ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Mai machine kam yayi tsayuwar kusan rabin awa sannan ya taka da kanshi ya leka ya kwad’a sallama!Wani yaro ya leko yana tambayar wanene……Yace “Je kace Hansai ta bayar da kudin mana”

Yaro ya koma ya fad’awa Hansai dake cikin garka tana shara!Ta rafka uwar ashar ta fito daure da daurin kirji ta tsaya gaban mai machine ta gantsaro kirji tana fad’in”Kace Hansai ta maka me?

“Kud’in machine” ya fada a taikaice……
“Gidan uban wa na hawo maka babur……? ta tambaya had’e da turo kallabi gaban goshi……

Da yake yana da sauran hankali yace “Kiyi hakuri bake ba Inna !wadda ta shigo d’azu nake nufi……”

Yayyafa ruwan tijara ta fara tana watsa hannu !ganin zata tara mashi mutane ya sashi jan machine dinshi ya fita tare da Allah wadaran da halin mutanen garin……

A Hanya ya gamu da Mai ungua yana tsayar dashi amma ya watsar ya zagayeshi ya tafi abunshi!Shi kam baya tunanin zai kuma zuwa wannan sakaran kauyen har abada……

Hafsuwalle Kam mashi na suka hawo kowa da nashi ita da Ard’o har kofar gidansu sannan Ard’on ya biya kudin suka shiga ciki!Sababbun suna tsaitsaye tsakar gida suna jiran bayani……
“An kasheta……” Cewar Zulai tare da tab’a hannu sama……

Banza Ard’o yayi mata sannan ya aiki Jummai ta kira Inno dake dakin Lauratu tana bata baki!A tare suka fito da lauratun yayin da tayi gurin Hafsuwalle tana tambayarta ina K’arama……

Kamar daga sama taji Ard’o na fad’in “Tana birni Lauratu”

A Rude take tambayar me yasa aka barota……Ard’on ya tsaya ya masu bayani sossae akan abunda ya faru !sannan ya fada masu K’arama ba mayya bace aljanu suka shafeta sannan ya fada masu tana can za’a nema mata magani!Wasu matan sun yarda da zancenshi yayin da tsirarru daga gidan suka karkade kunnuwa alamun karya ne!

Daga karshe ya masu gargadi da kakkausan murya akan Hafsuwalle tare da tatabbatar da rayuwa mai iganci a gidan ubanta……
Zulai kasa hakuri tayi tace “Shin Ard’o ya batun yake waye uban K’arama ko har yanzu Hafsuwallen bata fad’a ba”

“Ni ne Uban K’arama daga rana irin ta yau……”Cewar Sallau da ya shigo lokacin……

Duka yan gidan suka juya suna kallonshi yayin da Ard’o ya gyada kai ya wucesu ya nufi gurin Hafsuwalle dake tsaye ta sadda kai ……Hannunta ya kama ya kaita har bakin Bukkar Inno yana fad’in “Kiyi rayuwa mai inganci diyata !Ni Ard’o na kaunaceki Hafsatu……!

Zulai kam kusa da Jummai ta matsa tana fad’in “Ko dae Sallau ne Uban K’arama na gaskia!

Murya k’asa k’asa Jummai tace “Wa ya sanar masu!

Baraka ta amshe “Haba ki duba yatsun kafafunsu kusan iri daya dana sallau fa!
Ba haggun salati suka rafka baki daya tare da rufe bakunansu ganin hankalin su Sallau ya dawo gurinsu ……
Sannan suka rankaya suka nufi bukkar Zulai baki d’ayansu……

《》《》《》

Beebah na fita Sumayya ta dauki maganin ta nufi Toilet tana juyi!Na goran ta zuba kadan a buta tana fad’in “Bara nayi tsarkin sae nayi inserting wancen anjima na k’ara tsakin idan na zo zan cire……”

Hanci ta kai ta sunsuna ta yatsina fuska jin warin daddawa “Dan bauchi……”ta fad’a tare da juyi tana ware hannaye……

Duk’awa tayi tana tsarki hankali kwance sannan ta gutsuri curin kad’an ta saka ta mike!Rufe ido tayi gam jin kamar tayi tsarki da ruwan barkono……
Karamin tsaki ta saki ta fita daga toilet din ta zauna baki gado har lokacin tana jin zafin na karuwa!Tun tana daurewa daga zaune har ta kai ga mikewa tsaye ta fara tsalle……Itakam bata jin zata iya cirewa don so take Ma’aruf ya jita kamar sabuwar Amarya……
Cikin kankanin lokaci idonta yayi jawur ta mike ta kunna AC da fanka ta cire zaninta ta bude kafafu iska na shiga wae ko ta rage zafin……
Kasa daurewa tayi ta fashe da kuka hadi da kiran number Beebah!ringing din farko beebah ta dauka tana fad’in”Yadae Sumy?

