ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Turo baki tayi tana murguda baki kasa kasa kafin ta zagayesu ta wuce ba tare da tace komae ba !Har sae da ta kusa fita bakin kofar gidan sannan ta juyo tana kallon su tace “Allah ya wa’e (watse)maki albarka Julai……”Ta fice gidan da gudun tsiya ……
Zulai ta d’aga kafa zata bita jummai ta riketa tana fadin “Barta inna Zulai! ki kyaleta ai anan zata kwana ko?da k’warank’watsa tunda har ta zageki yau bara tayi bacci lafiya ba……” Gantsarewa tayi jin an kamar an soka mata allura a baya takai hannu ta sosa ,tana gama sosawa taji wani gurin ya dauki k’aik’ayi sosawa ta kuma yi tare da daukar tabaryarta zata wuce !Cak ta tsaya tare da cire rigarta tana fadin “Laminde taimakan dan sosan bayana kinga ya karad’e da k’aik’ayi ……”
Tabe baki Laminde tayi tana fad’in “Ke ni bana iya tab’a wannan hegen bayan naki da kike wata baki sa mashi ruwa ba ……”
Ta bude baki zatayi bala’i taji kamar ana kara mata azaba a bayanta ……jikin bango ta matsa ta ci gaba da goga bayanta da karfi amma kamar ana karasa !Abu kamar wasa sae ga Jummai na birgima tsakar gida tana ihun k’aik’ai ……Ganin da gaske take yasa matan gidan fara taimaka mata ana sosa mata da cokulla tare da yan jik’e jik’e da aka yi ta d’ura mata ……Kusan awa biyu sannan azabar ta fara ragewa suka kamata suka shigar da ita daki ……
Umma kam tana di’bar icce bata san wainar da ake toyawa ba sae da ta dawo sannan ta iske K’arama ta haye ruwan cikin wani yaro dan gidan Fulani tana jibga tare da ihu kamar ita yake duka ……Yara kuwa sun zagayesu sae dariya suke !Da kyar ta samu ta janye K’aramar daga jikinshi tana ihu ta shigar da ita cikin Bukkar su sannan ta ce “Me ya had’a ki dashi K’arama ?
Dago kai tayi tana kallon Umman da rinannun idanunta tace “Ce man yayi Shegiya, meye Shegiya Umma?
Shiru ta mata tana kallon idanunta sannan ta mike a sanyaye ta janyo wata kwaryar fura ta bude ta fara bata ……Bata damu ba ta fara sha tana lashe baki kafin ta bude baki tace “Ummana wa ya baki kanya da kika fita?
Da sauri ta kalleta tana fadin “Ba wanda ya bani kanya K’arama”
Tabe baki tayi tana kallon cikinta sannan tace “Kuma na ganta a cikinki yanzu ……?
Da sauri ta buge mata baki tare da sakin kuka a hankali tana fadin “Ban hanaki Fadar haka ba K’arama? so kike mutane su tsane mu bayan azabar da muke ciki yanzu?Na shiga uku ni Hafsatu wace irin d’iyace haka Allah ya bani ?Ya Allah na roke ka bayyana ABUNDA KE B’OYE a tare da wannan d’iyar ko ma huta da azabar rayuwa……”
Dafe Bak’inta tayi tana hararanta kasa kasa tare da fad’in “Ni kika daka Umma?
Bata kalleta ba ta cigaba da kukanta a hankali tare da daga hannunta sama tana addu’a sannan ta juyo tana kallon K’arama da har lokacin ita take kallo ……
Tsaki K’aramar ta saki a hankali tana hararan Uwar tata sannan tace “Dallah ni Bari kallona!Ina Ruwana dake ni ……”Ta karashe maganar tana watsa mata harara tare da jujjuya baki……
Wani Sabon kuka ya k’wacewa Hafsuwalle najin abunda K’aramar take fada ta saka hannu tare da kifa mata mari tana fad’in “Ni kikewa Tsawa K’arama?
Fashewa tayi da kuka ta mik’e tana tana kallon Umman tata lokaci guda ta saka hannu tare da duma mata K’ulli ta bar bukkar da gudun tsiya tana fad’in “Ai dai na rama “
“Innalillahi wa’inna ilaihir raju’un “Hafsuwalle ke fada tare da dafe inda K’aramar ta daketa tana fitar da kuka gwanin ban tausayi ……
【】
Ma’aruf ko da ya koma gida ya fadawa Madre abunda ya faru ” Wae wata aljanar yarinya ta mashi fitsari a jiki har yanzu gurin bai bar wari ba ji yake dama ana cire k’afa da yau yaje an cire tashi……”
Dariya ta fara mashi don sam bata ji Haushin Yarinyar ba !Tana sane da yarda Ma’aruf ko daukar yara bayayi don kar su mashi fitsari……
Kallonta yake kamar ya fasa mata kuka sannan ya kalli sumayya da ta shigo daga ita sae Three quater da blouse tana tambayar Madre abunda take wa dariya ……
Aiko Madre din na fada mata ta hau dariya tare da rashewa saman rug din tana nunashi ……
Kallon Madre yayi sannan ya kalli Sumayyar yana fadin “Bansan yaushe raini ya shiga tsakaninmu ba Sumayya”
Nunoshi tayi da hannu tana kokarin danne dariyarta tare da fadin “Yaya Ma’aruf ana plastic surgery fa!
