ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ban san wane iri hali Gare shi ba Madre!Ina Sumayya take ne……?”
“Tana ciki yanzu Ma’aruf ya koreta……” Madre ta fada tana kallon dakin Sumayya……
Dariya Maryam ta saki tana fadin “Madre anya ba yar gida za’ayi ba?don d’iyarki na son Autanki”
Dariya Madre d’in tayi don ita kanta ta lura da take taken Sumayyar sannan suka shiga ba da firansu har Abbansu ya dawo suka gaisa……su Afrah da Ihsan kam kamar suna jira suka bishi part dinshi suka cika shi da shegen surutu don ma yana da son yara sossae……
《》《》《》
Har Dare ya take Hafsuwalle bata ga K’arama ta dawo ba sossae hankalinta ya tashi ta mike ta nufi inda take zama amma ko alamunta bata ji ba……
Bayan gida ta leka amma wayam babu K’arama babu dalilinta a sanyaye ta dawo tana tunanin ko tana d’akin Lauratu ne !Ta dad’e tsaye tsakar gida tana sauraren ko zata ji motsinta amma shiru, Zulai ta fito rike da buta a hannu ta kalleta a wulakance ta watsar tana fad’in “Wane munafunci ake shiryawa anan kuma Hafsuwalle?ko jarabar ce ta tashi ake neman namiji!
Shiru Hafsuwalle tayi sannan ta rab’e ta koma cikin Bukkarsu yayin da hankalinta ya k’ark’ata K’arama na dak’in Lauratu acan zata k’wana !Gabanta ya fad’i da ta tuna indae Mutanen gidan suka tabbatar da K’arama ta k’wana d’akin Lauratu to zasu sha wulakanci !Tunda a k’a’idar garin Amarya bata fitowa sae tayi sati d’aya haka babu wanda ke shigar mata dak’i har sae ta fara harkokin tsakar gida……
Kwanciya tayi tana addu’ar Allah yasa K’aramar ta fito ba tare da ta k’wana ba !A haka bacci b’arawo ya kwasheta ……
K’arama kuwa tunda ta ma Ummanta k’ulli a baya ta fice daga gidan !K’auyensu Malan Lado ta nufa da yake yanzu ta san hanya sarai bata buk’atar rakiyar wani ……
Ita Kad’ae ta yanki daji har ta isa garin sannan ta zagaye ta bayan gida ta shiga Bukkar Baffanta ……
Kamar Kullum a kwance ta iskeshi idonshi na kallon sama d’akin sai doyi yake !Bata damu da warin d’akin ba tunda ba sani tayi ba ta rab’a ta tsallakeshi ta bude furar da Maitafasa ta kawo mashi ta fara sha !Tsaf ta shanyeta saboda yunwar da ta k’waso sannan ta kalli Lado tana fadin “Bara na karo wata sae na baka ko Baffa……?
Ta mike da sauri ta bar d’akin !Lumshe ido yayi a ranshi yana fad’in ” Karki Fita kin ji d’iyata!bana son wani abu ya sameki saboda ke kad’ae nake gani na samu sauki a rayuwata”Hawaye suka gangaro mashi ganin babu mai jin maganarshi ga K’aramar ta fice da gudu kuma yana jiyo Maganar Maitafasa da Kundum……
Tana Fita ta iske Kundum na ma Maitafasa kitson Zanen Hannu Mai tafasar ta zage sae bala’i take wae Kundum ta matse ta a cinya ta sakar mata tusa ……
Bahaggon salatin da Kundum ta saki shi yasa Maitafasa zabura ta mike tana fad’in ” Amma Kundum anyi lalatarta!ina Macijin da kikewa wannan salatin na rafke shege tunda ke mata kika rako duniya”
Juyawar da zatayi suka hada ido da K’arama dake tsaye tana dage gira tare da miko kwaryar fura……
“Allah ka yafe man na kashe shegiyar nan kowa ya huta”Ta yayi tabaryar dake kusa da ita ta nufi K’arama zata doke……
Ji kake Tim Maitafasa cikin makeken ruwan k’watar dake baje tsakar gidansu……
Wata Dariya K’arama ta saki tare da tab’a hannu har da tsalle tana nuna Maitafasar dake kokarin tashi……
“Amma wanga diya anyi hegeyi yanzu Maitafasar kikewa dariya don ta fad’a kwata?cewar Kundum tana kokarin gimtse tata dariyar muguntar
“To bakar munafuka bud’e baki kiyi taki dariyar mana !Da kwarankwatsa na dade da sanin ke kundum algunguma ce……”Maitafasa ta fada tana kokarin mikewa amma kamar wasa taji cinyarta ta rike yayin da azaba ta fara mamaye cinyar……
Jehowa K’aramar Tabarya tayi tana fad’in “Wallahi kika bari na tashi yau sae anyi sallar gawarki a garin nan……Sae na maki karyawar rashin mutunci “
