ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Inda ake aje Mankara Mai tafasa ta leka tare da cilla farin yadin tana fadin “Likafaninki da mankararki Hansai sun shirya “Sannan ta fada gidan Mai unguwar !Cikin Sa’a ta iske Hansai tayi goho tana damawa Shanu dussar ai kowa ta daddage ta maka mata sandar a baya……Kara ta kwalla tare da gantsarewa ta kife cikin dussar don ba karamin duka Maitafasa ta mata ba……

Matan gidan suka nufo su dakyar suka rirrike Maitafasa da ta cigaba da kwadawa Hansai Sandar bayan ta kaita kasa ……Dakyar suka kwaci Sandar lokacin Hansai an jigatu jini ya wanke mata fuska hannunwanta kuma da take kare dukan sunyi sumtum dasu……
“Ku barni na Kashe kafura tun kafin ta kashe man Ladona……”Mai tafasa ta fada tare da rarumar katun dutsi ta jefawa Hansai dake jan Kafa ta fada,bukkar Mai unguwa tana kwala mashi kira……

Da yake matan gidan sun san abunda ke tsakanin Hansae da Maitafasa masu bata hakuri nayi masu turata nayi……
Hawa take kamar fulawa ta cigaba da fadin “Wallahi ni da ke Hansai Allah kadae ya isa ya shiga tsakani don ko mijinki bai isa ba wallahi !Duniyar nan duk mai shirin kashe man Lado ta wallahi ni zan fara kashe shedani !Ni Uwar Mai tafasa Uwar Lado da ka taba Ladona kara ka kona mai unguwa da ranshi wallahi!

Da Kyar suka samu ta bar gidan ta fita tana fadin “Wallahi sae na dawo kuma daga yau duk abunda ya samu Ladona sae na dawo na juyeshi a kanki banza bakar munafuka !Yo dake Hansai ba kara Kundum ba faran munafuka akanki baka…Banda jaraba har yanzu baki bar kishi ba dani bayan mijin yayi shekara sha biyar da rasuwa Hansai !Kiyi kishi da Buwale da Kande mana tunda yanzu mijinsu kike aure………”
Da Haka har ta bar gidan ta shiga gidansu Lanto ta karbo Curin hura uku da nonon Goma ta nufo gida zata damawa Lado……

Tana shiga gidan ta wuceshi ta dauko kwarya da koshiya ta fito ta zauna tana fadin "Su Ladona bacci aka samu ?
Shirun da taji ne ya sata cigaba da damun furarta tana yar waka tare da daga murya tace "Wae Kundum lahiya kike shiru?Kundum dake zube tsakar daki bata san me ake ba ……

Sae da ta gama damun Furar sannan ta matsa tana bubbuga shi tace “Ladona tashi ka kurbi fura sae ka cigaba da baccinka ko?

Zaro idanu tayi ta wuntsilo ta dawo gefen da yake kallo ganin babu numfashi a tare dashi ta kanga kunnenta a hancinshi tana kiran sunanshi a rude tare da jijjigashi ……

Kururuwa ta saki tare da dafe Kai tana kiran “Ladona” sannan tayi hanyar dakin Kundum tana kururuwar daya dawo da Kumdum daga duniyar doguwar sumarta……
A Tare suka fito dakin ko wace ta kama hanyar gabanta ……

Cikin lokaci Kadan gari ya gauraye da Rasuwar Malan lado yayin da Maitafasa ke kuka kamar zatayi hauka ! Duk wanda yaji rasuwar sae ya tausayawa Maitafasa saboda an san irin son da takewa Lado ……

Likafanin da ta tanada don Hansai dashi aka nannade Ladonta !Maitafasa bata rage kukan da take ba sae da aka dawo rufo lado Limamin ya kirata yana fada mata cewa a kabarin Lado sun iske ruwa mai sanyi a kwance tare da goro fari kyal guda biyu a ciki ! Sannan ta sassauta kukan da take ……Gida ya cika da mutane har da wasu yan garuruwan amma Kauyen su Hafsuwalle basu san wainar da ake toyawa ba ……

HAJJA CE ????
&
FEEDOHM????

???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》

               ????????
                  ????

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????

SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu

   Page *47-48*

K’arama na bisa iccen mangoro Ard’o yazo wucewa Kallonta yayi ya kuma kallonta ganin ta kwantar da kanta jikin wani reshe tana kuka !har zai wuceta yaji ta bashi tausayi karo na farko tun tasowarta don yana da tabbacin bai tab’a gani K’arama a haka ba ……
Sae da yayi Jim sannan yace “Hafsatu……”
Kallonshi tayi ta rufe idonta kwallar dake ciki ya gangaro saman kuncinta ……

Tausayinta yaji sossae ya saka hannu ya daukota ya dire ta k’asa yana tambayarta abunda aka mata ……

Kasa magana tayi sae dae Hannunta da ta watsa alamum oho……
Cikin kulawa yace “Wani ya dakeki ne Hafsatu?
A Hankali tace “Kai ni Bansani ba Ard’o……”

