ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

 Page *37-38*


 *S*ai da ya kammala komai sannan focal person d'in shi ya kai shi can airport ya hau jirgin zuwa kano, tun a hanya yayi waya aka turo mai da drive. Suna dira ya hango parado d'in shi da ya siya a ita aka zo d'aukar shi ya k'arasa yashiga driver yaja, har suka je gida amsa wayoyi yake yi direct ya wuce side d'in Madre kai da ka ganshi kasan a gajiye yake ya zauna kan sofa tare da killar da phone d'in shi a gefe ya rintsa ido.

“Ma’aruf ka dawo ke nan?” Madre ta fad’a tana k’okarin fitowa daga kitchen. Amsawa yayi a wahale har ta k’araso kusa dashi tana kallon shi cike da tausa yawa dan ta hango gajiya sosai a fuskar shi.

“Toh kaje kayi wanka sai na turo Sumayya ta kawo ma abinci, da kaci sai ka kwanta ka huta…” Da sauri ya hau gir-giza kai alamar a’a cikin turo baki tamkar karamin yaro yace, “no Madre please karki turo min ita wallahi ciwon kai zata samin, ko ta tambaye ki na dawo kice mata a’ah kawai.”

Yana kaiwa nan ya mike yayi hanyar fita, yana jiyo Madre na cewa, “a’ah yaro ni kam ban iya karar ku ba, idan ta tambaye ni Zan gaya mata gaskiya.”

Yana shiga ya fad’a kan rog yana sauke numfashi, gaba d’aya abinda ya faru da lado ne yake mai yawo yana mamaki ace wai kishiyar uwar ka ita ce zata illataka sabida wani sakar ci, sai yanzu yake jin haushi da be tsaya yasa an hukunta Hansai ba amma ya bar shi har zuwa lokacin da zai koma garin.

Mtww… ! yaja tsaki tare dayin juyi bayan ya tuno cewar kwanakin bikin shi sun kusa zuwa shi bama wanda ya sanarwa, mtww… ! ya kuma jan wani tsakin tare da mik’ewa tsaye ya shiga bathroom bayan ya rage kayan jikin shi.

Daga shi sai small towel a kugunshi ya fito, tunda ya bud’e bathroom d’in ko’ina na cikin d’akin ya fara fitar da wani daddad’an kamshi me azabtar da zuciya, dressing mirrow ya k’arasa ya d’auki wani k’aramin towel d’in wanda yafi na jikin shi kan-kanta ya fara goge jikin shi dashi, yana gamawa ya fara shafa mayuka masu tsada da kamshi sannan ya wuce dressing room ya fito da sweetshit green color da jeans white color ya sanya yasa takalmi trainer’s kalar green ya feshesu da kala-kalan turaruka masu masifar kamshi ya sanya ear muffs a kunnan shi yana jin suratul tauba a haka ya shiga side d’in Madre.

Zaune ya same ta tana danna laptop gefenta duk takadda ya k’arasa ya zauna a 2seater tare da kallon ta yana turo baki like small boy. “Kaje dining kaci abinci.” Kurum Madre ta ce mai ba tare da tad’ago ta kalle shi ba dan tasan idan ta d’ago me zata gani.

K’in tashi yayi sabida beji abinda take cewa ba sakamakwan ear muffs d’in dake kunnan shi, a hankali ta kalleshi tayi mai alamar ya cire da hannu sannan yayi yadda tace d’in but still bakin shi a zumbure ta ta6e baki tare da cewa,

“Kaje kaci abinci nace ka dawo daga tafiya kak’i bawa ciki hakk’in shi, ko a koshe kake?” Ta tambaye shi tana ture laptop d’in gabanta, Ma’aruf ya gir-giza kai tare da cewa.

“Please Madre muje ki bani…” Kallon shi tayi da mamaki sannan ta mik’e tayi hanyar dining d’in tana cewa, “ni gara ma kayi auran Ma’aruf na ga alamar yanzu tabarar taka neman yin yawa take yi….”

A baya ya bita yaja kujera ya zauna, sakwara da miya ta zuba mai wadda taji nama da stock fish ga uban ogu leave sai kamshi ke faman tashi ta zuba mai lemon kwakwa da ya sha peak milk ya wanke hannu a cikin boul d’in dake gurin ya fara ci kenan sai ga Sumayya ta dawo.

“Oyo-yo Yaya Ma’aruf dama yau zaka dawo?” Cewar Sumayya tana k’arasowa wajan shi da sauri cikin farin ciki da murnar ganin shi da tayi… Banza da ita yayi yana ci gaba da cin abincin shi tamkar be jita ba har ta k’arasa kusa dashi taja kujera a kusa dashi ta zauna.

“Welcome Yaya Ma’aruf…” Ta sake fad’a ya sa ‘yar k’aramar sakwarar da ya gutsuro a cikin bakin shi kafin ya tauna ya had’iye yace “thanks…” Cikin ranta tace “thanks kuma kai da zaka ce min OK ko yauwa sai kace wani thanks sai kace nayi ma kiss…” A fili kuma tayi murmushi tare da kura mai ido, ba k’aramin kyau yayi mata ba, ji take inama zai tsaya da ta rungume shi taji shi a jikinta wannan pink red d’in lips d’in nashi ba abunda zai hanata d’ora nata akai ta lumshe idanu ta bud’e su tar akan nashi….

