ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

“What are you looking for?” Ya fad’a bayan ya d’aure fuskarshi
Sumayya tayi murmushi tare da gyara zama ganin yana son magana tace “Yaya Ma’aruf naji ka shiru baka min zancen yadda bikin Mu zai kasan ce ba kayi shiru…”

Jaridar hannun shi ya ajiye tare da kallonta, “Zo nan me kike so na gaya miki…” Da sauri ta mik’e ta k’arasa kusa da shi tana mamakin jin cewar yace ta dawo kusa dashi, shi kuwa tun sanda ta shigo parlorn kamshin turaran ta ya bugar mai hanci ya ji yana son kamshin turaren da ta shafa ……

“Kin gane ko Sumy !, bana bukatar yin wasu bidi’a just kawai a yi lalle ranar d’aurin aure sai ayi walima kawai, albarkar auren muke so ba wani abu ba….”

Turo baki tayi cikin shagwa6a, hannunta na cikin nashi ji yake tamkar ya rungometa amma bazai iya ba gudun kar ya janwowa kanshi fitina, abinku da lafiyayye giredin namiji mai ishashishiyar lafiya. “Haba Yaya Ma’aruf ko dinner ma baza muyi ba, please dan Allah mana sai kace ni da kai ba wayayyu ba…?”

“Mteww… !, yaja tsaki cikin jin haushi a hankali ya zame hannun shi dake cikin nata ya d’auki jaridar shi daya ajiye yace “Ok fine, kije kuyi but ni dai baza ku ganni a wajan ba that’s all…”

“Yaya Ma’aruf Me yasa zaka yi mana haka..?” Sumayya ta fad’a kamar zata yi kuka, Madre ce ta fito hannunta d’auke da memo da biro ta k’arasa parlorn ganin su tare yasa ta saki murmushi tace,

“Yauwa gara da na ganku tare Ma’aruf ina so naji wane color kake so na punitures d’in ka?” Madre ta fad’a bayan ta zauna cikin d’aya daga kujerun.

Cikin rashin son maganar shi ya kalli Madre tare da miskilalliyar fuskar shi yace “Madre bana da wani zabi so choose me any colorful…” Murmushi tayi dan tasan color d’inshi ta koma kan Sumayya dake ta faman cono baki daga gani tana cikin fitina Madre tace…,

“Ya haka kuma Sumayya..? Waya ta6a minke haka da safen nan? Sumayya ta juya tana nuna mata Yaya Ma’aruf da hannu fuskarta a shagwa6e. “Sorry baby kinji rabu dashi zo ki gaya min abinda yayi miki….”

Zama tayi kusa da Madre tace “kinji shi wai baza muyi kowanne event ba, ko zamu yi shi bazai je gurin ba kawae Madre so yake ya zubar man da mutunci gurin friends dina….” Madre ta zaro ido tana kallon Ma’aruf cikin mamakin shi tace “Me ke damunka ne Ma’aruf?Wane irin mutum ne kai ..? To Ba abunda za’a fasa kuma sai kaje komai kaji na gaya maka…”

“Shikenan Madre amma a tunanina albarkar auran ake so, amma tunda kince haka zanje…” Yana fad’a ya bar parlorn kamar ya sake ihu side d’in shi ya wuce ya d’auki laptop d’inshi yana wani research……

{{ }} {{ }} {{ }}

  Karasawa suka yi cikin gwadabniya har cikin d'akin da lado ke kwance, Ma'aruf ya kalli side d'in da wani babban malami yaje wanda suka zo tare yace "bismilah malan kalla..." Malan Kalla ya matsa kusa da lado dake kwance yana binsu da ido, wata jaka ya bud'e gaba d'aya d'akin ya kaure da kamshin almuski da wani farin ruwa mai dukan kai sossae nan da nan Lado ya fara zaro idanuwa yana kokarin yin motsi da 6arin jikin shi d'aya.

Kura mashi Idanu Ma’aruf yayi yana nazartar wani abu daga jikin shi, malan kalla ya fito da garin ganyen magarya da jikakiyar kanwa ya fara watsa wa a gurin da lado ke kwance. Ayatulkursiyu yace su karanta baki d’ayan su mutanan gurin su focal parson, guard, Ma’aruf, mai unguwa da makocin su malan sahabi kowa sai mamul-mamul yake da baki idan ka d’auke malan kalla da Ma’aruf da focal parson sune kawai suke yinta dai-dai, nan da nan ana watsa mai ruwan kanwa da ganyen magarya lado ya fara wani irin kuka kirjin shi na d’agawa, Ma’aruf ya gazgata zargin shi na cewar asiri aka yiwa Lado.

Wata irin murya suka ji gaba d’aya ta kaure cikin d’akin tamkar zata tsaga bango, kallon Lado malan kalla yayi tare da cewa “Wace ce ke..? Me kike yi ajikin bawan Allah kike wahalar dashi tsawon shekaru..?