Cikin kuka tace “Wallahi Beeba nayi inserting wannan abun sai shegen zafi!zan iya fidda wa yanzu tunda ya dade……”

Murmushin mugunta ta saki tace “Haba Sumy!dama magani mai kyau a dole yayi zafi!ki daure ki bari sae anjima sannan……”

K’ara fashewa da kuka tayi tace “Wallahi kamar na saka pepper aciki Beebah……”

Tabe baki tayi tana wani sakaran murmushi tace “Da Farincikn ki k’ara na mijinka Sumy ki daure !dama kin san duk magani mai amfani dole yayi zafi……”

Shiru tayi ta katse wayar!a hankali take kuka tana mirgina saman rug d’in tare da tura hannunta cikin pant!ganin abun bana wasa bane ta mike da gudu ta nufi toilet tana kuka har da majina zata cire taga duk ya nake a ciki!kad’an kad’an ta fara fitar wa sannan fad’a cikin ruwan sanyi ta zauna sauran ya cigaba da biyo ruwan yana fitowa……

Tafi awa daya cikin ruwan sannan ta fito ta daura towel ta rashe tsakar dakin ta ware kafafu iska na shigarta……

Wajen karfe 7:46pm taji Mai gadi na bude gate ta mike tana share hawaye!kamar mara lafiya take taka kafafunta saboda azabar zafi……riga ta saka doguwa ta fita falon tana jiranshi……

Da Sallama ya shigo d’auke da K’arama a kafad’a ta tayi bacci!Waro ido tayi tana fad’in “Ya Ma’aruf me yasa ka dauko Ihsan dan Allah……”

Shiru ya mata ya kwantar da K’arama bisa kujera sannan ya kalleta ya kalli K’arama dake minshari yace “Ba Ihsan bace……”

Ware ido tayi sossae tana kallon K’arama sannan ta kece da dariya tace “Ina ka samo wannan abun haka?Lallae Ya Ma’aruf rufe maka ido akayi ka dauko wannan dattin a kafadarka……”

“Huh……” ya fada sannan ya zauna yana fito da wayarshi……

“Ka man magana man ina ka samota?

“Kauyensu……” ya fada lokacin da yayi dialing number Madre

“Wannan ai barata iya wani aiki ba Ya Ma’aruf gaskia a canzo wata……”ta fad’a cikin salon shagwab’a

“Na Sani” ya fad’a a takaice……

Zata sake magana taji yana gayar da Madre cikin waya!tare da fad’a mata ya dawo kuma dauko wata yarinya amma gobe zai zo ya mata bayani……

Bata san me Madre d tace ba sae dae taga yayi murmushi tare da yanke wayar……
Harara ta watsa mashi tana fad’in “Kaman bayani mana inda ka samo wannan yarinya tunda kace ba yar aiki bace ……”

Cikin sanyin Murya yace “Wae Sumayya baki iya tarbar miji bane?Na dawo ba tambayar ya hanya!ba ruwa amma kin sani gaba sae maganganu kike?

Zunbura baki tayi ta nufi kitchen ta hado mashi tea ta d’auko bread ta zo ta aje gabanshi……Ware Ido yayi yana kallon Tea da bread din sanasn ya daga ido ya kalleta ya mayar da idonshi ga K’arama dake ta jan minshira ya mike “Ko ni Maye ne Baran ci wannan abun ba Sumayya……”

Kamar yayi kuka ya sake fita ya bawa maigadi kudi yace yaje gidan Madre ya karbo mashi abinci……sannan ya dawo ya hade kai da guiwa kamar k’aramin yaro!

Ita kanta ta san batayi dae dae ba ta matsa tare da dafa bayanshi tace “Dan Allah kayi hakuri wallahi babynka ya hanani shiga kitchen da na mike sae naji kamar zai fad’o……”

Bai ce mata komae ba haka bai d’ago ba!kwantar da kanta tayi jikinshi tace “Am sorry dear!Amma dan Allah ka fad’a man inda ka samo wannan yarinyar……”

Yasan tana da hakk’in ya fad’a mata don haka ya dago a hankali yace “Mahaifinta ya rasu bata da lafiya shine na taho da ita na nema mata magani……”

A Hankali tace “Amma duk kauyensu aka rasa mai daukarta sae kai……!me ke damunta……?

 Ya san surutu irin na Sumayya dan haka yace "Tana da kidney problem……"

Harara ta watsa mashi tace “Dole ta dinga man aiki kam don yanzu ba’a zaman banza kafin ta tafi……”

“Huh……” kawae ya fada sannan ya mike jin sallamar maigadin!ya fita ya karb’o sakon ya dawo……
Mikewa tayi ta dauko plate Alkubus ne da miyar k’oda …… ta zauna ta zuba mashi suka fara ci a tare sae da ya koshi sannan ya matsa kusa da K’arama ya kira sunanta a hankali……
Shiru yaji sae uban minsharin da take sha ……
“Hafsah……” ya kira yafi sau goma amma ko juyi batayi ba !Sumayya ta kwashe da dariya tana fad’in “Waya fada maka haka ake tada mutun bacci a kauye!bara ka gani……”
Kafin ya bata amsa ji kake tassss a kumatun K’arama……
ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button