ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Bude ido yayi yana kallonsu sannan ya bude baki da kyar yana fadin “Am Ok……!
Da Sauri Facilitator yace “Sorry Sir wallahi ban san wannan shashancin zai faru ba da dani aka je kauyen!
Maida idonshi yayi ya rufe yana fadin “Is ok……
Bala’i Facilitator din ya cigaba da yi shi kadae ita kanta Guard din tayi nadamar fada da tayi ……Sae da yayi mai isarshi sannan ya shiga ya kira Director din ……Sama sama suka cigaba da maganar sannan aka kawo mashi abinci amma yarda suka aje haka ya barshi har sae da lokacin meeting yayi sannan ya mike suka tafi ……
A Gurin meeting din ma sae da Facilitator ya fadawa Hakimi abunda ya faru ……Shi kanshi hakimin cewa yayi zai saka a kira mashi Mai unguwa Audun yaji dalilinshi na barin yara suna zuwa gurin bak’onsu har su tabashi……
Shi kam wanda akeyi donshi banza ya masu don bai ga abun tada jijiyoyin wuya ba!aciki bakin cikinshi d’aya kayanshi da ta b’ata tare da fitsarin da ta mashi a kaya, ga wani irin wari da yake ji yana yi duk idan ya rufe idonshi ……
【】
Mai unguwa kam tunda ya karbi kudin ya soke aljihu ya kama dan kekenshi ya haye ya yanki daji yana y’ar wak’arshi a hankali ……Yayi nisa da tafiya ya hangi wata yar K’aramar yarinya tsaye gefen hanya tana kuka ……
Sae da yaje gabanta sannan ya tsayar da keken da kyar yana kallonta yace “Na ci Gidanku !Banda iskanci sae yara su zo su tsaya tsakiyar hanya suna wa mutane kuka !Ina iyayenki……”
Da Hannu yarinyar ta nuna mashi cikin daji har lokacin tana kuka !Tsaki yaja yana fadin “Ni k’warank’watsa ma ban taba ganin mai kalarku ba a cikin yankina ……dan biri “ya karashe maganar yana dariya sannan yace “Ke yarinya yaushe kuka dawo nan yankin?
Da katuwar Murya tace “K’wanan mu biyar……”
Dariya ya saki yana fadin “Kam bala’i ka ji man yarinyar da Muryar k’arti !Ba mamaki wannan K’wababbar fuskar taki ita ta dace da wannan Hegiyar muryartaki……”Ya karashe maganar yana dariya……
Kafe kekenshi yayi jikin hanyar Sannan yayi hanyar da ta nuna mashi yana nade katuwar rigarshi yace “Mu je ki gwada man iyayen naki naji shegen da ya basu damar zama a yankina ba tare da izini na ba……”
Bata ce mashi komae ba tayi gaba ya bi bayanta sae surutai yake shi kadae……Tafiya sukayi mai nisan gaske amma da yake ya shirya rashin kirki bai lura da nisan ba!Wasu yan bukkoki suka iske a tsakiyar daji sannan ta shige bukkar da sauri ta barshi tsaye ……
Wage baki yayi yana fadin “Owoo ni za’awa Shegantaka a barni tsaye? to yayi dai dai yarinya ba da ke zanyi ba yanzu da iyayenki zanyi !
Daga Murya yayi yana fadin “Bai zama dole na maku sallama ba tunda ban san da zamanku a yanki na ba!Ina mai gidan fiton ka fada man wane Shege ya baka izinin zama k’asata ba tare da yarda ta ba……”
Wani dattijo ya fito sanye da rawani irin na buzaye yana fadin “Marhaban wa ke kirana haka ……?
“Mai ungua Audu ne……!ya fada yana mazurai
“Maraba mai unguwa……”Tsohun ya fada yana matsowa
“Ba wani maraba dattijo zuwa nayi naji wane she……”Maganar ta katse ganin bindi a bayan dattijon
Girgiza kai tsohun yayi yana fadin "Ka ce mene Mai unguwa Audu?
Mazari ya fara yana fadin “Na…ce rigim rigigim !na kuma cewa Bindi……”Kwasawa yayi da gudu yana nade babbar riga !gudun ya tsaya lokacin da wasu karnuka suka tare mashi gaba……Ihu ya saki yana sakin fitsari kafin ya canza hanya ya kara kwasa da gudu……
Gudu ta dinga yi cikin dajin yana haki yayin da karnukan suka mara mashi baya suna wani irin Haushi ……Da kyar ya fito hanya! bai tsaya daukar kekenshi ba ya yanki hanyar Garinshi ……Sae da suka kusa shiga garin sannan karnukan suka daina binshi suka juya suka shige daji ……
Kusa da gidanshi sukayi Karo da Mai tafasa ya ja numfashi ya tsaya yana fadin “Na Shiga Uku ni Audu wane irin mutane ne yau na gani……”
Watsa mashi harara tayi tana fadin “Amma dae Mai unguwa Audu an tab’e !Me ya biyo maza da suke tafiya suna sakin fitsari a wando?
