ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Jikinta ya gyara mata sannan ya sanya mata doguwar riga sai faman narke mai take a haka ya tafi da ita asibiti.suna zuwa gwajin farko ya tabbatar da cikin ta 4 month’s, sosai Ma’aruf yayi farin ciki sai dai ya kasa nuna mata sabida karta kuma narke mai. Tunda ya tsaida motan tayi saurin fita zuwa sashen Madre cikin karad’i ta dinga kiran sunan ta Madre! Madre!! Madre!!!… Tayi upstairs da gudu cikin zumud’i tana zuwa ta fad’a jikin ta tare da kankameta ba kunya Madre tace,

“Lafiya Sumayya kike irin wannan murnar? Madre ta fad’a tana rik’e da kafad’ar Sumayya wacce bakinta yaki rifuwa, idanta kyar cikin na Madre take fad’in.

“Madre am pregnant!,wallahi yau four months kenan Madre.” Ta kuma kankame ta, Madre ta zaro ido cikin mamaki, Ma’aruf dake kokarin shigowa yayi cak!,yana jin kalmar da Sumayya ta fad’a a hankali ya juya cikin takaici ya koma downstairs yana jin wani bak’in ciki a zuciyar shi.

“Why Matar shi bata da sirri ne a rayuwar ta? Me yasa take son fallasa duk wani sirrin su, bata jin kunya ciki har da mahaifiyar shi? Demit….!

《》 《》《》《》

K’ara k’ank’ame Maitafasa k’arama tayi tamkar zata shige cikin ta, tsoro da bak’in ciki suka had’u suka yiwa Maitafasa tayi saurin ture k’arama daga jikinta tana fece majina idanuwanta sunyi jawar tayi hanyar da girken dabbobinta ke gurin, wani dogon ice ta d’auka tayi kan k’arama dashi karaf ta sauke dukan jikin Hafsatuwalle wadda ta k’araso gurin da saurinta.

“Wallahi tallahin Allah sai taci na jaki, yau yarinyar nan baxata kwana ba sai tabi ladona inda takai shi..” Maitafasa ta fad’a tana k’ara dokawa Hafsatuwalle icen hannunta.

Da sauri mutane suka rufar musu Umma na kuka ta kare k’arama da hannunta wadda ke faman ture Umman tata amma tak’i sakinta, isowar mutane yasa Umma mik’ewa da sauri taja hannun k’arama suka sa gudu amma duk da haka mutanen kyauyan basu dena binsu da duka ba k’arama na cizon Umma dan ta sake ta amma taki gurin har fashewa yayi amma tak’i sakinta sai da suka dangana da kauyan su.

Da guru tashiga cikin bukar su tana kankame k’arama take mata wani razananan kallo tamkar wata kura, da kakkausar murya tace “Umma ki sakeni nace… !.”

Muryar su jummai ce ta k’atse Umma dake shirin yiwa k’arama magana. “Wallahi yau sai kun fito daga cikin d’akin nan, sabida kar asirinku ya tonu shine an samu lado ya warke zai fad’i gaskiya shine ‘yar kaniyar maiyyar ‘yarki taje ta cinye kurwarshi, toh wallahi k’aryar ku ta kare cikin gidanga….” Baki d’aya mutanen gidan dana kyauyan su lado suka amsa da kwarai kuwa wallahi….

Ard’o ne ya shigo a rud’e ganin gugun mutane yasa shi k’arasawa gurin yana tambaya. “Yo meye kuwa Ard’o, banda shegiyar yarinyar nan da aka kafe cikin gidan nan tana ta iskancin da take so… ! toh yau maitar tata tafara aiki dan taje ta cinye kurwar lado sabida ya warke zai fad’i gaskiya….”

Zulai ta fad’a tana cillara hannu sama tare da dukan cinyar ta idanuwanta har kankancewa suke sabida jaraba tamkar ita akayiwa rasuwar. Su Maitafasa ne suka k’araso harda katuwar addar ta wadda ada lado yake zuwa farauta da ita, suna zuwa gida ya kuma kacamewa da tashin hankali a cikin gidan.

Lauratu na jikin bangon d’akinta sai rusar kuka take yi gashi sallau baya gidan ya tafi kasuwa. Inno ma tana tsaye bakin bukkarta tama rasa abin yi sai ido kawai da ta zuba musu…….

FEEDOHM????
&
HAJJA CE????

???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》

               ????????
                  ????

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????

SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu

Wannan shafin nakune kyauta domin jin dad’in ku, hak’ika hajjafeedohm na alfahari daku grps d’in Feedohm Novell’s???? & Hajja ce ????novels grp we so much love you people d’in dake ciki….????????

 Page *51-52*

Tsawa Ard’o ya daka musu baki d’aya suka yi shiru,inno ma ta k’araso jikinta duk a sanyaye,lauratu kuwa kasa fitowa tayi sai faman kuka take cikin masifa Maitafasa ta kali Ard’o tana mai masifa.

“Kaji dallah can gafara kasa anyi shiru kayiwa mutane tsaye, inzaka yi magana Ard’o kayi kuma kasa mutanan nan su fito komu mushiga ta k’arfi ardun Allah.” Mai-tafasa ta fad’i tana yi kamar zata makewa Ard’o fuska, nan da nan mutanen wajan suka suma hayani guru ya kuma kaurewa da maganganu da habaice-habaice.

Cikin bukar kuwa danbe ake sha tsakanin Umma da k’arama, cikin wani mugun kallo da k’arama kewa Ummanta ta kalleta tana huci numfashin ta tamkar ta tattaro ma al’umar garin ta had’a tace wa Umman ta “baza ki kyaleni bane?… ! tallahin Allah aradu zan makeki na fita wallahi sai na rama dukan da akai miki, Umma ki rabu dani ki kyaleni ki kyaleni.” Kalaman da k’arama keta gayawa Umman ta amma ta matseta sai faman naushin cikin ta take yi Umma na kuka sabida azabar zafin da takeji a cikin.

“Ya isa haka kowa yazo ya fita, kubar min yarinya ta ni yanzu na yadda cewar k’arama ‘yar lado ce dan….” Ai basu bari ya k’arasa ba suka fara mai tufin Allah tsine inno sai sharar kwallah take domin cin zarafin yayi yawa Mai-tafasa tace, “Aradun Allah Ard’o yau ko kaine Mai-unguwa kace ka yadda k’arama jikar kace sai inda Allah ya barmu bare k’arama mayya ce tacinye min lado lokacin da nake murnar ladona ya warke, yau kama sai k’arama ta bakunci lahira…”

Nufar d’akin suka yi baki d’aya mutanan gurin, kafin kace me sun fito da Umma dake makure da k’arama a jikinta idanun Hafsatuwalle sunyi luhu-luhu sunyi jawur sabida azabar kuka da tashi amma na k’arama a suye sai wani kallon jummai take tana zaro manyan idanuwanta kafin ta tuntsire da dariya tamkar mahaukaciya sabuwar kamu tace “Ard’o kaga inna jummai yau da farau-farau d’in Tanimu tayi karin kumallo ana bashi ta karbe mai idan nayi karya ta bari a bud’e cikin agani…”

‘Lahh kaji min shegiyar yarinya nima cinyeni take son yi dama tun data farka yau take kawo min hari Ashe dana fita karfi ne taje tacinye lado shine bata koshi ba take son had’awa dani yanzu na Shiga uku ni jummai Maman Gaddafi…” Mutane suka yi kan k’arama Ard’o da inno suka yi saurin karewa yayin da Umma ke durkushe a gurin ta rik’e cikinta da hannuta lokacin lauratu ta fito bayan ta gano shigowar sallau…..,

《》 《》《》《》

“Madre wallahi ni yanzu ban iya yin komai babyn nan yana wahalar dani amma Yaya Ma’ar yayi ta cewa bana kaza bana kaza, kuma nace ki samo min me aiki Madre kinki ni yanzu ya zanyi.. ! gashi kasala ta kuma yi min yawa.” Sumayya ta fad’a tana daga jikin Madre dake rik’e da mediceted glass d’in ta, cikin kulawa da nuna tattali Madre tace.

“Sorry Sumayya na fara bin cika miki, wadda aka samu d’in tana son yi amma ‘yata na kwance ba lafiya amma nasa a kuma binciko miki wata me aikin nima ai at this stage zanso ki samu mai temaka miki da wasu abubuwan.” Cikin sauri Sumayya ta kalli Madre tare da cewa.

“Yauwa Madre na! Toh yaushe za’a samo? Dan Summay yanzu bata aikin uban komai hatta wanke pant vest, da bra duk ta dena. Madre tayj murmushi tare da fad’in.

“Sai randa aka samu amma nace karya wuce cikin week d’in nan.” Lokacin Ma’aruf ya shigo cikin gayun shi, wankan suit yayi white color yayi bala’in yin kyau ya k’arasa ciki tare da gaishe da Madre dake kallon shi cikin mamaki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button