ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ma’aruf ina zuwa kuma haka…?!”
Sai daya sauke numfashi sannan ba tare da ya kalli inda suke ba yace “zan je na gano mutumin nan, ina son na tabbatar da ya samu komai hatta sana’ar da zai iya yana daga zaune so flate d’in 2:00pm zan bi.” Ya fad’a tare da juyawa zai fita Madre na mishi addu’ar dawowa ita kuma Summaya tayi saurin bin bayanshi. A k’afar fita suka had’a ta matseshi ta baya tare da kissing d’in wuyan shi cikin shauk’i dan ba k’aramin kyau yayi mata ba har wani masifaffan kishi da sha’awar shi suka dirar mata at once.
“Sweetheart please kaje dani.” Ta fad’a tana shafar wuyan shi, kallon mamaki yayi mata tare da kallon cikin jikin ta, a zuciyar shi addu’a yake Allah yasa kar babyn shi ya kwaso d’abi’un ta a fili kuma ya janyeta a jikin shi tare da shafar gefen fuskarta yace.
“Bye take care.”
Da sauri ya shiga mota driver yaja suka fita yana jimamin halayyan sumayya da be san haka take ba sai bayan sunyi aure.
Yana sauka garin katsina aka had’a shi da guide sai focal person d’in shi suka nufi gwadabniya kauyan su malan lado, tun da suka fara dosar kauyan basu ga mutun ko d’aya ba hakan ya bawa Ma’aruf mamaki sai yaji duk babu dad’i yau ba’a biyo suba har suka je k’ofar gidan. Focal person d’in ya shiga cikin gidan amma tsit hakan yasa shi nufar d’akin da yasan lado na kwance amma shima ba kowa hakan ta dawo ya sanarwa da Ma’aruf, “what did you said? Toh ina suka tafi baki d’ayan garin? Oh my God… !.” Ma’aruf ya furta cikin mamaki.
“Mu k’arasa fadar Mai-unguwa wata kila mu asamu bayani.” Cewar focal person d’in yana kallon Ma’aruf dake ta faman shafar kyakyawan quarter million d’in fuskar shi “ok.” Ya fad’a tare da shiga cikin motar suka wuce kauyan su Hafsatuwalle mamaki fal zuciyar shi.
《》 《》《》《》
Da sauri ya k’arasa gurin ta yana tambayar “lauratuna lafiya kuwa? Kama hannuta yayi suka k’arasa gurin mutanan ko wanne da makami a hannunshi can ya hangi Mai-tafasa ga inno da Ard’o suna kare k’arama da Ummanta shima ya k’arasa gurin yana bada hakuri duk da cewar besan meke faruwa ba.
“Wallahi yau sai k’arama ta bi lado ba zasu sake kwana cikin gidan nan ba.” Mai-tafasa ta fad’a tana kuka tamkar an mareta yayin da su jummai ma ke ta fad’a cikin karayar muyar inno tace.
“Kuyi hakuri indai k’arama ce da Hafsatuwalle zasu bar muku garin amma karku d’auki mataki akan kashe k’arama….”
“Su tashi subar gidan toh kafin mu kaddamar musu.” Ard’o ya kalli inno yaga sai kuka take lallai yau yazama dole su Hafsatuwallen shi su bar garin idan ba haka ba aiyi musu aika aika ya juya yaga Umma sunkuye lauratu ta rik’o ta sai kuka suke yayin da k’arama ke zaune tana kwakular kasar gurin. A gaba suka tasa su mutane jingim Umma ta rik’e da k’arama sai tirjewa take yi akan sai ta saketa taje ta rama dukan da Mai-tafasa tayiwa Umma lauratu sai kuka take ganin ana korar su da jifa da zage-zage har suka baro gidan suka nufi hanyar barin garin.
Jibgegiyar motar data doso ce ta sa suka tsaya tare da bin motar da kallo, gaban su ta karaso focal person yayi saurin mod’ewa Ma’aruf kofar ya fito cikin nutsuwa tare da karewa mutanan gurin kallo ciki harda Mai-unguwa da shima ya k’araso gurin ba jimawa, wani banzan kallo yake aikawa da Mai-ungawa wadda yasa shi muzurai da idanuwa………..,
FEEDOHM????
&
HAJJA CE????
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》
????????
????
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????
SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
Page *53-54*
Kusa da Hafsuwalle ya k’arasa ganin jini a fuskarta a hankali ya tambayeta “Me ke faruwa anan?……Saboda ya lura ita kadae ke da sauran hankali a gurin ……
Sunkuyar da kai tayi ba tare da tace komae ba sae kukan dake fita a hankali mai cin rai!Mai ungua ya k’araso kusa dashi yana fad’in “Ranka ya dade wallahi yanzu na k’araso na tarad da wannan hargitsin……”
Kallo d’aya ya mashi ya watsar ya kuma tambayar Hafsuwalle me ke faruwa……K’arama ta ba shi amsa da “Wasan jifa suke da mutuwa shine Maitafasa ta jefe Ummana……”tare da saka hannu a aljihunshi ta fito da katuwar wayarshi da ta lek’o……
Maitafasa tace “Bani guri buwalle na karashe shegen wasan jifan da tace anayi akan shedaniyar yarinyar can……!
Wani sakaran kallo ya watsa! kafin yayi magana Mai’ungua ya ce “Yallabai rigima suke akan wannan yarinyar da kake gani!Da farkon fari yarinyar Shegiyace!Sannan Mayya ce!A Kakkabe a kare d’azu ta lashe kurwar Ubanta mutumin nan Malan Lado da ku ka san da zamanshi a fad’in kauyennan……”
Dafe kanshi yayi yana maimata Inna lillahi wa inna ilahir raju’un!Idan ya fahimci maganar Mai ungua Malan lado ya rasu kenan!Mai tafasa ta katse mashi hanzari ta hanyar watsa mashi tafin hannunta a saman fuskarshi tana fad’in ” Bani guri Bature !Ni maitafasa bana daukar iskanci aradun Allah!Kai din wofi baka isa ka hanani daukar mataki ba!Da k’warank’watsa Tunda har ta lashe man Lado to kai din banza baka isa ka hanani kasheta ……”
Wawan Marin da ya zuba mata ya katse sauran Maganarta !Yayin da tayi baya ta hantsila ta fad’a jikin Kundum……Ji kake Tumm Kundum ta janye jikinta cikin mugunta tana cije baki……
A fusace ya kalli Mai ungua yace “Ku iskeni gidan Hakimi yanzu!Sannan ya karbi wayarshi dake hannu K’arama ya kalli Hafsuwalle yace “Shiga mu je……”
Babu Musu ta ja hannu K’arama guard ta bud’e mata motar suka shiga da kyar aka tada motar……
Inno kam Juyawa tayi gurin Ard’o cikin kuka tace “Ka gaza a matsayinka na maihafin Hafsatu Ard’o!ka gaza gurin kula da hakkin da ya rataya a wuyanka,shin kana da wani abu da zaka fad’awa ubangijin da ya baka Hafsatu na banzatar da rayuwarta da kayi? ko kana tunanin Allah bara ya tambayeka akan digon hawayen Hafsuwalle bane!Baka yarda da tarbiyyar diyarka bace ?ko ko Hafsatu ba jininka bace da ka wofintar da ita a idon duniya!Duk abunda ya samu Hafsuwalle ka raba biyu ka dauki kaso daya Ard’o kaine sila da ka kasa warware komae……!A Hankali ta juya ta kama hannun Lauratu suka shige gida……Ard’o kam tsaye yayi ya kasa koda motsi……
Kallo d’aya zaka ma Mai’ungua ka gane yana cikin rud’u a sukwane ya kalli Mai tafasa yace “Shi kenan kun janyo mana bala’i Maitafasa!Aradun Allah kafin kice komae a gaban Hakimi sae kinsha tsumagiyar dukan da kikayi masu…”
Cikin sauri tace “Ni kam na yafe Ladona!Mai ungua kaje kace masu suyi hakuri wallahi na tuba!Ni shegiya inje gaban hakimi inci ubana……”
Kundum ta taba hannu tana fad’in”A A Maitafasa ke da kike neman kudin zuwa birni k’arar Hafsuwalle! Yau kuma kin samu dama ki ce bara ki je ba……”
Kukan kura tayi ta cakumi Kundum tana fad’in”Na Dade da sanin ke bakar munafuka ce dama Kundum!Gidan Uban wa nace maki ina son kai hafsuwalle birni k’ara?
Kundum ma cakumar Maitafasa tayi suka kaure da nusar cikin juna yayin da yan garin ke fad’in”Gaskia Kundum ke ce baki da gaskia Yarda Maitafasa ta shiga wannan bala’in kuma ki kawo mata wata maganar……”
Sakin Kundum din tayi ta watsawa mai maganar harara tace “Dalla gafara munafukai!Ba har daku aka dakesu ba……”
“Da k’warank’watsa babu ruwana……”Cewar Bulawale yayin da ta tafi buguzum buguzum ta nufi hanyar komawa kauyensu ……Kafin kyaftawar ido matan garin duk sun sab’e an bar Maitafasa da Ard’o sae Mai unguwa dake tsaye kamar sakarae……