ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

A Hankali ta mike ta fita d’aga dakin ya bita a baya!Sae da ta shiga d’akin sannan ya tare bakin kofa yana aika mata da kallo na musamman……
Juyar da kai tayi cike da kunya ta sunne kai……ya kamo hannunta ya rike cikin kwantar da murya yace” Wa yace ki fita d’azu……?
A Hankali tace “Hura na sawo gidan fulani……”
K’ura mata ido yayi yace “Ban yarda Lauratuta ta dinga fita mutane na kalle man mata ba……”
D’aga kai tayi tana kallonshi tare da gyad’a kai a hankali……
Sakin hannunta yayi ya bata hanya ta dauki raken ta fita……
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》
????????
????
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????
SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
Wannan shafin na kune dan jin dad’inku, Mai-tafasa na fushi daku sabida kuna mata dariyar tayi….., Aunty Maijidda Musa, aunty bilki,aunty Zuwaira, aunty haiba, Ummy fingers, Meenet, Mmn ihsan, Mmn Khalid, arfat lawan, precious Hindu,Meenar parrot, Rasheeda tabaco, Hayat A Idris kai gaskiya kuna da yawa masu yiwa Mai-tafasa dariya wannan kad’an kenan domin kunfi ku nawa..!!!✋
Page *61-62*
Ranar k’arama kasa komawa bacci tayi sabida kamshin da room d’in keta faman yi, zuwa tayi wajan k’ofar cikin duhu ta dinga bugawa amma tak’i bud’u ta kwanta k’asa still bataji dad’i ba tayi wajan wata k’ofa tana bud’e toilet ne shima sai kamshi yake yi nan da nan tasa kuka daga baya ta hango window sai ta fara murmushi tare da mik’ewa ta bud’e tabar d’akin.
Cikin filawas d’in gidan ta shiga tayi kwanciyar ta duk da nan d’in ma a tsaftace yake amma yawan su yasa taji d’an dama-dama sai faman surutai take yi tana tunrserewa da dariya cikin dare.
Acan d’aki kuwa Ma’aruf ne ya tsare Sumayya da bala’in shi yana cewa,
“Wallahi Sumayya baki da wayyo,ke sakarai ce shasha-sha, baki da sirri gashi nan garin haukanki kinsa ana neman kashe mu ko a illatamu. Toh bari kiji na gaya miki !, daga yau daga rana irin ta yau idan kika sake shan wani abun da cewa na ni’imane wallahi zakiga abinda zan miki sakarai kawai.”
Bakinta ta turo mai ganin sai balbala mata masifa yake yi cikin jin haushin kalaman shi tace,
“Amma Yaya duk ina yin wannan abun ne dan kaji dad’i shine kuma yanzu zaka tayi min fad’a? Wannan ma matsala aka samu amma na baya duk da nayi ai…. !“
Bakin nata ya buge da bayan hannun shi hakan ya hanata k’arasa maganar da take yi, “wa wuya kawai garin hakan zaki je ki illata d’an cikin ki? An gaya miki masu ciki suna irin wannan ciye-ciyen? Ku da yake matan hausawa bakuda yadda a haka duk sai kuyi ta illata kanku wai dan a janyo hankalin miji haka ake yi dama? Why baza ki min biyayya ba? Kiyi min girki kamar yadda Madre keyiwa Abba ba? Duk inda naje na dawo duk abinda kikeyi ki ajiyeshi kizo ki temaka min da abunda zan bukata amma duk sai na saki a hakan ma kina yi kina cewa kin gaji ko vazaki iya ba, to hakan ya isa bana so na fisonki a yadda kike natural idan kinji to idan baki jiba wallahi Sumayya you will see….”
Yana kaiwa nan ya kwanta tare da juya mata baya zuciyar shi na kona. Sumayya tana ta ture turen baki ta kwanta it am a tare da matsawa jikin shi ta ringume ta baya yana jinta tana shafar jikinshi yayi mata banza dan har lokacin be huce ba.
Tun sallar farko ya farka sannan ya shiga bathroom yayi wanka tare alwala yayi sallar nafila duk Sumayya na kwance.yana idarwa yafita dan gano k’arama amma me ! yana shiga wayam babu ita ya lek’a toilet ba kowa hankalin shi ya tashi yana mamakin ina ta shiga? Gashi kofar yadda ya rufeta haka yazo ya bud’e ya shiga uku….”
K’iran sunanta ya shiga yi da k’arfi cikin tashin hankali “Hafsa! Hafsat!! Hafsatu!!! Kina ina? Where are you?” Ya fito zuwa parlor yana dudubawa babu k’arama hankalinshi ya kuma tashi da sauri ya fita zuwa parking lot yana dubawa nan ma babu ya k’arasa wajan me gadi….,
“Am bakaga wata ‘yar yarinya ba ta fito?!”
