ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

               ????????
                  ????

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????

SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu

This Chappy is for you FATIMA OMAR FAROUK……ILYSM

   Page *59-60*


A Zabure ta wulkita ta fad'o kasa tana zare idanu kafin ta turo baki tana fadin "Waya mareni?

“Babu……” Ma’aruf ya fada a takaice……

Sulalowa tayi tana k’arewa Falon kallon sannan ta mami Sumayya ta kwalfa mata mari ta nufi bayan kujera tana fad’in “Na Rama……”

Zafin ya shigeta sosaae ta dafe check dinta tana kallon Ma’aruf din da yayi mutuwar zaune !ganin baya da niyar magana ya sata zabura zata mike tana fad’in “Wallahi sae naci uwarki kuma kin daki zamanki a gidan nan……” yayi saurin janyota jikinshi ya rungume yana kokarin danne dariyarshi……

Fashewa tayi da kuka tana fad’in “Ni ka kyaleni!a gabanka fa ta mareni idan kai baraka rama man ba ka barni na rama……”

Murmushi yayi mai sauti yace “A gabana kika mareta itama……”

Ta sake fashewa da kuka tana kokarin kwace jikinta” Haka ka ce ko?ka fi sonta a kaina ko?to wallahi sae na daketa……”

“Aljanu gareta……” ya fada cikin whisper
Waro ido tayi tare da lafewa jikinshi ta kasa motsi……
“Kina dukanta zasu rama mata tsakar dare!ya fad’a cikin dakewa……
A Hankali tace ” Amma wallahi bata zama yau zaka mayar da ita……”

A Hankali yace ” Duk inda ta shiga bata fita Sumayya”

“Saboda me……”
Dago kanta yayi yace “Aljanunta ke mak’alewa gidan basu tafiya su dinga bawa yan gidan tsoro karshe ma su kashe auren mutanen gidan……Ki bari zata baki hakuri kuma zan fad’a mata matata ce karta kuma tab’aki!Amma kema ba ruwanki da ita……”

Shiru tayi tana raba ido ……
Murmushi yayi ya kira ” Hafsah……”
Amma shiru kake ji !Janyeta yayi ya leka a hankali bayan kujeran !ya tarad da sakaran sheme bacci ya kwasheta……dama bata gama baccin ba sumayyan ta tada ita……

Komawa yayi ya lallab’a Sumayya ta yarda ya kai K’arama dakinta ya kwantar sannan suka koma dakinshi……

Wanka ya shiga ya fito ya kabbara sallah sannan itama ta dauki goran ruwan da ta rage ta shiga toilet!ta dade tana tuna azabar da taji yayin da wani bangaren na zuciyarta fad’a mata “Curin ke da zafi……”
Haka ta shahada ta tsiyaya tayi tsarki dashi……
Tun kafin ta mike ta fara jin zafi !ta taka a hankali ta fita d’aure da towel ta haye gado ta kwanta tana cije baki……

Sae da gama sallah sannan ya mike ya fita ya leka d’akin da K’arama ke ciki ya mata addu’a ya rufeta da bargo sannan ya dawo gurin gimbiyar……

Kamar kullun ita ta koma kamar mijin ta janyoshi tana kissing dinshi tare da shafa shi!Cikin kankanin lokaci zafin barkonon dake cikin abunda tayi amfani dashi ya fara shafarshi!kamar yarda yake damunta!maimakon suyi enjoying sae ya koma tana kukan azaba yayin da ya janye ya kwanta gefenta idanunshi sun kad’a sunyi jawur……

A Hankali yace “Me kikayi amfani dashi?

Cikin kuka tace “Babu komae……”

Mikewa yayi ya fincikota zaune yana kallonta!A Tsawance yace “Uban me kika saka a jikinki……”

“Wallahi babu komae yau kuma ni’imar ce tazo da zafi……! bata rufe baki ba ya tsinka mata mari ……

“Ki fada man uban me kikayi amfani dashi da kike son cutar damu……”ya fad’a a tsawance……

Kuka ta saki da karfi tare da dafe inda ya mareta!Kukan ya janyo hankalin K’arama dake ta shawagi cikin falon ta nufo kofar da taji kukan na fitowa ta daddage ta tura da karfin bala’in !da yake ba rufe take ba ta fad’a tsakar d’akin timmm……
Da sauri Ma’aruf ya janyo bargo ya rufe jikinshi tare da kunna lamp yana kallonta……

Tsawa ya daka mata hade da tambayarta “Menene……?

Kallon d’aki take baki bud’e sannan tace “Kuka naji shine ya shigo na ji menene?

“Menene……?ya maimaita a hankali yana kallonta had’i da girgiza kai……

Kai tsaye tace “Eh……Idan fad’a kuke na rabaku mana……!