Dariya Kundum ta saki tana watsa hannu baya tace “A hayye su Maitafasa a cikin fitsarin shanu ……Yo ba k’ara inyi dariyata ba tunda abun naki ba mutunci “
Ihu Maitafasa ta saki tare da rike cinyarta tana fad’in “Kundum taimaka kamar cinyar zata cire nake ji……”
“Yo ta cire mana !Mai ya shafi Kundum bakar Munafuka……!Cewar kundum tare da tsallake Maitafasa ta shige makewayi babu ko buta……
K’arama kuwa d’akin Maitafasa ta fad’a tana tsalle harda tab’a hannu ta dauko katuwar kwaryar da ta gani cike da fura ta koma d’akin da Lado yake ta fara bashi ……
Shi kanshi Ladon Yana mamakin yarinyar yarda take iya mashi komae ba tare da ta tambaya ba wani sa’in har tsoro take bashi saboda ko kad’an babu wanda zaice K’arama na iya bawa wani ko da abinci bare yarda take janye shinfidarshi ta canza mashi wata ta kuma gangaroshi sannan ta wurga kayan da ya bata tsakar gida ……Sae dae Maitafasa ta dauka ta wanke tana bala’in duk lokacin da ta kama mai canza mashi shinfida birni za’a rabasu……
Wasa wasa maitafasa ta kasa tashi har Sae da Kundum ta tausaya mata ta kira makwabta aka kamata aka kaita d’akinta sannan ta lek’a ta kira mata wata tsohuwa dake d’auri tazo ta murji kafar ba tare da tasan menene ciwon ba ta tafi ……Ana gama murzar kafar wahalallan bacci ya kwasheta……
K’arama kam batayi tunanin komawa k’auyensu ba ta rab’a gefenshi ta kwanta itama anan bacci ya d’auketa yayin da Malan Lado ya kura mata ido yana jin soyayyarta tare da tausayinta na ratsashi ji yake ina ma zaya iya daya fadawa duniya su bar sheganta mashi diya domin halalinshi ce……
【】
Ma’aruf kam Kafin Ya koma Madre tawa Abbanshi maganar tana son a hadashi Aure da Sumayya !Da fatan alkhairi Abban ya bisu don ya tabbata barata tab’a zab’awa Autansu mace ta banza ba !kuma yana da yak’inin Sumayya ta samo tarbiyya mai kyau tunda Hannunsu ta tashi ……
Shi da kanshi yawa Ma’aruf din maganar ya bashi Sumayya !Wata irin faduwar gaba ya samu a ranar don ko kad’an bai tab’a tunanin zai auri Sumayyar ba beside ma bata cikin matan da yake tunanin aure !Sai dae ko kad’an baya iya gardama da iyayenshi ……Don haka kai tsaye ya amsa a baki sae dae a zuciyarshi kamar ta kone yake ji !Bai nuna ma kowa bai ji dad’in zab’in da iyayen nashi suka mashi ba sae dae ya barwa kanshi!
Ko kwana biyu bai karayi ba ya tattara kayanshi ya koma india tun da lokacin saura 3 month ya dawo baki d’aya……kuma a yarda iyayen nashi suka fada da ya dawo za’ayi bikin nasu ……!
HAJJA CE????
&
FEEDOHM????
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》
????????
????
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????
SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
_????????????You are the best gift our parents could ever give us. You are the one who made our childhood unforgettable. Wish you a very sweet and warm birthday. Our aunty, our support, we love you so much sister *UMMI AISHA*????.????????_
Assalamu alaikum sisters, kuyi hakuri yau kunji shiru, sistern FEEDOHM ce Allah yayi mata rasuwa, Allah yaji kanta da rahama yasa karshen wahalar kenan, idan tamu tazo yasa Mu cika da imani Amin????????
Page *33-34*
Sumayya kam Sai da ya tafi da kwana biyu sannan Madre ta fad’a mata !kamar zata mata sujjada dan murna babu kunya ta dinga wangale baki harda su rawa ta zama Mrs Ma’aruf……Madre kam da kallon mamaki ta bita dashi tana jin-jina rashin kunya irin na sumayya !!
A ranar ta fad’awa duk wasu friends nata har wad’and’a ta manta dasu cewa ta zama Mrs Ma’aruf yayin da ta canza suna a dukkan account d’inta na social media zuwa Mrs Ma’aruf……
Saboda bala’in zakewa ranar tama wata friend d’inta Beeba waya wai ta kawo mata mai magungunan mata zata saya ta fara amfani dasu tun yanzu ……