Gyada kai kawae yayi ya wuceta ya shiga gida !har zaya wuce ta gaban Bukkar Hafsuwallen sae ya kasa !wani bangaren na zuciyarshi na kwad’aita mashi ganin Hafsuwallenshi yayin da Tausayi da Kaunar da yake mata ya tsaya mashi a zuciya !A Sanyaye ya tsaya daga bakin Kofar ya kira sunanta “Hafsatu……”

,,Da Sauri ta fito don tabbatar da ko Ard’on ne ke kiranta kowa gizo muryashi take mata ……Ganinshi ya sata zubewa gabanshi tana goge hawayen farin cikin da suka zubo mata ……

Kau da Kai yayi yace “Hafsatu ya na ga Hafsatu K’arama cikin damuwa shin ko wani abu ke faruwa ne ?

Girgiza kai tayi tace “Babu Abunda ke faruwa Ard’o” muryarta na rawa……

Kallonta yake cike da tausayi tayi bak’i ta jeme kamar ba diyarshi ba !anya ya mata adalci a matsayinshi na Uba?Cikin tausayi yace “Ki je ki daukota Hafsatu Idan yunwa take ji ki shiga cikin bukkata ki dauko fura ki bata na yarje maki Hafsatu……”

Kallonshi take ya dawo mata Ard’onta mai kaunarta……Ta Girgiza kai tana share hawaye tare da murmushi lokaci guda tana kallonshi har ya nufi Bukkar Zulai……Sanan ta mike ta dauko mayafinta ta fita neman K’arama……

 Bakin iccen ta ganta jingine tana dafe da kanta kiranta tayi amma bata amsa ba haka bata dago ta kalleta ba ……Har sae da ta zo kusa da ita ta dafa bayanta sannan ta kalleta tare da fashewa da wani irin kuka !

“Me aka maki K’arama?Ta fada a hankali tana kallon jikinta da ke kyarma ……

"Baffa Ummana !ance baran sake ganinshi ba "ta fada tare da rungumeta……

Cikin sauri tace “Waya fada maki K’arama?

Kai tsaye tace “Yar Kudundub’a ce !
Girgiza kai tayi duk da gabanta dake fad’uwa tace “Wacece Yar kudundub’a? Karya take maki Ko jiya ba kinga Baffan naki ba?

Shiru K’arama tayi tana kallon Umman kafin ta jata da karfin kamar ba ita ba ta nufi Hanyar garinsu Lado!Duk Yarda Umnan taso ta ki zuwa amma ta kasa !har sae da suka isa bakin garin sannan gabanta ya tsananta fad’uwa!Hango mutane a kofar gidan ya tabbatar mata da zancen K’arama……Yayin da taja ta turje bakin wani katon icce tana kuka mara sauti ……

K’arama na ganin ta tsaya ta saki hannunta ta nufi cikin gidan har lokacin hawaye ke kwance a fuskarta !Kusa da Maitafasa ta rab’a ta zauna tana kallonta Kamar yarda maitafasar ta tsareta da ido tana jan majina ……

Hannun K’arama Maitafasa ta kamo sannan ta mike ta tsaye ta fashe da kuka tana fadin “Indae ba Hansae ba to Wannan yarinyar ta Kama Ladona”

Maganganu mutanen dake cikin gidan suka fara k’asa k’asa kafin Kundum dake ta cije lebe tana son tayi magana amma tana tsoron Abunda ya faru ya sake faruwa!daurewa tayi tace “K’arama ko shegiy……”Maganar ta makale yayin da ta hadiye miyan tsoro tana murje idanu……

Kukan Maitafasa ya tsananta tace “Dan Allah Hafsatu K’arama indae har kinsan ke kika cinye man Lado ki taimaka ki fad’a man a tonoshi ki tsallakeshi ya tashi !wallahi ina son Ladona kamar raina ki taimaka man yar nan na tuba ki yafe man ……” jan majina tayi sannan ta kara da cewa “Ni Maitafasa ban tab’a ganin munafuka mai son raba uwa da d’a ba irin……”ta kuma yin shiru tana kallon K’aramar sannan tace “Na Tuba Hafsatu……”

Girgiza kai K’arama tayi ta rungume Maitafasa da sauri yayin da Maitafasar ta fara kokarin tureta amma taki Sakita sae Uban kukan da takeyi……

《》 《》《》《》

Ma’aruf kam yana kokarin bawa Sumayya hakkinta soyayya yake nuna mata dae dae gwargado dan ma wani lokacin rawar kanta na bata mashi rai !Ga Uwa uba rashin sirri duk wanda ya shigo gidan sae ta bashi labarin rayuwar da suke ……Yau ma kamar kullun ya shigo gidan ya iske Beebah kawarta zaune suna fira a falo ……

Shigowarshi bata sanya Sumayya daina fadin “Ke wallahi Beeba Aure dadi gareshi !ke ni fa yanzu bana kwana bisa pillow sae dae bisa kirjin mijina ……Kin san me yafi birgeni a jikin Ya Ma’aruf?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button