ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Gyada mata kai yayi ba tare da ya juyo ba !Ita kam hakan bai hanata yawo da hannunta saman kirjinshi ba tare da daura kanta a bisa wuyanshi ……

Duk irin yarda yaso ya daure kasawa yayi dole ya juya ya fara mayar mata da martani yayin da ta fara fita hayyacinta tana kiran sunanshi cikin Zakuwa ……

《》《》《》《》

Hankalinta ta mayar Kan Sallau dake tambayar Lauratu ina zata je ……

Cikin ladabi Lauratun tace “Zan je na duba Baffa ne da jiki “

Daure fuska Sallau yayi yana kallon Fuskar Lauratu da tayi wa ado da kwalli tare da uban jan baki har saman goshi sannan ya kalli K’arama dake rike da hannun Lauratun tana lilo yace “Haba Lauratu Ahaka zaki fita mazan waje su kalle man ke fisabilillahi?

Shiru Lauratun tayi tana kallon K’asa yayin da K’arama ta sheke da dariya tace “Amma ko an cuci maza !Yaya Lauratu me zasu kalla da fuskanki duk bak’in kwalli?ni dai mu tafi “

Da yake ya san halin K’aramar bai ce mata komae ba ya kalli Lauratun cikin sanyin murya yace “Ki Taimakeni Lauratu karki fita da wannan kwalliyar ko wa ya kallah sannan dan girman Allahi ki saka katon Zani ki kulle duk jikinki ki zo muje na rakaku ku ganoshi mu dawo “

Gyada kai Lauratun tayi sannan ta koma daki ta goge kwalliyarta tare da dauko katon Zani ta lulluba ta sake fitowa ta iskeshi shi kadae ……Cikin sanyin murya tace “K’arama fa?

Kafin ya bata amsa suka hango K’arama ta fito daga dakin Zulai rike da katuwar kwarya ta nufi bukkarsu ta aje sannan ta ja ta tsaya bakin kofar gidan tare da juya masu baya ……

Zulai kam fitowa tayi daka bandaki ko buta babu ta wurgawa K’aramar harara kamar wata kishiyarta sannan ta shige daki tana waka a hankali ……

HAJJA CE????
&
FEEDOHM????

???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》

               ????????
                  ????

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????

SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu

 Page *43-44*

Da Sauri Lauratu ta nufi gurin K’aramar taja hannunta suka fita yayin da sallau ya mara masu baya kamar wani mai gadinsu yanayi yana kare Lauratun gudun kar yan garin Su kalle mashi mata sannan duk wani motsinta saman idonshi takeyi !Ita kam hankalinta naga K’arama dake ta faman fitar da numfashi kamar namijin zaki……

Suna shiga gidan suka iske gidan cike da jama’a an zagaye Lado dake kwance a tsakar gida yayin da maitafasa ke tsaye tana ta zuba ruwan tijara ita kadae ……
Sallamarsu ce ta saka matan garin fad’in “Gasu nan ma Maitafasa”

Ta watsa hannuwa baya ta nufosu ta cakumi wuyan K’aramar ta dire kusa da Malan Lado tana fadin “Kalli Fuskar wanga d’iya Lado ta gidan Ubanka tayi kama da zuri’armu da zaka fada man cewa d’iyarka ce “

A Sanyaye yana Zubar da hawaye yace “Wallahi Inna wannan d’iyar jinina ce “

“Lado banda mutunci fa !da kwarankwatsa ka k’ara maimaita wannan zancen sae na zabga maka mari a kumatunka duk da kake haka “ta karashe maganar tare da dungure mashi keya ……

Tab’e Baki Kundum tayi tana fadin “Ba’a banza ba Lado ya amshi wannan d’iyar ba Maitafasa……”

Juyowa tayi tana karkad’a yatsu tace ” Fad’a man a me ya amsheta algunguma? Yatsina hanci Kundum tayi ta juya k’eya ba tare da tace komae ba sae uban tsokin da ta ja……

Wata mata dake tsaye cikin garke tace “Taya bara ya amsa ba bayan ita kanta yarinyar Mayya ce “

Da Sauri Maitafasa ta saki wuyan K’arama tare da dafe kirji tana fadin “Raba ni da aikin mayu !Ke Lauratu “

Daga kai Lauratun tayi ta kalleta sannan ta kalli K’arama dake ta raba ido tana kallon mutanen gurin !ta d’aga k’afa zata isa gurin Sallau ya kamo hannunta yace “Zan Dauki komae a duniyar nan amma banda cin zarafinki Lauratu “

Kallonshi tayi da idanunta da suka ciko da kwallah ta gyad’a kai a hankali sannan ta zame hannunta daga rik’on da ya mata ta nufi inda su Maitafasar ke tsaye ta kama hannun K’arama ta rike ……

Ihu Kundum ta saki tare da zubewa k’asa tana fadin “Dan Allah kiyi Hakuri karki cinyeni yar nan “

Mutanen gidan suka dauki bahaggun salati mara karshe suna fadin “Shi kenan ta kama Kundum” yayin da suka yo kan K’aramar suka danketa kamar wata katuwar Mace suna fad’in “Wallahi Sae kin tsallaka ta munafukar yarinya daga zuwa zaki kama ta” wata ta kai mata rankwashi a tsakiyar kai ……

Dafe gurin tayi tana turo baki tace “Wace?