Me gadi ya kalli Ma’aruf daya tashi hankalin shi cikin rashin fahimtar maganar tashi yace.
“Ranka ya dad’e ai na d’auka su hajiya Maryam basu zo gidan ba! Ni kam banga ‘ya’yanta ba ko d’aya a nan gidan.”
A rud’e Ma’aruf ya kalleshi tare da dafe goshin shi yace,
“No ba ‘ya’yanta nake nufi ba, yarinyar dana shigo da ita jiya da…..” Beh!, k’arasa ba suka ji tana cewa.
“Kai ina zakaje?!” Hhhhhhh “duk kunji tsolona nice fa k’alama anwan Yaya laulatu.” Tayi magana irin ta yara tana b’abb’aka musu dariya,hannunta Ma’aruf ya kama yana janta zuwa cikin parlor ya rage tsawo dai-dai nata sannan ya kama kunnanta d’aya fuskarshi a d’aure ya zare mata idanuwa yana cewa.
“Idan na sake ganin kin fita baki sanar min ba saina cire miki kunne d’aya…!”
K’arama ta kuramai danuwa tare da dashare masa baki hak’oran nan nata yalaye tamkar tasha d’orawa sannan takai hannunta d’an k’arami saman hancinshi tana shafawa tace.
“K’alya kace yi bazaka cire min kunnena ba dan naji tsolo kace akan…”
K’irjin Ma’aruf ya buga jin abinda ta fad’a, nan da nan ya fara tunanin yadda zai yi da ita sabida ba karya tayi ba ta gano abinda ke zuciyar shi ne. Cikin dakewa shima ya zare mata idanuwa tare da jan hannunta ya kai ta d’akin yace ta kwanta tayi bacci kafin ya dawo.fita yayi zuwa d’akin shi nan yaga Sumayya a tsaye tana kallon shi ya rab’ata ya wuce bathroom yayi alwala lokacin an idar da asuba hakan yasa yashimfid’a pray mate yayi sallahn.
Sumayya na tsaye yana yin sallama tace mai, “Yaya Ma’ar yarinyar nan baza ta k’ara kwanan gidan nan ba,bata da kunya inajin sanda take ce maka karya kake.”
Lazimi ya fara ba tare da yayi mata magana ba dan har lokacin be huce ba.matsawa tayi bakin gado ta zauna tana turumai baki ganin yayi mata banza yasa ta rik’e bayan tana yarfe hannu tare da cizon lips….
“Wayyo Allah na !
“Wayyo na shiga uku Yaya cikina… !
Ta fad’a tana rintsa ido tare da dafe cikin da hannu.da Yaya mata banza amma daya san ciki zai iya yin komai sai ya k’arasa wajanta yana tambayarta.
“menene Sumayya.?!”
K’arama ce ta shigo cikin d’akin sai faman kale-kale take kafin ta juya tana kallonsu ta saki dariya tamkar wata babbar mata. Matsawa tayi kusa dasu tana kallon Sumayya dake jikin Ma’aruf tana rik’e da ciki k’arama tace….
“Kai.. ! wallahi k’ayya take yi babu ciwo a cicinta.”
Wata uwar harara Sumayya ta rafkawa K’arama tare da zare mata idanuwa yadda Ma’aruf ba zai ganta ba.itama K’arama kwalalo mata ido tayi tana kallon cikin Sumyyar,dariya tayi tana zama kusa da Ma’aruf tana cewa,
“Kai… ! akwai yaro an kallallami a cikinta she motsi yake yi, lah yana tayi wallashi zo kagani kaima….!”
Tayi magana tana k’ok’arin kamo hannun shi cikin sauri Sumayya ta bige mata shi da kafa,cikin masifa take magana.
“Waike dan ubanki baki san dai-dai bane? Tashi ki fita dalla can sai uban zarni kike yi salon kisa min tashin zuciya… !“
Ma’aruf ya bita da kallo yadda yaga ta zage sai masifa takewa K’arama,ga mamakin Sumayya sai taji tana cewa…,
“Wallashi bazan tahi ba, bayan d’a zuma sai da kika sha na cikin jarka har kika yi amai irin wanda amaryar ilu takeyi…..”
Zaro idanuwa Sumayya tayi tare da shigewa jikin Ma’arufa ta fashe da kuka tana cewa,
“Yaya wannan yarinyar mayya ce,nidai gaskiya bazaka barmin ita a cikin gidan nan,Yaya Ma’ar wannan yarinyar wata rana d’an cikina zata cinye dan Allah ka fitar min da ita ni wallahi bana sonta bana son zama da ita shegiya mumafuka kawai….!”