ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sae da Mai’ungua yawa Maitafasa jan Ido sannan ta yarda suka hawo mashin d’aya suka nufi birni yayin da Ard’o ya samu mai mashin shima ya bisu……
Gidan Hakimi suka nufa acan suka iske Hafsuwalle da K’arama zaune cikin fada ……
Guri suka samu suka rakub’e kafin Hakimi ya shigo!Maitafasa ta rarrafa kusa da hafsuwalle tace “Hafsuwalle baki ji kunyar zama shari’a da ni Maitafasa ba?Haba Hafsuwalle tuno lokacin da kike Amaryar Ladona!Ni ce Zabbi!Ni ce Fura!Ni ce manshanu!Haba Hafsuwalle mu sasanta tun kafin naji tsumagiya a gadon bayana……”
Karaf K’arama tace”Idan ta tuna lokacin da kika kwala mata k’ota fa……”
Kafin tayi Magana Hakimi ya shigo tare da Ma’aruf suka zauna dae dae lokacin da Ard’o shima ya shigo ya zube ya kwashi gaisuwa sannan ya kuma ya rakub’e a bango!Maitafasa kam banda mazurai da soshe soshen karya babu abunda take !
Mai ungua aka nema yayi bayani !Da kyar ya bayar da labarin tun daga farkon rikicin har karshe sae kame kame yake shima yanayi Maifasa na fad’in “Wutarka daban dake Mai unguwa” “Yaushe nace K’arama ta cinye Lado……?ko kuma tace” Allah ya had’a Munafuki da warin kabari……”
Sae da dogari ya kwatsa mata tsawa sannan ta kama bakinta……
Hakimi ya tambayi “Wanene Uban Marigayin?
Mai unguwa yace “Mahaifinshi ya rasu sae dae nine matsayin Ubanshi ranka ya dad’e……”
Hakimi ya kallesu d’aya bayan d’aya yace”Wacece Uwar marigayin?
Zumbur Maitafasa ta mike tana fad’in “Gani anan Ranka ya dade!Matsowa zanyi ne koko kai zaka matso yarda zaka ganeni……”Mai ungua ya janyota ta zauna ……
Hakimi yace “Ina Mahaifin Hafsatu?
Ard’o ya kalli Hakimin sae dae bakinshi ya masa nauyin amsa sunan Mahaifinta!Shi Hafsuwallen ta kalla hawaye na zuba a idonta ta nunashi da hannu……
A Hankali yace “Nine Mahaifinta kafin na zubar da k’imata saboda zancen mutane……”
Tambayar Maitafasa akayi ko gaskia Mai ungua ya fad’a amma ta karyata rabi da kwatar zancenshi !illa iyaka ta yarda da cewa K’arama ba jikarta ba ce !
Hafsuwalle kam iyakar gaskiyarta ta fad’a cewa K’arama diyar Ladoce !Shi kanshi Hakimin baya da hujjar da zai karbi zancen Hafsuwallen ko na Maitafasa……
Ma’aruf kam shiru yayi yana jin dramarsu yayin da yake Kallan K’arama dake harkan gabanta har da su dariya!Sae da taji Maitafasa na fad’in “Da kwarankwatsa ta fad’o mata yanzu bata ce K’arama ta cinye lado ba……”
Sannan ta kwasa da gudu ta fad’a gidan Hakimin tana fad’in “Aiko zata fad’o maki yanzu……”
A Cikin gidan ne ta kalli cikin matar Hakimi ta kece da dariya tana fad’in “Yan birni harda ganyen ciyawa suke ci……”
Daga farkon Matar Hakimin banza ta mata Sae da K’aramar ya janyo hannunta tana fad’in”Baku da tuwo ne kika ci ganye da wake?
Harara ta watsa mata don ta saba ganin y’an kauye irin haka……Ita kam K’arama binta tayi har kitchen tana fad’in”Jiya kinci Nama da Ankaha yau kuma kinci Ganye da wake shin baku da tuwone ku?Ga yan cikinki duk sun harde guri guda……!
Matar Hakimi ta kwala ihu yayin da dogari ya shigo da sauri ta fad’a mashi abunda ya faru ya kuwa kama K’arama da kyar ya maidata fada ya fad’awa Hakimi abunda tace ……
Nanne Maitafasa ta rafka gud’a tace “Ahayye yanzu kam na amsa Nace Mayya ce tunda har tayi ma Matarka……”ta karashe maganar tare da watsa Hannu……
Hakimi cewa yayi shirman yara ne a kyaleta amma Maitafasa tayi karab tace “K’arama meye a Cikin Hakimi……”
Cikin rashin Damuwa ta kalli tukeken cikinshi tace ” Ni dae wake na gani da wani abu kamar tuwo amma ba tuwo bane……!Aikam Hakimi ya fara mazurai tare da kare cikinshi da hannu ……
K’arama ta kalli Maitafasa ta kwashe dariya harda tab’a hannu tace”Ke kam Maitafasa banda Tafasa da Zawo a gefe babu abunda nagani……!
Dariya Ma’aruf ya sake mai sauti ganin abun yake kamar shirme sae da juyo tace mashi “Kaine kad’ae kasha Madarar shanu!