Uban rankwashi Maitafasa ta kuma kai mata tana fadin “Hafsuwalle ce dan ubanki “tare da watsa bak’in hannunta saman fuskarta sannan ta kashe ta da mari lokaci guda ta ta cakumi kwalar rigarta ta d’aga ta sama ta tsallake Kundum da ita sannan ta direta k’asa cikin mugunta da zulunci ……

A Jiyar Zuciya Kundum ta saki ta mike zumbur ta nufi bukkarta tana d’angyasa kafa rike da kirjinta tana hucin wahala tare da zare idanu ……

K’arama kam kuka ta saki da karfi saboda yarda Maitafasa ta direta k’asa har sai da dutsi ya fasa mata tafin kafarta !Yayin da Lauratu ta rungumeta da sauri tana kuka ta nufi Hanyar barin gidan da ita !amma mugayen matan dake zagaye da gidan suka fara dukansu suna fadin ” munafuka……”

Sallau dake tsaye bakin Zaure ya karaso cikin gidan ya zame masu kamar Mahaukaci ya kwaci Matarshi ya rungume suka bar kauyen yayin da ita kuma tana rungume da K’arama dake ta faman tsuka tana goge hawayenta!

Kundum kuwa na shiga daki ta fara karkada jimammen kugunta tana gwatso tare da gwalo !Ji tayi kamar ana dukan fatar jima a kasa !bata damu ba ta janyo wani kodadden zani zata daura lokaci guda dakin ya kauraye da duhu yayin da ta gwalalo ido waje tana lalubar kofa amma ta rasa ta……

Cikin dauriya ta fara karanto addu’ar su ta jahilai mutanen da “Yar kyalwa baiwaye dakin Kunduma tantar tantar yar kyalwa kunna hitila ……”

K’arama ta gani duke gurin kafarta yayin da ta kama agararta ta ja cikin mugunta ……

Cikin jin haushi Kundum tace “Awo kece munafuka to da kwarankwatsa sae dae a fitar da gawarki dakin nan ” Ta Duka da niyar cakumo K’arama amma ta nemeta ta rasa…… Ihu ta k’wala yayin da fitsari ya samu damar sulaluwa ……

K’arama ta gani tana yawo saman dak’in dauke da katuwar wuka jawur da ita tana cakama iska !Duk lokacin da ta caka wukar Azabar a cikin Kundum take karewa ……Ihu ta farayi tare da zawo tana neman taimako amma babu mai jinta duk mutanen dake cikin gidan ……Yawan K’arama ya linko sau shiddah yayin da manyan hakora suka fito ta karkashin habarta ta fara zagaye Kundum dake fitar da nishi sama sama ……Azabar tsoro ta saka Kundum sandarewa a gurin yayin da ta sulale ta gaba ta fadi saman tarin kasar dake zube a tsakiyar dakinta ……

Malan Lado kam tunda ya rufe idonshi yana hawaye bai sake budewa ba har sae da tarin matan dake tsakar gidan suka watse sannan Maitafasa ta matso ta zauna kusa dashi tana Fad’in “Ladona Ladona ashe bayan kana kwance Hafsuwalle Bokaye ta fara nema don ka amsa Wannan Mayyar diyarka ce”

Girgiza kai yayi cike da takaici yana da tabbacin Sharri ne irin na Maitafasa ……

“Ladona shi yasa naga wannan yarinyar tana zuwa baka abinci ashe magani suke barbada maka a ciki” Ta karashe maganar cikin sigar kwantar da murya……

Har lokacin bai bude idonshi ba sae dae hawayen dake zuba ……Dariya tayi tace”Yanzu da bakinka Ladona babu sauran kuka yanzu ma jira nake Hansai ta dawo garin don jiya Mai unguwa yace man yau da mairaice zata dawo shi yasa kaga yau ko tafasa banje debowa ba na tanadi gororina da sanduna na dukan Hansai !kai Lado har dae likafanin Hansae na tanada don wallahi karamin yaki zaayi a wannan kauyen yau……Ina Sonka Ladona duk wanda yace zaya tabaka a garimnan to wallahi baya da riba a rayuwa……”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button