Takaici ya kashe Sumayya tace “A Hakan dan Ubanki zaki shigo ki ji Menene?to Ubanki ne……”

Kallon Sumayya tayi na yan mintina sannan tace “Uhmm Fad’an daddawa kuke ko?Kayi hakuri kaga ita bata san me ke cikin jarkar ba kawae ta kama ta wanke kashinta……Hala warin daddawar ka ji ?

Zabura tayi zata mike ta koma ta kwanta saboda har lokacin azabar bata saketa ba!

“Get out……” ya fada a hankali yana kallon K’arama……

Ita kam K’arama tunaninta da Sumayya yake sae ta kalleta tace “Yace ki d’auko ya gani……”

Nunata yayi yace “Da ke nake Get out……!

Ware hannuwa tayi tana fad’in “Ohon maka……”

Tsaki yayi yace “Fita anan!

Ta turo baki tace “Yunwa nake ji!a kauyenmu sau Uku yaya lauratu da Umma ke bani abinci……”

A Hankali yace “Fita ki jira bakin kofa ina zuwa……” A Hankali ta fita ta tsaya jikin bango tana tab’a hannuwa……

Sumayya ya kalla fuska a daure yace ” Ki fiddo man abunda kika yi amfani dashi kafin na fito……”Ya mike ya saka jallabiya ya fita !ba tare da ya mata magana ba kunna filitan falon ya shiga kitchen ya debo mata abinci a plate ya dawo ya tura mata a gabanta……

Ta ture spoon din ta fara cin alkubus d miyar koda tana yatsina fuska !loma daya tayi zuwa biyu ta ture plate din tana fad’in “Bana cin wannan tuwon nafi son irin na garinmu……”

Banza mata ta kura mashi ido tana jiran yayi magana!ganin ba kulata zayayi ba ya sata mikewa ta matsa kusa dashi……

“Kai……”ta fad’a tana tabashi……
“Uncle……”Ya fad’a,kai tsaye……
“K’arama dae ba Bunkul ba……”ta bashi amsa……
Dafe kanshi yayi yana kallon agogon falon !Karfe biyu har da rabi na dare……mikewa yayi ya jata har d’akin Sumayya ya kwantar da ita yana fad’in “Kiyi bacci dan Allah……”

Zatayi magana ya kashe haske ya rufe dakin ta yarda barata iya bud’ewa ba ya koma gurin Sumayya……

Makure ya tarad da ita rungume da goran Maganin da roba!Harara ya watsa mata ya karb’a tare da sunsunawa……
“Wa ya kawo maki wannan?
“Dan Bauchine?ta fada kanta na kasa
“Waya kawo maki?ya daka mata tsawa……
“Beebah”……

【】

“Sallama……”
Bulawe dake d’aki ta fito tana tab’a hannu “Maitafasa yaushe aka dawo birnin……?

Harara ta watsa mata tana fadin ” Ke Buwale ba wannan ya kawoni ba……”

Tabe baki Buwale tayi tana kallon kafad’Aar Maitafasa dake dauke da sahun bulala tace ” Amma birni ba imani ashe sae da kika sha tsumagiya……”

Harara ta banka mata tace ” Bansan munafunci!Ina binki Murtala ta tafasa!sannan kinci bashin daddawa ta goma!kika amshi hura ta talatin!ga surfen da na maki na ashirin!tattaro ki bani kudina……”

Kwantar da Murya Buwale tayi tana watsa hannu “Yanzu Maitafasa ina zan zamo wad’annan kud’in na biyaki……”

Maitafasa ta watsa hannu baya tana fad’in “Da kwarankwasa duk inda zaki samo ki samo kafin na sake zagayowa……”

Tana fita ta shigd gidan dake gaba !Suma can lissafin tsofaffin bashin da takd bi tayi!Sannan ta fita tana watsa hannu……Duk wanda tasan tana bi tsohon bashi garin sae ta mashi sallama ……

Sannan ta dawo tun daga farko tana bin gidajen……

Duk wanda bai bata kudinta ba sae ta kama akuyarshi ko kaza ta tafi……

【】

Cikin farinciki Lauratu ta kalli Umma tace “Umma Baturen zaya nemawa K’arama magani ta warke……”

Gyada kai tayi a hankali tana kallon Lauratun !Rabon da ta zauna sunyi fira da Lauratun har ta manta……
Kamo Hannunta tayi tace “Umma sae ta warke zaya maidota……?

Sallamar Sallau ta hana Hafsuwalld fad’in abunda tayi niyya……ta Dukar da kai cikin jin kunya!Shima Sallau din a kunyace yace”Inna Hafsatu Barka da dare……”

A kunyace ta masa da “Yauwa “Idonta na k’asa……

Lauratu ya kalla cikin so yace “Lauratu ga rake can ki dauko a dak’i ki d’ebarwa su Inno……”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button