ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani mugun kallo ya bisu dashi jin sunan da suke kiranshi a gaban friends d’in shi “Tasleema bana ce kar wanda ya sake kirana da wannan stupid name d’in ba..?” Ya fad’a ranshi a had’a suka fara kalon juna Hidaya tace “sorry uncle Ma’ar… Sai tayi saurin rufe baki jin ta sake fad’a ya kallesu tare da nuna musu kofar da suka shigo yace “get out… ! marasa kunya kawai.” Fita suka yi suna dariya Inteesar tace “ah su uncle angon Yaya Sumy gaskiya sun yi perfect wallahi, matsalar d’aya da Yaya Sumy zata sha fama miskilanci…” Suka kuma sakin dariya sannan suka shiga cikin d’aki gurin amarya.
Zaune suka same ta ana mata makeup duk kawayan ta suma suna tayin nasu, kallonta suka yi inteesar tace “gaskiya Yaya Sumayya kin yi dace da miji, uncle Ma’aruf ya had’u ta ko ina kinga kyawun da yayi kuwa yanzu…? Hidaya ta kar6e zancen “wallahi uncle handsome guy ne ya had’a komai a rayuwa.” Tasleema tace “kyau, ilimi, nasaba, kud’i, daraja, biyayya, tausayi, in fact shi have everything what I mean komai da komai…”
Wani kayataccen murmushi ta saki tare da sauke ajiyar zuciya lokacin an gama makeup ta mike tasa wata doguwar riga bridal tace “intee yana ina yanzun…?” Inteesar tace “yana side d’inshi tare da friends nasha..” Sumayya ta kalli Beeba “please Beeba d’akko min wannan turaran.” Beeba ta kalleta da mamaki tace “kin san dai ba yanzu zaki amfani dashi ba sai an kaiki gidan miji uwar zumud’i kawai..”
Ganin Beeba ta hanata yasa tayi tsaki, ita yanzu so take kawai ta ganta a gurin shi sabida ta tsuma ga wanda Madre tayi mata ga wad’an da tasha a 6oye hakan yasa duk take jinta wani iri tana jin tamkar takai kanta sai dai yawan mutane yasa ta kasa zuwa. 8:00pm aka fara tafiya dinner wanda daga an gama an dawo za’akai amarya.
“Ma’aruf kaje ka shiga mota ana jiran ka kaji ko….?” Madre da ta shigo d’akin shi ta fad’a dan gaba d’aya event din da aka yi sai tazo ta sashi yake fita. Yanzu ma be so zuwa ba shi yasa tazo ta mai magana, yana jin haushi haka ya shirya cikin wani shegen yadi milk color da ratsin blue ajiki, hula yasa zanna blue da shoe cover yayi kyau sannan su Sameer suka kai shi motar da aka tanadar musu shi da anarya.
A ciki ya sameta gaba d’aya kamshin turare dana khumra sun turare motar, Ma’aruf kenan, yana matukar son kanshi hakan yasa yayi tasiri a zuciyar shi ya zauna kusa da ita tare da matsawa jikinta ya riko hannunta, jikin ta ya fara rawa nan da nan taso rud’ewa kamar ya gane ya janyo ta jikin shi yana kara shakar kamshinta a haka aka ja mota……
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》
????????
????
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????
SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
Page *41-42*
*D*inner akayi ta kece raini kowa ya ci ya sha daga abunda aka tanadar yayin da Madre tayi barin kudi kamar ita ke bugasu……Sae kusan 10 Na dare sannan aka tashi gidan Madre din aka koma kafin zuwa Safe ayi walima Ango ya tafi da amaryarshi don ba'a bukatar yan kai amarya ……
Tunda Asuba aka fara shirya shiryen walimar AA Event & Design dake kabo crescent off Ahmadu bello way Garki 900242 Abuja ……Madre ta dauko sukayi decorating harabar gidan ……
Sun kawata gurim sossae ta yarda ko makiyi bara ya kushe ba ……Karfe 4:10pm aka fito da Amarya Sumayya sanye da Arfo Lace white da ratsin Baki a jiki……tayi masifar kyau sai sheki take tana sargale da hannu Ma’aruf shima kanshi abun kallone Sae dae kallo daya zaka mashi ka tabbatar da murmushin Yaken dake kwance a saman kyakykyawar fuskarshi sab’anin Sumayya dake murmushin farinciki ……
Sae da suka fara zuwa suka gayyar da dagin Abbah sannan suka koma ga dangin Madre suka saka masu albarka sannan suka koma inda aka tanadar masu kujerunsu suka zauna ……Yayin da sauti mai taushi ya karad’e gurin……
Wajen magrib sannan jama’a suka fara watsewa yayin da Madre taki yarda tawa Ma’aruf nasiha ta koma part din Ma’aruf tayi kwanciyarta sae dae Abba da Maryam kadae suka masu Sannan suka ce ya dauki matarshi su tafi……
Ko irin kukan da ake Sumayya bata yi illa murmushin da take tana yake hakora duk da irin sharrin da abokan wasa ke mata……Bangaren Ma’aruf kam yarda kasan shine Amaryar haka ya koma kallon mutanen gurin yake kamar ya fasa kuka yana neman Madre amma sam bai ganta ba !kasa hakura yayi ya kira Maryam ya tambayeta “Ina Madre?
