ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Shiru yayi ba tare da ya bude idonshi ba haka ta kare zamanta tare da surutun ta bai tanka mata ba ……
Wani Yaro ya shigo da gudun tsiya yana fadin “Hansai ta dawo Maitafasa……”

《》《》《》《》

INA AMARYA SUMAYYA?

Dakyar Ma'aruf ya shigeta lokacin ba ita kadae ba shi kanshi ya wahala……Azaba da rad'ad'i suka dirar mata lokaci guda yayin da numfashinta ya janye gaba daya ……Ma'aruf kam bai san wainar da ake toya wa ba kawae aiki yake ba tare da ya lura da bata numfashi ba !Tun yanayi abun yana gamsar dashi har ya koma yanayi don dole saboda ya k'asa hakura ya barta !Sae wajen asubah sannan yayi kokarin tilasta kanshi ta hanyar sulalewa kasan rug din dakin ya zube ba tare da yasan inda kanshi yake ba ……

Sanyin asubah ya hura Sumayya ta ja numfashi da kyar ta kwalla Kara saboda axabar rad’ad’in dake ratsata……Uban gayyar kam Uban tsoki ya saki wanda shi kanshi ya rasa na menene lokaci guda ya dafe cikinshi yana juyi a hankali ……

Kusan Awa daya tana kuka da karfi tare da kwala mashi kira ta kasa koda motsi !Da kyar ya mike yana kallonta da idanunshi da sukayi jawur lokaci guda ya dauke kai tare da mikewa yana dafa bango ya nufi toilet……

Ya dade cikin bathtub din sannan ya fito har lokacin yana jin Kukan da Sumayyar take !Tausayinta yaji lokacin da ya fito yaga yarda bedsheet din yayi kaca kaca da jini ……Sae da ya zura kayanshi yayi sallah sannan ya kalleta tayi lamo jikin pillow kukan ya daina fitowa ! Shi kam duk da baya neman mata amma yana zargin akwae abunda Sumayya tayi amfani dashi da ya kusa halaka su haka ……Kit din da Maryam ta saka mashi a mota ya fita ya dauko ya bude ya fito mata da jallabiya baka da hijab ya aje saman gado ya kalleta cikin kulawa yace ta saka ya kaita asibiti……

Kuka ta saki cikin shagwaba tace “Ka Saka man Ya Ma’aruf wallahi bana iya koda d’aga hannuna……”

Gyad’a mata kai yayi ya janyota ya cire blanket din da ta rufe jikinta dashi ya fara canza mata kaya !Bala’in da take ji bai hanata tuna Matarnan mai kayan mata tace mata bayan komae ya kammala ta sake saka wani magani dake cikin karamar roba cikin ruwan zafi ta zauna zata sake komawa kamar budurwa……

Girgiza kai tayi da ta tuno azabar da tasha jiya yayin da wani bangare na zuciyarta ke bata shawarar ta sake gwada may be don farkone shi yasa ta wahala haka ……Kallonshi tayi a sanyaye tace “Ya Ma’aruf ina son zan shiga toilet nayi wanka tukun ……”

HAJJA CE ????
&
FEEDOHM????

???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》

               ????????
                  ????

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????

SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu

  Page *45-46*

Ba tare da ya kalleta ba yace “Zamu je asibiti Sumayya……”

“Wankan na da amfani……” ta fada tana kallon erection dinshi
Kallonta yayi sannan ya kalli inda hankalinta yake ya saki Dan karamin tsaki ya mike yana zabga mata wani uban kallo ya nufi Bakin gadon ya dauki wayarshi ya kunna sannan ya zo ya sabeta ya fita da ita ……

Sae da suka je asibitin sannan ta gane kuranta don ba karamin aiki ya mata ba !Sae da aka mata Propofol injection sannan aka mata dinkin ……Doctor din kam bai samu fuskar wa Ma’aruf din dogon sharhi ba ……

Sae kusan 12 sannan suka dawo gida ya iske Madre ta aiko masu da breakfast mai rai da lafiya !Sae da ya bata taci sae shagwaba take mashi sannan ya bata magungunan da suka basu tayi bacci !tsayawa yayi yana kallonta ba laifi itama ta had’u kuma yana mata son da yakewa yan uwanshi sae dae sam baiyi tunanin zai iya rayuwar aure da ita ba saboda masifar rawan kanta!

《》《》《》《》《》

Su K’arama na isa gida suka iske mutanen gidan cirko cirko tsakar gida ummansu kuwa na tsakiya durkushe daga mai dunguri sae mai zagi ……Kallo Da K’arama ta mata ta dauke kai ta koma bakin Bukkarsu ta zauna ta zauna tana duba kafarta inda Maitafasa taji mata ciwo……

Zulai ta juyo tana kallon Lauratu da tayi mutuwar tsaye tana kuka ganin kaskancin da akewa Ummansu tace “Kuka yanzu kuka fara Lauratu indae har Uwarku bata daina halin bera ba……”

A Razane take kallon Zulai sannan ta kalli Inno dake tsaye bakin bukkarta tare da kallon Sallau ta sake kuka tana fad’in “Wallahi Ummana bata halin Bera sallau……”

Gyada mata kai yayi shima kamar yayi kukan yace “Na gasgata Lauratu!Inna Zulai dan girman Allah ku daina abunda kuke yi ku tausayawa wannan baiwar Allah ku bar zuciyarta ta huta!