Kafe ta da ido yayi !Hakimi kam cewa yayi a kira sarkin Mayu yanzu !Cikin mintina kadan Sarkin Mayu ya iso akace ya dubata ko Mayya ce……Duk binciken da yayi ya tabbatar masu da babu Maita illa iyaka Aljanu suka bude mata ido!
Cikin Hikima Hakimi ya neme ya masu sasanci su koma gida sanna yayi wa Ard’o magana akan banzatar da ita da yayi ya nuna masu koda ace K’arama ba diya Lado bace bai kamata su mata haka ba balle Hafsuwalle da auren sannan tsakanin Miji da mata sae Allah!Kuma yanzu babu wanda ya isa ya warware wannan matsalar sae Ubangiji su tafi Allah zai fito da ABUNDA KE B’OYE Sannan Maganar K’arama Mayyace bata taso ba tunda ance Aljanune shi yayi alkawari zai sama mata magani har ta warke ……Maganar sakin da Maitafasa tayi wa Hafsuwalle bata taso ba tunda ba Lado ya saketa ba !ta koma gida tayi wa mijinta ta kaba……
Maitafasa kam datsewa tayi ta fara yayyafa ruwan tijara wae karyane kawae ana so arufe maganar ne ita kam ta rigaya ta saki Hafsuwalle kuma bata da gadon Ladonta!K’arama mayya ce kuma yanzu ta ce ita ta cinye mata Lado babu wasu aljanu don haka dole a bi mata Hakkinta!Sam ta manta gaban Hakimi take yayin da take watsa hannu tana mayarwa tare da girgiza kai……
Sae da Hakimi yace a mata bulala Goma sannan tayi shiru tana zare ido !Tana ganin za’a daketa ta tuno da lokacin da akayi k’arar Dan gidan Mati a kauyensu gurin mai unguwa……Yaron ya dage yawa Mai unguwa dukan tsiya akace aljanune……Don haka ta saki duwawu ta fara banka Tusa da harba kafafu tana d’aga hannu sama……
HAJJA CE????
&
FEEDOHM????
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》
????????
????
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????
SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
Page *57-58*
Maitafasa Kam da yake machine daya suka hawo da Mai'ungua tunda suka taho take ta ruwan bala'i kamar shi ya daketa……Munafuki kam da yana tsiru da ya fito a goshinshi!sae da suka shigo daji sossae sannan tayi wani uban juyi ta tik'oshi kasa!Mai machine ya yi niyyar tsaya tace "Bar shege hannun nashi a bujena yana lalubata kuma ba miji na bane!
Mai machine ya gyad’a kai yace “Allah ya kyauta ai wasu mazan yan iska ne”
Banza ta mashi tare da gantsare baya tana cije baki!Yayin da ta kullafi dukkan mutanen kauyen!kuma tasha ALWASHIN duk shegen da take bi bashi sae ya biyata yau ko da kuwa uwarsa zai saida……!Sannan gaba da Hafsuwalle kam yanzu ta fara tunda sanadinta ne aka kai birni aka daketa……
A Haka har Mai machine ya shigo kauyen ya tambayeta inda zaya ajeta ta nuna mashi kofar gidan mai ungua da hannu!Tana sauka ta kama hanya zata shiga gida……
“Inna kud’in fa?mai machine ya tambaya……
Hannu ta watsa tana fad’in “Kai yaro ba wani Inna!sunana Hansai……Idan na shiga zan turo yaro ya kawo maka!idan na manta kuma ka turo yaro kace Hansai ta baka kudin babur d’inka……”
Gyad’a kai mai machine yayi !Yayin da tashige abunta tana watsa hannu !ta wani sird’ad’e dake gefen zauren gidan ta fita daga gidan ba tare da ta shiga ciki ba!ta sulale ta nufi gidanta……
Tsakar gida ta iske kundum na surfe !kallo daya ta mata ta watsar ta rafka gud’a tana fad’in “Ayyiriri!Bakaken munafukai masu hakuran shanu ga Mai tafasa ta dawo da ranta!
Dariya Kundum ta saki itama ta rafka shewa tana fad’in” Ahayye!Maraba da Maitafasa ga ruwan zafi can a gasa duwawu……”
Tab’a hannu tayi da niyar watsawa a fuskar Kundum!tayi saurin janyewa da ta tuna marin da watsa hannun ya ja mata!lokaci guda ta saki tsaki tana fad’in “Yo Ruwan zafi haihuwa nayi algunguma?
“Ko baki haihu ba jamammun idanunki sun nuna kinsha dan banzan duka Mai tafasa……”Cewar Kundum tare da tilla tabarya sama ta cabke tana dariya……
“Sakarai ake duka a zauna lahiya Kundum!Mai tafasa kam tafi karfin bugu a birni!sae dae buga in buga!Yo banda lalataccen mai mashin da ya turbude ni k’asa ai wallahi da baki ga walle na ba har ki ce duka na akayi……” Mai tafasar ta fad’a tayi gurin Bukkarta……Kundum kam shewa ta dauka kamar babu gobe! Don ta san shegiyar karyar Mai tafasa……