ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

����
��
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM��
&
K.A.S Precious HAJJA CE��
SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
Page *7-8*
Yana shiga office din ya iske Abban nashi baya ciki Messenger Office din ya tambaya ina Abban ?yace mashi sun shiga meeting ne ……Sakon ya bashi ya juya ya fita tare da gaisawa da wadanda ke mashi magana ……
WHO Office dinsu ya nufa ,Tunda ga waje zaka fahimci wayeshi ta yarda dukka mutanen gurin suke bashi girma Cikin mutunci yake amsa masu gaisuwarsu saboda babu wanda bai girmeshi ba a gurin kawae Sa’ar Rayuwa Allah ya bashi……
Hadadden office dinshi ya nufa wanda ke dauke da kayan alatu na rayuwa
Coat dinshi ya cire sannan ya ja kujera ya zauna Bude laptop din dake saman table din yayi tare da saka siririn glass din dake aje kusa da wasu tarin files……Cikin natsuwa ya fara bincike yanayi yana lumshe idonsa wanda ya rigaya ya zame masa d’abi’a……
Duk wani abunda ya shafi case din da garin da abun ya faru an rigaya an turo mashi ta email dinshi har ta hotel da room number da zai sauka an turo mashi da number State Consultant da LGA facilitator dinsu ……
Dogon tsaki ya sake lokacin da ya rufe laptop yana fadin “Gwadabniya” tare da tabe baki……Bai bata jin sunan garin ba a rayuwarshi bare ya saka ran zaije wata rana ……Kara sakin karamin tsoki yayi ya dafe kanshi kamar ya sake ihu tare da cire glass din……
Komawa yayi bisa tarin takardun da ke aje ya fara bincikawa cikin natsuwa har ya fitar da da wani file。 sannan ya mike ya fita ya baiwa Messenger dinshi yace ya kaiwa Doctor Habib…………Gida ya nufa don ya shiryawa tafiyar saboda yarda ya tsara bara yayi kwana biyu ba a garin……
《》《》《》
Malam Sani Mahaifin Hafsatu yayi sallama gidan…… tun kafin ya karaso cikin gidan Jummai ta tare shi a zaure tana rike da tabarya “Malan Hafsuwalle ta zo……” ta fada murya kasa kasa ……
“Ahhaba ki ce baki mukayi yau, Marhaban da mutanen Keteriya!amma ita haka ake zuwa babu sanarwa ……?ya karashe maganar yana kokarin zagayeta ya shiga cikin gidan
Cikin sauri tace “Har da jaririyar ta danya shar Malan……”
Yar dariya yayi irin ta manya sannan yace “Ai kunga abunda yafi haka indae Hafsatuta ce ,akwae janye janye yanzu haka ta makwabtace ta dauko!Hafsatu a akwae son mutane……”
Murya kasa kasa tace “Kai Malan Hafsatun ka ta haifeta da cikinta…”ta karashe maganar tana nuna cikinta da hannu
Wani kallo ya jefa mata yana fadin “Bana son zancen banza jummai,Malan lado ya warkene?
Watsa hannu baya tayi tana fadin “Ina fa ya warke malan?abun kunyane ta janyo maka da mutuncinka a garin nan……”
Bai ce mata komae ba ya wuce ya shiga gidan yana kwalawa hafsatun kira,Daga jin yarda yake kiran kasan bana kwanciyar hankali ba ne ,Dukka mutanen dake cikin d’akunansu suka fito sukayi cirko cirko suna maganganu kasa kasa wanda daga ji kasan gulma suke……Daga Hafsatun har Inno da lauratu suka fito waje……Hannu Hafsatun ya kurawa ido sannan ya kalli fuskarta ……
Jikinshi yayi sanyi lokaci guda ya kalleta yana fadin “Hafsatu ina kika samo jaririya haka…?
Kasa magana tayi sae kukan da ta saki a hankali tana kallon kasa ……
“Dake nake Hafsatu!ina kika samo jaririya danya haka……”
“Jaririya ta ce Ard’o…” ta fada cikin kuka…
“Mijinki ya warkene Hafsatu……?ya tambaya cikin sanyin jiki
Girgiza kai tayi tana share hawayenta ……
“To Ina kika samota Hafsatu? d’iyar wacece haka?