Gaba daya suka rafka salati wanda dama sarar mutanen gidan ce yayin da jummai tace “Sallau kaima an jike ka kenan……”

"Wallahi baa jikeni ba !Shin me ta maku da zaku sakata tsakiya kuna wulakantata haka Inna Zulai?Shin ita ba diyar nan gidan bace ?koko ance maku Inno bata kaunar yarta take zuba maku ido tana kallonku shin ku baku san Kawaici bane inna Zulai……"

Matar Bedo tace “Yanzu dae Sallau kana kare surukarka !Hafsuwallw daga ido ki kalli Sallau ki ce bake kika Saci Kwanon Man Shanun Inna Zulai ba……?

Saurin Kallon K’arama sukayi shi da Lauratu sannan ya mayar da kallonshi ga Hafsuwalle dake duke tana hawaye amma ta kasa dagowa ta kallesu ! Tana da tabbacin dakinta aka ga kwanon man shanun amma tayi imani sae dae idan K’arama ta dauko shi……

K’arama tayi tsallen kura ta dira gaban Umman tata tana dangyasa kafa tare da yarfe hannu baya tace “Abun Sata na Sata ne Zulai……”
Hafsuwalle ta janyota ta zaunar da ita kasa tana kallonta da rinannun idanunta alamar tayi shiru ……
Makale Kafada tayi tace “Ba zanyi shirun ba Umma bayan itama man Shanun na sata ne gidan Fulani ta shiga ta iske sun gama kad’i Habee ta shiga daki ta dauko kwarya ta satoshi……”

Uban Mari Zulai ta zabga mata tana fadin “Dan Ubanki ni zakiwa Sharri K’arama ?In je in sawo man shanun hayin dan malan ki ce sato shi nayi !To da kwarankwasa bara Ardo ya shigo yau sae dae ni ko ku a gidannan ……”

Mikewa tayi tana Murd’a hannu ta fita yayin da zulai ta cigaba da zabga ruwan tijara yan gidan na tayata !Hafsuwalle da Lauratu kam sun yarda da abunda K’arama ta fad’a sae dae babu wanda ya motsa daga inda yake ……

K’arama kam gidan Fulani ta nufa ta iskeshi Zaune yana gyara lalataccen kekenshi ……Da yake tasan basu zama inuwa daya dashi don haka ta tsaya daga nesa ra d’aga murya tace “Fulani an kama barauniyar Man shanunku……!
Da Sauri ya mike ya dauki katuwar sandarshi yana fadin “Ke K’arama ban san shegantaka yasin na iso nan sae na k’wadeki……”

Tab’e baki tayi tana d’age kafa guda tace “Yasin da gaske nake Fulani Zulai Matar Ardo ce ta sace maku man shanu kuma kazo gidan yanzu na,nuna maku……”

Kamar sakarai ya biyota har cikin gidan yana fadin “Yasin idan karya kike sae na k’wad’eki……”

Murgud’a baki tayi tace “Idan da gaske nake fa?

Washe baki yayi yace “Zan baki naira Goma……”
Dariya tayi sannan suka karasa cikin gidan kallo ya koma kan fulani da K’arama ta shige bukkarsu ta fito da Kwaryar Man shanun da ta kai ta mike mashi tana fadin “Zulai ta Sata shine nima na dauke na kai Bukkar Ummanmu mu dinga sha !Sae suka gani suka ce Ummana ta sata ……”Ta kalli Lauratu tace “Dan Allah yaya Lauratu ba kowa ya rasa ba kenan ?

Ita kanta Lauratun bata san sadda murmushi ya subuce mata ba ta kama hannun Ummanta ta dagata ta kaita har bakin bukkarsu sannan tace “Allah zaya warware komae Ummanmu……”Daga haka ta juya ganin K’arama ta rike kwarya tana fadin “Bani kudina Fulani sannan kaje ka turo matarka tawa Zulai yarda tawa Ummanmu……” Kudinta ya bata ya juya yana kwafa ……

Matan gidan kam surutai suka fara yi Kasa kasa sannan suka watse suka bar Zulai da ta fara Borin karya!!!!!

【】

Maitafasa kam jin cewa Hansai ta dawo ya sata kwasawa bukkarta da gudu ta dauko wata katuwar gora tare da farin yadi ta fita gidan ! Kirjin Malan Lado ya fara dagawa da karfi saboda masifar bakin cikin dake cike da zuciyarshi ……Lokaci guda numfashinshi ya fara sarkewa hakoranshi suka fara,haduwa da juna !A Hankali ya fara maimaita kalmatusshahada sannan idonshi ya rufe ruf da guntun hawayen da ya gangaro……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button