ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

"Ikon Allah tun yanzu Sumayya?abunda Beeba ta fad'a kenan tana rike baki kamar tana gaban ta
“Kinga laifina ma kenan Beeba ko?Kawae ki samo mun masu kyau ki kawo mun yanzu, bana son nakai gobe ban fara amfani dasu ba……”
“Allah ya kyauta.” Abunda Beeba ta fad’a kenan ta yanke wayarta kit!……
Tsaki Sumayya ta saki ta matsa gaban madubi ta fesa turare sannan ta d’auki wayar ta kira Ma’aruf, amma har ta kare ringing bai d’auka ba!ba kuma don bai ga kiran nata ba a’a hasalima wayar na bisa kirjin shi yayin da yake kwance rigingine yana kallon sama……
Kusan sau uku tana kiran shi bai d’auka ba sannan ta zauna ta rubuta gutun message ta tura mashi “Please pick my call i wanna hear you rancid voice despites the fact you’re the light that brighter my heart……It’s me Mrs Ma’aruf.”
Yana jin shigowar text d’in amma bai duba ba har sae da ta sake kiranshi sau biyu sannan ya d’auka ba tare da yayi magana ba……
Cikin Zumud’i tace “Hello……”
“Yaya Ma’aruf……”
“Kana jina……?”
“Sumayya… !” ya fad’a a takaice……
Cikin shagwab’a tace “Shine kuma kayi shiru ka kyale ni……”
“Bana son surutu me kike son fad’a……?ya fad’a a hankali idonshi a rufe.
“Allah ya baka hakuri Yaya Ma’aruf dama ina so ne na tambayeka zan d’an fita idan beeba tazo na rakata inda take aje motarta tunda naga yanzu na zama matarka komae kai ya kamata na nemi izini gurinka……”
Dariya da takaicinta suka dirar mashi lokaci guda har bai san lokacin da yace “Uban wa yace kin zama matata ki kirani ki tambayeni idan zaki fita Sumayya?ya karashe cikin sanyin muryarshi amma a nashi tunanin fad’a yake ……
“Madre tace an baka ni……kuma laifine don na tambayi mijina zan fita?ta fad’a a shagwabe……
Yanke wayar yayi tare da bin ta da harara !Shi kam an hadashi da bala’i wallahi !abunda ya fad’a kenan a fili tare da jan karamin tsaki……
Ita kam Sumayya bata ji komae ba illa tsallen da tayi ta fad’a saman gado tana juyi ita kadae……
【】
“Uban wa na kama yanzu ……”Cewar Matar Fulani tare da cakumo wuyan K’arama da ke zaune gurin kuka tayi bud’u bud’u da ita kamar ba gobe……
Ido ta k’walalo mata tana kokarin aje k’aton dutsen dake goye a bayanta tana fadin “Ni kika kama!
Duka ta sakar mata akai tana fad’in “Uban me ya hadaki da Jabiru……?
Turo baki tayi tana dafe inda ta bugeta tace “Ba shi bane ya ce man shegiya……”
Kara dukanta tayi tana fadin “Karya ya maki dan ubanki ba shegiyar bace !uban waye bai san amanar Malan lado aka ci ba aka haifeki” ta karashe maganar tare da hankad’ata ta fad’a ta zauna kasa tana harba kafafuwa ……
Juyawa Matar Fulani tayi tana zage zagenta !K’arama kam dutsen dake bayanta ta dauka yayin da ta saita duwawun Matar fulani ta jefa mata ta watsa da gudunta ta bar gurin……
Dafe gurin tayi ta juyo amma babu K’arama babu dalilinta wani uban zafi ta ji ya soketa kamar lokacin aka jefa mata shi ,ta d’aga kai ta kalli kukar da ke kusa da ita tana luliya gurin ……
Mace ta hango sama tana washe mata baki hakora a waje kamar na shanu……
Kwaryar nononta ta saki tare da dafe kai ta baza da gudu ta koma gida tana dafe da inda K’arama ta jefeta……
Ranar da Lauratu ta fara fitowa ranar matan gidan a waje suka shinfida buhu suka zauna duk da azabar ranar da ake ……Jira kawae suke Lauratun ta nufi Bukkar da Hafsuwalle take su fadawa Ard’o ya mata rashin mutunci Tunda yanzu ta zama karkashin Garka ta fita daga hannun Hafsuwallen……
Tana lura dasu don haka ko bukkar bata kalla ba har Sae da K’arama tazo ta raba kusa da ita ta zauna tana washe mata tace “Yaya Laulatu har an gama dafa ki a d’akin?
