ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin sauri ta fito ta tsaya gabanshi ta sadda kai a kasa don ta tabbata ba abun kirki ya kawoshi ba……Gulmammun matan gidansu da ba’a kira ba suma suka fito sukayi cirko cirko tsarkar gida suna jiran su ji ta inda zai fara ci mata mutunci’

Bata fuska yayi yana hura hanci yace “Ina kudin da bak’ona ya baki……?

Kanta na K’asa tace “Suna a daki na aje! idan Umma ta gama Sallah zan gwada mata “

Hura hanci ya kuma yana fadin “Rabasu Uku ki bani kashi biyu……!

Da Sauri ta kalleshi take idanunta suka ciko da kwallah tace “Dan Allah mai ungua ka rufa man asiri ka bar kud’in dan Allah! wallahi ko langa Ummana bata sayar man ba da za’a ba uwar mijina!Yan kudin da muka tara kwanaki an sacesu tun dazu ummana ke kuka bata da abunda zata kai man a daki !Dan Allah ka rufa mana asiri tunda Allah yaji k’anmu mun samu !Wallahi idan bamu sayi komae ba Gori zamu sha da cin mutunci har ya’ya’ da jikoki……”

Banzan kallo ya watsa mata yana fadin “Bansan Shashanci banza !idan da bai baki kudin ba ya zakuyi!Ni mai unguwa nace kije ki raba kudi uku ki kawon kaso biyu idan kuma kika kara magana da k’warank’wasa duka zan karbe “

Jummai ta tabe baki cike da bakinciki tace “Wallahi kama yi masu arziki da baka amshe duka ba Yo aikin me ta mashi da zai bata kud’i……!

Laminde ta dauka da fadin “Yo Banda ma kana adalin Mai unguwa taya zaka bata kaso daya ka dauki biyu bayan gurinka yazo! aikin uban me ta mashi……?

Washe baki yayi yana fadin “Kin kuma yi Gaskia Laminde ……”

Lauratu ta fito rike da kudin a hannunta ta mika mashi Dubu Shidda ta dauki Hudu tana hawaye …… kirgawa yayi yana fadin “Dubu Shidda kenan !ke nawa ne a hannunki?

A Hankali tace “Dubu Hudu ne”

Bahaggun salati suka dauka suna fadin “Amma dae Lauratu anyi munafuka!Ina laifin ki dauki dubu uku tunda uku yace ki raba !wato mai unguwa zaki munafunta ko ?

Girgiza kai tayi tana kokarin danne kukanta tana fadin “Wallahi a’a canji zan samo na cika mashi jikka uku da murtala……”

Jummai tace “Uwar canji zaki samo bayan kin lahe kudi a hannunki !an dae ji kunya har mai unguwa ba’a raga mawa ba……”

Warce kudin yayi daga hannunta yana fadin “Kin rasa duka wallahi munafuka kawae !ni wallahi na gaji da zamanku a wannan kauyen kun dauko zunubi kun hana mana bunkasar arziki……”

“A Hayye……”Matan gidan suka dauko tare da kashewa suna dariya !Wata ta dauka “Mun ga abunda uwar taki zata hada maki zuwa gobe tunda an karbe wadannan masu bakin hali anyo abun kunya an dawo an tile mana anan …”

K’arama dake tsaye bakin kofar bukka tana murda hannunta ta kallesu tare da kwashewa da dariya tana tabe baki “Wae abun kunya an tilele……”ta fada tana saukowa daga tudunkar ta nufo Lauratu dake kuka tace “Sae kiyi Hakuri Tunda shima ku’in (Kudin)nashi zubewa zasu har da na aljihunshi……”

“To Mai bakin baki ……”Cewar Zulai matar Ardo tare da matsowa tana kallonta

“Anya K’arama ba Mayya bace?Jummai ta amshe tana rike Hab’a

“Idan itace ma yanzu zanyi maganinta wallahi!Jummai samman barkono da Tsakin kuka tare da kakkabin daudawa……”Zulai ta fada tare da fincikarta ta wulla wata tsohuwar Bukka dake kusa dasu……

Da Sauri Lauratu ta rike Zulai tana fadin “Wallahi Inna Zulai ba Mayya bace dan Allah karki mata hayaki yarinya ce……”

“Idan ba mayya bace ki bari a mata hayakin mana Tsohuwar munafuka” Jummai ta fada tare da mikawa Zulai Barkonon da tsakin kuka da Daudawa har da uban garwashin da ta debo a katuwar tukunya……

Da Gudu Laure ta nufi Bukkarsu tana fadin “Umma dan Allah ki fito wallahi zasu kashe K’arama wae mayya ce”Turus tayi ganin Umman nasu tsaye tana lekensu ta wata yar kofar dake cikin bukkar tana kuka……