“Yaya Ma’aruf ina ta maka zancen different event d’in da za’ayi kayi shiru baka ce min komai ba, dan Allah yau karka tashi bamu gama magana ba.” Duk abinda suke yi Madre na jinsu, har mamakin Sumayya take yi irin yadda taji tana zuba surutu kuma duk akan yadda bikin su zai kasan ce ne, shi kuwa gogwan yayi shiru sai faman cin sakwarar shi yake tamkar jariri ake bamawa. Da yaji surutun nata yayi yawa ne yasa shi kallonta da manyan sexy eye d’in shi yace.

“Sumy… !, wai ba kya gajiya da surutu ne…? And ina cin abinci kike son muyi magana da yake haka aka yi teaching d’inki…? Bana son hayaniya kije ku shirya kome zaku yi I don’t have a time to talk akan wannan abun abi..?”

Bata wani ji haushi ba ta d’aga mai kai tare da m’ik’ewa tabar gurin hannunta rik’e da wata leda mai d’auke da magungunan mata da taje Beeba ta rakata suka siyo gidan wata hajiya mai komai da ruwanki. Da kallo ya bita har ta shiga room d’inta ya gir-giza kai tare da wanke hannun shi dan appertained d’in shi nacin ya gishe.

Sumayya na shiga d’aki ta zube kayan akan gado sun fi kala ashirin ko wanne da amfanin shi ta d’auki wata katuwar jarka ta fara kwankwad’ar abunda ke ciki ko rashin dad’in ba taji ba har tasha rabi sannan ta d’auki wasu ta fara cusawa a ppt d’inta da Cotton wood…. Lol amarya.

FEEDOHM????
&
HAJJA CE????
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》

               ????????
                  ????

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????

SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu

 Page *39-40*

FEW MONTH LITTER

*G*idan cike yake da 'yan uwa da abokan arziki na both amarya da ango, Madre bak'i yaki rufuwa ana aurar da auta duk inda ka ganta bakin ta da murmushi ta k'awayanta na gurin aikin su sai zolayarta suke sai dai tayi dariya kawai ta wuce dan murnar da take ciki tafi komai yawa a zuciyar ta.

Tana fitowa compound ta hango Ma’aruf yaji uwar kwalliya kai da ka ganshi kasan cewar shine ango, abokan shi guda uku suna biye dashi suma duk sunsha ado Madre ta sakar mai murmushi tare da komawa cikin d’aki dan kar mutane suga zak’ewarta a tafi ana yi da ita abaki. Waje suka fita inda maza suke manyan mutane da kananun ma’aikata kai da gaka tarun kasan ba k’aramin people ya tara ba, Ma’aruf yayi mamaki dan shi yasan ba wani invitation card ya raba ba amma kakaf abokanshi na k’asashen waje dana gida Nigeria d’ai-d’ai kune babu “Toh waya sanar musu..? Ya tambayi zuciyar shi amma ba amsa “ko Naseer ne yayi mai wannan aika-aikar…?” Ya juya yana kallon Naseer dake ta faman gaisawa da mutane “amma kuwa idan shine sai ya yi mai rashin M.” Ya fad’a a cikin zuciyar shi sannan ya fara smiling yana gaisawa da mutane.

Kunnuwan shine suka jiyo mishi ana cewa an d’aura auran Muhammadu Ma’aruf da Sumayya akan sadaki dubu d’ari biyu da mukullin mota…. Daram-Dam… ! k’irjin shi ya buga cikin ranshi yace “Dubu d’ari biyu sadaki…? Waye yace musu zai bada har wannan kud’in shi da yake son albarka aure, uwa uba harda car key shi da beyi niyar siyawa Sumayya mota yanzu ba sai yaga irin takunta..”

Saleem ne ya ta6o kafad’ar shi ganin tamkar be san an shafa fatiha ba yayi figigit yana kallon shi kafin shima yakai tafin hannunshi masu tsananin taushi ya shafa fuskar shi “kai Ma’aruf ka saki jiki mutane sai kallonka suke yi sai suyi tunanin baka son auran please dan Allah.”

Fitar da komai yayi daga ranshi aka fara gudanar da taro cikin kwanciyar hankali, sai da abokan shi suka fara tafiya sannan ya samu damar shiga cikin side d’in shi su da su Naseer sai tsiya suke mai yak’i kula su. Yana zuwa ya cire babbar rigar dama duk ta isheshi jiyake tamkar an d’aura mai katon dotse yayi saurin shiga bathroom ya fad’a cikin jarcuxe yana sauke ajiyar zuciya “ikon Allah…” Ya furta cikin ranshi “wai yau shi ake d’aurawa aure..? Ikon Allah shi be ta6a kawowa zai yi aure kusa haka ba sai gashi lallai kar mutum yaja da ikon Allah, shine mai komai sannan mai yin komai. Ya dad’e a cikin ruwan kafin ya fito ya sanya bathrobe ya wuce dressing room, nan d’in ma sai da ya dad’e sannan ya fito cikin shirin shi. Shadda ce yasa ash color tazarce tayi mai bala’in kyau ya fita parlor su Yaseer, Naseer da Sameer sai tsiya suke mai yana musu murmushi. Yana zama su Hidaya suka shigo da warmers na abinci suka dire musu suna kallon su, “uncle Ma’ar gashi nan inji Madre tace za’a kawo sinasir yanzu…”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button