Kallon mutanen gidan tayi taga kowa ya zuba ido yaji ko zata mata magana !hawaye suka taru a idonta ita dai bata jin zata iya k’yale K’arama ko da za’a fidda mata rai ne ……
Goge hawayen tayi ba tare da tace komae ba ta janyo K’arama jikinta ta rungumi ita kanta ta san tayi rashin kanwarta……
“Shikenan Lauratu yanzu Ard’o bai isa ya saka doka ki bita ba?cewar matan gidan kamar hadin baki ……
Kuka ya kwace mata tace “Wallahi bazan iya rayuwa babu K’arama ba a kusa dani dan Allah ku barni da ita”
“Idan Ard’on yazo sae ki fada mashi haka……”Cewar Laminde tare da nade buhunta don dama abunda take jira kenan……
Hafsuwalle ta leko tare da kiran K’arama don duk abunda suke tana saurarensu ……Cikin Sa’a K’arama taje ta sakata Bukka da wayau da dubara ta zaunar da ita tana mata tatsuniya ……
Inno kam girgiza kai tayi a hankali don har ga Allah abunda akewa su Hafsuwalle ya fara isarta kawae tana daurewa ne don babu uwar da zata ce bata son d’iyarta a duniyar nan ……Ko da Ard’o ya dawo suka fada mashi banza ya masu saboda yana jin Kunyar Lauratun yanzu tuda ta rigaya ta zama surukarshi !
Tun daga lokacin Hafsuwalle ta daina barin K’arama na yawan shishshigewa Lauratun saboda matsalar cikin gidan ……Tun tana mata kuka idan ta sakata bukka har ta daina saboda ko’ina Umman zataje sae ta ja hannunta su tafi ……
K’arama kam ganin Umman tata na lallabata yasa ta itama take jin maganarta sossae amma hakan baya hana idan ta daketa ta mike ta rama ta gudu ga rashi kunya duk lokacin da abun ya kad’o mata ……
Mutanen gidan ma bata ragawa duk wanda ya daketa sae ta rama idan kuma bata samu ramawa ba to kai kuma ranar baka bacci ……zaka kwana kana ihu ana baka tsoro! hakan bai saka sun daina takura masu ba don basuyi tunanin saboda ita ake basu tsoro ba ……
Maganar Idan kaci abu ka fito ta kalli cikinka tace ga abunda kaci har lokacin bata daina ba sae dae ta kanci dan banzan duka gurin tsofaffin garin wata rana……
Two month later……
Tana bayan umman ta sun debo ruwa sae uban surutu take kamar an bude fanfo ……Aje tulun tayi ta juya baya da gudu tare da leka Zauren wani gida da aka saki buhun kofar Sannan ta matso kusa da Ummanta tana tab’a hannu had’i da tab’e baki ……
“Umma jiya Habi Surukar Fulani tace man wae yar iska……”ta a fad’a idonta na kan zauren
A Sanyaye Umman ta kalleta tana girgiza kai saboda ta san wani abun take shirin aikatawa……
Hade hannu tayi sannan ta dauki tulun ruwanta tayi gaba abunta tana murmushi……Tana ajewa kafin Umma ta shiga d’aki ta aje Zanin lullubinta ta fito ta shige kewaye ta dire ta katanga ta bar gidan……
Gidan Fulani ta isa ta tarad da Habi da Matar Fulani suna sussukar masara ……
Da yar ficiciyar muryata tayi sallama ta mak’ale zauren gidan ba tare da ta shiga ba ……
“Wacece nan ta labe…?cewar Habi
“K’arama yar iska ce ……”ta fada tare da yin tsalle daya ta fado cikin gidan ……
A Harzuke matar fulani ta matso tana fadin “Ke ce dama ?Uban me ya kawoki gidannan ?Wae Habi bance kar wannan shegiyar yarinyar ta kuma shigowa gidan nan ba?
Kyafta idanu ta farayi tana fadin “Babban d’an iska na gani a zauren malan bashe shine nazo na fad’awa matar d’an iska da surukar d’an iska……”ta karashe maganar tare da rike kugu tana girgiza kamar wata budurwa……
Kamar ta saka masu gas haka suka hayyako mata ta kwasa da gudu ta bar lungun……
HAJJA CE????
&
FEEDOHM????
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》
????????
????
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM????
&
_K.A.S Precious HAJJA CE????
SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyar mu
Page *35-36*
*B*ayan Ma'aruf ya kammala karatun shi ya dawo Nigeria Aisha budurwar shi dake tsananin son shi da kyar ya samu ta rabu da shi lokacin har kuka tayi da yace mata anyi mishi baiko da wata tayi kuka sosai dan ba karamin so take mai ba shima lokacin yaji tsananin tausayin ta amma ba yadda zai yi dole yasa ya gaya mata gaskiyar lamari.
Zaune yake a parlorn Madre yana karanta wata jarida Sumayya ta fito, tana ganin shi ta koma room d’inta tare da kara turare a jikinta kasan cewar tasan yana son kamshi. Parlorn ta koma ta zauna bayan ta gaidashi ya amsa tamkar baya so, kafin ya d’ago ya kalleta suka had’a idanu guri d’aya yace.