da Junaid da Sharefddeen da Shakiru sai Otun da Agba Akin jirgi 蓷aya suka shiga, lumshe idanunsa Abu Maleek yay da sauri kuma ya 蓷aga jin ana magana da 茩arfi da 茩asan jirgin, cikin sauri ya fito Queen Roomana ce tsaye yana zuwa tace “Abu Maleek matarka mun neme ta mun rasa” da wani irin 茩arfi yace…