“Ke Mai tafasa bana son ruwan tabbata nine na Tabe……”ya fada har lokacin yana haki
Watsa hannu tayi tana fadin “Idan akwae wani Audu mai jikakken wando anan gurin to dashi nake !Bana son munafunci bani kudin Tafasa ta da ka ci jiya!……ta karashe maganar tare da wurga mashi hannu kusa da fuska
Tsaki ya saki yana fadin “Don kina bina Muttala zaki shine zaki man tabbata……!ga dubu ki bani canjina kuma da k’warank’watsa ko motsi ba zakiyi ba sae kin bani canjina……”ya karashe maganar tare da lalubo aljihunshi ……
Ido ya wurgu waje jin babu komai a aljihun sae kullin wani abu a leda ……Fiddon shi yayi da sauri yana jujjuyawa ganin Nono ne kindirmo a cikin ledar “Wa kuma ya bani nono……”Ya fada tare da maida hannunshi aljihu yana lalubar kudin amma wayam babu su ……
A rude yake fadin “To ina na yarda kudinnan……”
Juya mashi baya tayi tana d’age kallabinta ta fiddo keya tace “Koma ina ka yardasu Mai tafasa dai kudinta take bukata……”
“Kinga wallahi Mai tafasa da kudin aljihuna……”Ya fada kamar yayi kuka……
“Wallahi banda mutunci Audu ka fiddo man kudina yanzu !
Da kyar ya lallabeta ta hakura ta tafi gida tana mita……sannan ya shiga gida kamar ya fasa ihu yana tunanin kila gurin gudu ya yarda kud’in kuma babu damar komawa ya duba ……Bai samu ya samu sauki ba sae da ya fitar da kwallah saboda bak’in cikin kud’in !Ranar duk wanda ya mashi magana a gidan zai sha zagine har na fitar hankali……ji yayi dama ya barwa Lauratun kudin bai karba ba……
HAJJA CE????
&
FEEDOHM????
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》
????????
????
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM????
&
_K.A.S Precious HAJJA CE????
SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyar mu
Page *27-28*
Mikewa k’arama tayi tabar musu d’akin ganin sai faman uban kuka suke yi, gurin mai unguwa ta koma ta tarar baya rumfar shi sannan ta koma gindin bishiyar kuka ta zauna sai dariya take tana faman surutu, duk wanda ya ganta sai ya tabbatar da cewar ta samu ta6in hankali ta yadda take kwasar dariya ba kakautawa….,
“Ard’o wallahi k’arama ba mutum bace dan mun tabbatar da hakan yau d’innan.” Cewar laminde da taga shigowar Ard’o yayi saurin kallonta da mamaki yana kokarin ajiye sandar korar awakin shi yace.
“Laminde ban shaida zancen kiba, hito kiyi min hila-hila.” Cewar Ard’o yana kallon rumfar su Umma hafsatu, laminde tace, “kur’anin Allah bari jummai tazo kaji karin bayani.”
K’arama ce ta biyo Tanimu yana rarrafe yana dariya har ya karasa kusa da Ard’o cikin 6acin rai ya kalli k’arama tare da gallara mata harara yace, “dan kaniyar ki ban ce kar in kuma ganin ki da yarana ba? Ja’ira kawai fitinanniya marar tushe.”
K’arama ta tura mai baki tana mai kunkuni har jummai ta fito daga makewayi (toilet) duk ruwa jikinta daga gani tana nufin wanka tayi amma duk wani gurin bema san an hallici ruwa ba ta karasa inda suke dama tun a ciki take jiyosu gulma na cinta ta fito tana cewa “Ard’o babu shakka yau mun tabbatar da cewar k’arama mayya ce dan munyi mata hayak’i karshe ma caraffke mukaga tanayi a ciki..”
Zaro idanu yayi cikin tsananin mamaki da tsoro yace “ta6 d’i jam ! abinda ba zai yiwu ba kenan shine take son ta fara takan yaro na kenan…?”
“Ke Hafsatuwalle… ! zo nan.” Ard’o ya fad’a cikin d’aga murya, Umma ta fito bayan ta goge hawanta. “Ke kam wallahi hafsatu kin janyo mana bala’i, ko waye uban k’arama ya had’a jinsi da mayyu dan haka Mu bazamu yadda ba mun baki nan da sati biyu idan baki binciko mana uban k’arama ba wallahin Allah zaki gane kuran ki.”