Cikin kuka tace “Umma ki fito dan Girman Allah……”

Girgiza mata kai tayi tare da rufe bakinta ta sulale gurin ta fashe da kuka mara sauti ……Sanin ko zata kwana a gurin Umman nasu bazata fita ba ya sata fita daga dakin da gudu ta nufi tsakar gida ……

Tari ta fara da karfi tana dafe kirjinta jin azabar barkonon dake fitowa cikin Bukkar da suka rufe K’arama ……Bukkar ta nufa jin Tarin da K’arama keyi tana kokarin budewa amma Jummai ta kwalfa mata mari tare da hankadata gefe tana fadin ” Yau ADUNDA KE B’OYE Ga wagga yarinya sae ya fito dan ubanki ……Kuma da k’warank’wasa ya tabbata mayyace sae mun hada wuta mun jefa Shegiya”

Har Sae da Hayakin ya bar fitowa daga Bukkar sannan Zulai ta bude, lokaci guda ta waro ido tare da ja da baya tana fadin “Na ga Shegiyar yarinya !Wato dan ubanki carafke kike ko ……”ta fada hade da karasawa cikin dakin ta janyota tare da watsa mata mari tana fadin “Idan ke ba mayya bace to ke Shegiya ce kuwa!

Kwace hannunta tayi tana wurga mata Harara ta K’asan ido tace “Kece Mayyan Julai……”

Sannan tayi gaba ta barsu tana tsallenta har ta shige Bukkarsu ta fada saman cinyar Umman tana fadin “Na ci dad’i yau Ummanmu……”

Kasa ce mata komae tayi sae rungumota da tayi tana kuka ……Ita kam K’arama bata ga abun kuka ba don ta haka ta ware idanu tana kallon Umman tata ko kyaftawa batayi……

Lauratu kam bayan Zulai ta mareta bayan gida ta zagaya ta zauna tare da hade kai da guiwa tana kuka ……Dafata da akayi ne ya sata dagowa da sauri tana kallon Matashiyar yar fillon dake tsugunne gabanta ……

Cikin Fara’a yar fillon ta janye hannunta daga jikin lauratun sannan ta janyo wata karamar jikka ta mika mata ……K’in karba tayi tana kallon Yar fillon cikin rashin sani don bata taba ganin mai ko kama da ita ba a yankinsu……

“Ungo Lauratu……”Yar fillon ta fada tare da kamo hannunta ta daura mata jikkar ……Kafin ta bata amsa ta mike da sauri ta bar gurin……

Kallon Jikkar Lauratu tayi a sanyaye sannan ta mike ta koma cikin gida har lokacin tana kuka mara sauti ……Ganin matan gidan ko wace ta kama harkar gabanta yasa ta shige bukkarsu da sauri……Ganin Umma kuka ya sata sulalewa a k’asa tare da yarda jikkar ta hau nata kuka ……Ita kam K’arama raba ido take ta kallansu……

《》《》《》《》

Ma’aruf kam tunda suka shiga motar ya rufe idonshi gam ya kasa budewa K’arama yake hangowa lokacin da ta saka k’azamin hannunta ta shafi sajenshi !K’ara runtse idonshi yayi yana girgiza kai ……

Driver ya kalleshi yace “Sir da matsala ne……?

Girgiza mashi kai yayi a hankali yana ware hannunshi daga jikinshi……Guard din ta saki dariya cikin sigar jan hankali tace “Sir ya hadu da aljana ne……”

“Haba dae……”Driver ya fada yana dariya a hankali……

Dariya ta kuma yi tare da leko kanta tana kallon Ma’aruf din tace “Serious!Sir ka bude idonka mun bar garin sossae fa……”ta karashe maganar tana kashe murya……

Duk abunda suke fada yana jinsu amma tsabar Aji irin nashi ya hanashi bude ido bara ya kula su ……

Office dinsu suka yi parking lokacin Yan’mata ke ta dawowa daga aikin da suka fita ……

Katuwar tabarma ce cikin barandar office din Focal Persons na wards tare da team volunteer da CCO da Facilitator ke zaune suna cin abinci hankalinsu kwance……

Rab’a su yayi ya wuce ya zauna bisa kujeran dake gefe guda tare da rufe ido kamar yana ganin wani abun cuta……

Gaidashi sukayi ya amsa masu ta hanyar daga masu hannu ba tare da ya bude idonshi ba ……

Facilitator ya matsa yana fadin “You’re welcome sir!Tun dazu Director ke jiranka
a ciki……!

HAJJA CE????
&
FEEDOHM????
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button