ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Banza ta mashi ta juyar da kai gefe guda……
Wayar ya bi da harara sannan yasa hannu ya dauka yayi shiru ……
Daga dayan bangaren akace “Sir akwae wani case na AFP da akayi reporting a jihar katsina ……So yanzu aka turo kai zakayi verifying dinshi daga England……”
Kallon Madre din yayi yaga shi take kallo “Hello……”ya fada kamar zaiyi kuka tare da yanke wayar ……
“Madre bana jin abunda suke fada ……”ya fada kamar ya fasa ihu
Wayarta kirar IPhone7 ta mika mashi tana fadin “Ka kirasu anan !wallahi Ma’aruf duk abunka sae ka dauki wayarsu……”
“Madre ……!ya fada kamar yayi kuka sannan ya dauki wayar tashi ya sake kira ……
Bai amsa sallamar da akayi ba yace “Ka turo man Number State consultant dinsu……”daga haka ya mike ya bar falon ……
Kyakykyawar matashiyar yarinya ta shigo sanye da atampha mai ruwan goro sae zanen ganye da akawa ado da ruwan toka kayan sun dace da jikinta……
Da fara’a ta isa gurin tana fadin “Madre Barka da safiya……”
“Yauwa Sumayya!shiga dakina saman mirrow ki dauko trcts ki kaima Ma’aruf idan ya fita ya mikawa Abbansa office ni zan fita……”
“To……” ta amsa tare da mikewa ta shiga dakin ta dauko sannan ta fita daga falon……
Sai da ta wuce balcony sannan tayi tafiya mai tsawo ta isa wani katon part dake zagaye da glasses……Wani red abu tayi clicking a jikin kofar sannan ta bude ta shiga ……
Katon falone kamae wanda ta baro sae dae wannan ya banbanta da wacen saboda complete kayan dake falon red ne harta plasma dake ciki ……
“Yaya Ma’aruf ……”ta fada tana bin falon da kallo……
Banza ya mata yana zaune bisa kujeran dake bayanta ……ganin zata shige bedroom dinshi ya sashi fadin “Sumayya……”Kasan makoshi ……
Juyowa tayi tana turo baki tare da fadin “Shine ka shareni……?
Ba tare da ya kalleta ba yace “Menene?
Kujeran dake kusa dashi ta zauna tana fadin “Madre tace na kawo maka ka kaiwa Abba idan ka fita……”
“Aje ki tafi……”ya fada ahankali ba tare da ya kalleta ba ……
Ta san hanlinshi sarai ta mike a sanyaye ta bar dakin ……
《》《》《》《》
Tafiya sukayi mai tsanin nisa sannan Hafsatun ta zube bakin wani iccen kanya tana haki ……
“Sannu Umma……”Lauratu ta fada tana dafa bayanta ……
A Wahale ta gyada mata kai sannan ta sa hannu ta karbi jaririyar dake ta mutsu mutsu a hannu Lauratu ……
Mama ta bata yarinyar ta karba da sauri tana wuntsila kafafuwa ……Murmushi Lauratu tayi ta kama kafar yarinyar tana fadin “Ummana da gaske wannan diyar Baffa ce……?
Da Sauri Hafsatun ta kalleta da idanunta da suka cika da kwalla sannan ta sadda kai tana goge hawayen ba tare da tace komae ba ……
Jikin Lauratun yayi sanyi tare da nadamar tambayar da tawa Umman tata duk da itama tana mamakin ta yarda zaa ce umman ta haihu ……Bayan tana sane da Baffanta da yayi shekara takwas a kwance ko hannu baya iya dagawa ,a inda yake nan yake kashi yayi fitsari sae dae Umman tata ke wanke mashi ……amma rana tsaka ace Umman ta haihu dole kanka ya daure……
“Kiyi Hakuri Umma dan Allah bansan tambayar zata maki ciwo ba ……”Lauratu ta fada tare da dafa Umma……
Bata ce mata komae ba sae bin kafafuwanta da kallo da tayi ,wanda suke wanke da jini ……rumtse ido tayi jin wani abu na tsira a kasanta sannan ta mikawa Lauratun Yarinyar ta mike da kyar tana fadin “Mu tafi Lauratu……”
Cire zaninta tayi ta goya diya dashi sannan ta kama hannun Umman tata suka yanki daji ……
Wannan karan tafiya kadan sukayi suka fara hango rukuni rukunim gidajen fulani dake cikin dajin ……
Wani Gidan gandu suka nufa ……
Yara dake wasa kusa da gidan suka dauki ihu “Ga Hasfuwalle ga hafsuwalle……”
Matan gidan da tsofaffi suka fiffito bakin kofar gidan suna fadin “Aradun Allah da gaske Hafsuwalle ce ……Sannu Hafsuwalle ansha hanya……Harda Lauratu yasin……”
“Ato Meye haka nake gani bayanki lauratu……?Cewar wata tsohuwa dake kama da Hafsatu kamar an tsaga kara……
Kallon Ummanta tayi da sauri sannan ta kalli tsohuwar tana fadin “Jaririyace Inno……”
“Ina kuka sameta……?cewar matan dake gurin kamar hadin baki ……
Wannan karan ma sae da ta kalli Umman tata wadda ta sadda kai kasa tana hawaye sannan tace “Ta Umma na ce……”
#HAJJA CE��
#FEEDOHM��
[12:03, 24/11/2017] hm: ���� ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》
����
��
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM��
&
K.A.S.Precious HAJJA CE��
*SADAUKARWA……*
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
Page *5-6*
*M*uryar inno ce ta kuma dukan dodan kunnan Hafsatuwalle "wai hafsatu sai kuka kike mana daga tambaya. Shin a ina kika samu jaririya d'anya sharaf?"