Ita Kanta tasan Madre boyewa tayi saboda son Autan nata sae dae ta kalleshi cikin kwarin guiwa tace “Auta Hidima tawa Madre yawa tana can gurin Family din su Abba suna kara gaisawa”
Daga haka ta ja hannunshi k’annan Madre suka rufa masu baya har kusa da sabowar motarshi da Abbah ya bashi yau suka shiga suka tafi ……
Haka suka isa gidanshi dake GRA wanda tun daga waje zaka gane tsaruwar da gidan yayi ……
Baban falon gidan dake dauke da Royal chairs suka samu masauki yayin da ya zube saman three siter ya dafe kanshi dake masifar sara mashi ……Ita kam Sumayya tsaye tayi ta ware hannaye tana juyi a hankali tare da karewa falon kallo har tsawon minti goma sannan ta dawo ta zauna saman hannun kujeran tare da dafa bayanshi tayi kasa da kanta ta kira sunanshi ……
Dagowa yayi ya kalleta sannan ya da kamo hannunta ya dawo da ita gefenshi ya zaunar da ita ya mayar da kanshi ya tallabe tare da lumshe ido ……
” Yaya Ma’aruf yunwa fa nake ji ……”ta fada lokacin da ta kai hannunta ta shafa sajenshi ……
Shiru ya mata ya sauko wayarshi ya typer message ya tura sannan ya kalleta yace “Ki jira ga Ahmed nan zuwa “
Turo baki tayi tace “Aa ba sae ya zo ba gaskia na daina jin yunwar……!
A Hankali ya kalleta yace “Why?
Kai tsaye tace “Wannan lokacin bai kamata kowa ya shigo mana gida ba !
Ya bude baki da niyar mata magana yaji karar doorbell ya mike ya nufi kofar ……Ahmed ya gani rike da leda ya mika mashi tare da mashi bankwana ya juya ……
Ko da yazo gabanta ya aje ledar ya juya ya shige part din dake kallon tsakiyar falon abunshi ……
,Ita kam Sumayya gyara zama tayi ta fara cin naman kajin dake ciki sannan ta kwankwadi Fresh milk tare da lumshe ido sannan ta mike ta nufi handbag din ta ta fito da wani ruwan magani ta shanye tas ta aje robar ta kara janyo wani dunk’ulen bak’in abu kamar curin dawo ta fara ci tana yatsina fuska saboda masifar d’acin da abun ke da shi ……Wasa wasa sae da ta fiddo kalaluwar magani kusan Biyar ta cinye sannan ta mike tana mika ta tsallake ledar kajin ta nufi Part din ta taga Ma’aruf ya nufa ……
Tsaye ta iskeshi gaban mirrow daure da towel yana combing din sumarshi !Ta cikin mirrow din ya hangota ya dauke kai kamar bai ganta ba ……
Murmushi tayi sannan ta fada toilet rike da handbag dinta a hannu!shi kam tab’e baki yayi ya d’auko jallabiya fara k’al ya sanya tare da shinfida prayer mat ya kabbara sallah ……
Koda Sumayya ta shiga toilet inserting magunguna ta fara yi kamar hauka sannan tayi wanka ta fito daure da towel a k’irji lokacin har ya sallame sallarshi har ya koma ya kwanta saman gado abunshi ……
Daga bakin toilet din ta saki Towel dinta ta hawo gadon ta kwanta bayanshi saboda masifar feelings din da take ji saboda kayan matan da ta kwankwada ……
Gabanshi yayi masifar faduwa take ya fara tunanin anya Sumayya bata bin maza kuwa?Wani bangaren na zuciyarshi ya bashi amsa da ina zata gansu bayan kullun Madre na tsare da ita a gida ……
Kiran sunanshi da tayi ya katse mashi tunaninshi yayin da ta fara fad’in “Sorry Bana iya kwana da kaya a jikina bayana ke rashes”