"Siiiiiiiiii..... *!*, suka ji yana fitowa daga bakin Lado ……Malan kalla ya shafa mai ruwan kanwa sai aljanar ta fara magana a fusace.

“Ku-ku-kun takura mana fa… ! kai.., ta nuna Ma’aruf da yatsan lado tace “ka takurawa rayuwar mu, ka hanamu sukunin da muka dad’e muna yi, ina ruwanka damu da zaka tahu mana da kalla…… !?” Ma’aruf yayi murmushi cikin nuna rashin tsoro duk da bugun da zuciyar shi ke mishi yace.

“Ko” Ya fad’a tare da mai da kallon shi gurin Malan yace “continue Malan daga inda ka tsaya…” Ayoyi malan kalla ya dinga kwararowa aljanar tana ta magana kafin ogan yayi shima cikin zunduma uban zagi dama bamagujene malan kalla yace.

“Ina jin ku me ya faru..?” Ifiritu yayi magana a kausashe yace “turo mu aka yi kuma mun samu gurin zama dan munyi katon gini a jikin shi…” “Waya turoku jikin shi…” Hhhhhhhh…. ! ifiritu yayi wata mahaukaciyar dariya tare da cewa “Babu ruwanka.”

Karatu malan kalla ya cigaba dayi su kuma suna ihu suna cewa yayi hakuri zasu fita kuma zasu fad’a amma yak’i denawa lokacin duk mutanan gurin sun shiga cikin rud’ani sai da ya kusa konasu da ayar Allah sannan ya watsa musu ruwan kanwa yace “toh muna ji waya turo ku?” Ifiritu a wahale tamkar d’an giya yace “Hansai ce matar mai-unguwa ta biyu, ta turo mu saboda yafi kowa amfanin gona har da d’anta badaru hakan yasa ta turo mu muka shige shi karku kona mu muna da yawa muda iyalanmu….”

“Kanbala’i! Aradun Allah bazan yadda wato daman Hansai ce ke son lahanta min lado…?” Cewar Mai-tafasa dake bakin kafa, “tallahi banga me rabani da Hansai ba a garin nan daman tuntuni naga take takenta!daga murya tayi tana fadin ” kundum, buwale, Asibi, baraka, lanto kai duk mutanan garin nan kuzo kuji min Hansai ta cuce ni ita ce ta kwantar da lado…”

Kafin kace me sun cika gidan yaran su da manya, nan mai-tafasa ta kara narka wani bala’in su lanto suna zugata haushi da takaici yasa Ma’aruf ya fito yana kallon su tamkar yayi amai sabida tsamin da ke tashi a jikin su yace, “shut up !, duk da basu gane me yake cewa ba amma sunga yayi tsawa sannan fuskar shi a murtuke yasa suka yi shiru yace su fita daga gidan su basu guri, sim-sim suka fita harda Mai-tafasa sannan yayi tsaki ya koma cikin d’akin malan kalla nata karatun alkur’ani su kuma sun zuba musu idanu, karasawa yayi suka ci gaba tare har kusan tsawan awanni biyar kafin sukayi nasarar kona su baki d’aya.

Waige-waige lado ya fara yi yana kiran Hafsatu, ganin bata fito ba yasa ya kalli mutanan yaga Mai-unguwa yace “Baffa malan ina Hafsatu na..?” Sai ga mai-unguwa na hawayen murna yau yaji muryar lado daya dad’e beji ba. “Tashi mugani..” Ma’aruf ya fad’a yana kallon lado cikin ido, “ba zan iya ba rankashi dad’e…” Lado ya fad’a yana zubar da hawaye Ma’aruf yasa focal parson ya tatta6a shi sai yaga 6arin jikin shi na hago baya aiki nan yayi musu bayani daman hakan zata faru kasan cewar yana da matsalar AFP sannan kwanciyar da ya dad’e guri guda yasa hakan yayi tasiri yanzu haka lado sai dai a samo mai weal chair da keke ya dinga amfani dasu, sun d’an jima kafin suka bar gurin su Ma’aruf suka koma state dan sanar dasu abunda ke akwai…….,FEEDOHM????
&
HAJJA CE????
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》

               ????????
                  ????

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????

SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu

ASSALAMU ALAIKUM FAN’S!, Nagode da sakwannin ta’aziyarku gareni, masu k’ira, PC, text message da masu yi min a grps, Allah ya bar kauna ita kuma Allah yaji k’anta da rahama yasa karshen wahalar ta kenan.????

Masu neman Novel d’in daga farko dan Allah a dinga tambaya a grps wallahi babu abinda yafi tura novel daga farko haushi gashi ba mutum d’aya ke soba, gashi idan ka hana aji haushi, idan baka yi typing bama aji, please dan Allah ku dinga mana afuwa ko masu su suje shafin Wattpad @Hajjac zai samu kafin Feedohm ma na bud’e, ko su bari ayi document sai abasu, thanks.????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button