Kasa d’agowa tayi ta kallesu ganin gaba d’aya idanuwan su na kanta yara da manya karaf idanuwan jummai ya sauka akan kafar Hafsatuwa da jini ke bin ta tace.
“Shiiii kenan wallahi ‘yar tace ga alamar jinin haihuwa nan mun shiga uku.” Gaba ki d’aya mutanan wajan suka saki salati suna tafa hannaye, hakan ya k’ara tayarwa da Hafsatu hankali cikin sauri lauratu ta ja hannun Umman nata suka doshi cikin gidan da matan suka fito.
Cikin d’akin Inno suka shiga, itama da sauri ta bisu ciki “bafa zaku zauna min a d’aki ba alhalin bansan a ina kuka samo wannan jaririyar ba.”
Inno ta fad’a tana nuna jaririyar dake rungume a jikin lauratu wadda ke ta faman bacci hankalinta kwance.
A hankali muryarta na rawa hawaye sun kasa tsayawa a fuskar ta Umma tace, “jaririyata ce inno ni na haifeta yau d’innan…”
Salati Inno ta kuma saki tana kama ha6ar ta “Hafsatu tayaya kika samu cikin har kika haifi yarinya duk bamu sani ba, kuma ai munsan malam lado ba lafiya gare shi baya iya komai sai anyi mai taya kika samu ciki kuma ‘yar waye..?”
{{ }}
“Bari ni kundum wallahi yarinyar nan ta bani mamaki ta rasa cikin wa za tace sai lado, ladon da kowa ya sani ba lahiya ce dashi ba amma tace cikin shine…”
Mai-tafasa tayi maganar tana sosa wuyanta alamar taji kaikayi a gurin. Kundum ta sake rafka gud’a ayyirrrr-yirrrrr, “koma dai menene Abunda ke b’oye ya fito fili sauran bayani dai yana wajan Hafsatuwalle.”
“Tallahi kinji na rantse ko kundum? Yau da ace lado lajiyar shi lau hukuncin da zai yi kan Hafsatuwalle sai ya ninka wanda na mata…”
Lado dake kwance a d’aki sai faman k’ok’arin son yin magana yake amma ya kasa, hawaye ne suka fara zubo mai masu zafin gaske. Mai-tafasa ce ta lek’a d’akin ta ganshi sai kuka yake tayi saurin k’arasawa kusa dashi cikin takaici tace…,
“Yi shiru lado nasan Hafsatu ta cuceka, ganin baka iya komai yasa ta danganta cikin nan da cewar naka ne. Kayi hakuri lado wallahi da raina da lahiya ta bazan bari a cuce ka ba..”
Lado kam banda girgiza mata kai da yake yi babu wani abunda yake, hakan shine kawai sign d’in da yake iya yi hakan yasa ko fitsari yaji baya iya fad’a sai dai ya sake shi a wando. “Kayi shiru lado dan babu wanda ya yadda da zance Hafsat…”
Mai-tafasa ta fad’a tana fita daga d’akin ta karasa gurin kundum dake tayawta surfan masara suka ci gaba da tattaunawa akan maganar….,
{{ }}
Bayan fitar Sumayya da kyar Mu'aruf ya mik'e, bathroom ya shiga wanda ya had'u yaji komai ya k'arasa ya shiga jarkuse wanda aka cika da ruwa mai k'amshi. Ya dad'e a ciki kafin ya fito da bathrobe a jikin shi. Dressing room ya wuce wanda shima ya gaji da tsaruwa sosai, direct underwears drawer ya wuce ya bud'e gasu nan ajere kamar a company ya zari vest da trunks yasa saka sannan ya k'arasa dressing mirror ya zauna kan stool yana shafa lotion mai kamshi tamkar bayasan shafar.
Drawern kayan shi ya k’arasa ya bud’e wadda baki d’ayan gurin suit’s ne kamar na siyarwa kala-kala ya d’auki black color d’in ya sanya bayan yasa ta cikin white color…,
Gashin kanshi ya gyara sannan ya bi duk ilahirin jijin shi da turaruka kusan kala 6 masu kamshi ya sanya socks da sandal ya fito daga room d’in, be koma side d’in Madre ba kawai ya wuce parking lot ya bud’e motan shi white paradox dake ta kyalli ya bud’e yashi ga, office d’in abban shi ya fara zuwa…[13:32, 26/11/2017] hm: ���� ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》