Cikin tsawa yace “Wallahi ko ki bar nan gurin ko na maki shegen duka “
Sanin zaya iya ne ya sata mikewa tana fadin “Allah ya baka hakuri” ta koma daki da gudu tana dariyarta ……
Kallon Madre yayi yana fadin “Kin gani ko Madre wallahi sae na duki waccan yarinyar yau “
Gintsewa tayi tana fadin “Allah ya baka hakuri Auta nima na daina”
Shiru yayi ba tare da yace komae ba !Itama Madre din shiru tayi tana kallon Autan nata ganin ya lumshe idanu sannan ta shafo kanshi tana fadin “Sorry kaji ko Autana kaine da abun dariya wae aljana ta maka fitsari a jiki ……”
Shiru ya mata tare da kwantar da kanshi saman kafadarta ya lumshe ido ……
Sallamar yayarshi Maryam da yaranta biyu Afra da Ihsan ya sashi bude ido tare da sakin karamin tsaki ya na shirin mikewa ……
Ihsan ta kwace hannunta daga na mamanta rugu ta hayeshi tana fadin “Oyoyo Uncle “
Bata fuska yayi yana kallonta yace “Headache” a takaice
Maryam kam gurin Madre ta nufa ta zauna yayin da Afrah ta rabe jikin kujera tare da sakin kuka da karfi ……
Su duka suka kalleta kafin Madre tace “Zonan Afrah ya akai?
Ma’aruf ta kalla sannan tace “Ba Uncle ke harara ta ba tunda muka shigo……”
Hararan ya sake mata yana fadin “Zan bata maki rai Afrah yaushe na harareki……”
Da gudu ta karasa jikinshi tana fadin “Uncle Baka Sona kullun nazo gidan nan sae ka harare ni dan Allah ka daina ina sonka kaji Uncle ……”
Jikinshi yayi sanyi don ya tabbata da ya harareta !janyo ta jikinshi yayi yana fadin “Is okey kinji ko Afrah ……Ihsan ya dai?
Madre kam dariya tayi tana kallon Maryam da ke ta faman korafin wae Auta ya bar Madre da Kumba a jiki ……
*HAJJA[truncated by WhatsApp]
????? *ABUNDA KE BOY’E……*
《Almost True Life Story》
????????
????
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????
SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
ASSALAMU ALAIKUM, masoya masu bibiyar ABUNDA KE B’OYE…! hak’ika muna ganin sakwannin ku ta yadda baki bazai iya lissafoku ba, sai dai muce kusani Hajjafeedohm na ganin saqwan kuma suna jin dad’i, fatan Allah ya bar kauna da soyayya, Mu samman ‘yan grps na HASKE WRITER’S FANS 1-2 hak’ik’a kud’in masoya na mun gode #Hajjafeedohm LYSM????
Page *31-32*
*F*uska a d'aure ya kalleta yana fad'in "Tunda gaki sae ki yanke mata……"
Harara ta sakar mashi tana fad’in “Ni kake fad’awa magana Auta?Yaushe na fara wasa da kai ban sani ba……?”
Murmushi yayi mai sauti sannan yace ” Allah ya baki hakuri Sister ……”
Itama murmushin tayi tace “Madre yaushe mara kunyar Autanki ya sauka……?
Shiru Madre d’in tayi tana kallonsu cike da kauna sannan tace ” Bai je gidanki ba ranar friday?
Da Sauri ya kalli Maryam d’in yana langwabe kai tare da kanne mata ido d’aya ,Yar dariya ta saki ta juyar da kai tana kallon Madre sannan tace “Ihsan Uncle yazo ranar Friday……?
Waro Ido yarinyar tayi tana girgiza kai alamu a’a tare da bud’e baki ……
“Ma’aruf……”Madre ta fad’a tana mashi kallon tuhuma
“Madre ba na fad’a maki motar ne ya samu matsala kafin na karasa gidanta……”ya fad”a yana kokarin guduwa daga falon ……
Jefa mashi pillow tayi tana girgiza kai cike da takaicin halinshi sannan ta juyo tana fad’in “Sae da nace yaje gidanki ranar Friday ashe baije ba?”