“Ard’o d’iyar Lado ce……!ta fada har lokacin tana kuka
“Watsatstsan Zance Hafsatu ……Wanga zancen naki ko Shanun gidannan bara su karb’a ” Cewar mutanen gidan kamar hadin baki……
Da Sauri ya karbi jaririyar daga hannunta ya nufi wata katuwar bukka yana kwalawa Sallau kira …Sallau ya fito daga bayan gida rike da katuwar sanda a hannunshi yana fadin “Shanun ne suka balle Ard’o”
“Fiton da Turmin kurtumi Sallau……”Cewar Ard’o yana nuna bukkar da hannu……
Matan gidan suka dauki magana kasa kasa tare da kallon juna suna taba hannuwa……
“Malan karka yi kisan kai ,ka dae san wannan jaririyar bata halak ba ce tunda tsawon shekaru takwas mijinta baya da maraba da gawa……”Cewar Jummai tana kokarin karbar yarinya
Cikin matan wata tayi zagal tace “A Kara ya kasheta da wannan mugun abun kunyar da ake niyyar dauko mana”
Hafsatu banda kuka babu abunda takeyi ,ita kam lauratu shiru tayi tana kallon ikon Allah ,haka Inno bata iya cewa komae ba don ta yarda da Hafsatu bara ta aikata abu mai muni irin haka ba ……
Gangaro da katon bak’in Turmin ne yasa gidan ya kara kaurewa da maganganu kasa kasa……
Ard’o bai ce komae ba ya jefa yarinyar cikin Turmin ya ma sallau alamar da ya miko mashi tabarya……
Babu musu Sallau ya mika mashi katuwar tabaryar tare da ja baya……
HAJJA CE��
FEEDOHM��
[13:32, 26/11/2017] hm: ���� ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》
����
��
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM��
&
_K.A.S Precious HAJJA CE��
SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyar mu
Page *9-10*
*G*aba ki d'ayan mutanen gurin jikin su yayi sanyi dan sunsan yau kwanan jaririyar ya kare. 6angaran Hafsatuwalle kuwa ko d'ar bata jiba sai dai hankalinta a tashe yake dan tasan ko anyi wannan abun babu wanda zai yadda da ita cewar yarinyar lado ce, ba tare da ta ankara ba sai jin daka tayi tumm... *!!!* nan ta bi Ard'o da idanu yadda ya zage yana daka jaririyar tamkar yana daka gumba.
“Kur’anin Allah ‘yar nan ta halak ce, gashi nan da ranta garau…”
Cewar Sallau yana k’okarin fito da jaririyar da Ard’o ya gama kir6awa tamkar ma babu abinda aka yi mata dan yadda aka sata haka aka fito da ita subul…
Duk jama’ar gidan suka waro ido da tsananin mamaki kafin kowa ya maida hankalinshi ga Hafsatu dake kallon k’asa tana wasa da jelar gashin ganta. Inno ta dafe k’irji tana kallon Hafsatu cikin nuna sonjin k’arin bayani.
“Hafsatu gamu ki gaya mana ya akai kika samu wannan cikin harkika haife shi bayan munsan lado bashi da mamora tsawan shekaru…”
Fad’in yabint tana daga nesa amma tana son jin tsegumi da jin kwakwaf…
"Yabint *!* ai na gaya muku cewar jaririyar nan ta lado ce tunda gashi turmin kurtum ma ya shaida gaskiya..."
Hafsatu ta kuma fad’a nan da nan magan ganu suka ci gaba daga baku nan mutanan gidan k’asa-k’asa, Ard’o ya zabura tamkar zai tashi sama yana kallon Hafsatuwalle yace…,
"Aradun Allah wannan maganar tak'i Hafsat akwai d'aure kai, muna son mu shaida zancenki tunda ga turmin kurtumi ya shaida amma ai lado bashi da lahiya bayya iya yin komai taya wanga lamari ya faru? Zamu je can shi gwadabniya dan mu shida."
Turmin kurtumi dad’add’an turmine tun zamanin iyaye da kakannin, al’adar garin ce in dai mace ta haihu dole ne aje a sashi ciki a kir6a dan tabbatar da cewar yaron ko yarinyar ta halak ce. Tsafataccen turmi ne sannan kuma yarda da imanin da alummar garin suka yi da hakan shine yasa indai suka daka mutum a ciki be mutu ba to hakan ya tabbatar musu da cewar d’an halak ne duk kuwa da cewar tsakanin ma’auranat akwai sadaki amma duk sanda suka haihu sai an saka yaro a cikin turmin kurtumi ko kuma cikin wuta da take ci ganga-ganga tamkar za’a kuna karamin daji…”
(Wannan ke nan)
Kus-kus aka farayi kafin inno ta furzar da huci mai zafi tace.
"Ni dai kam Hafsatu zaman ki ba dai a d'aki naba. Ard'o sai dai ka sama masu inda zasu tsafa rayuwar su ni dai kam bada niba..."
Guri ya kaure da hayaniya kowa ya nuna badashi Hafsatu zata zauna ba, sallau yasa suka yi shiru Hafsatu na hawaye ganin kowa yak’i ta lauratu ta k’arasa tare da kama hannunta itama cikin kukan take mata magana k’asa-k’asa.
"Umma ta kiyi shiru ki dena kuka, idan kowa ya guje ki ni ina tare daku kiyi hakuri Umma na..."
Kafin Hafsatu tayi magana sukaji muryar Ard’o na cewa.
"Mukam dai Hafsatu sai dai ki zauna a rumfar Yafindo, amma damu da yaran mu babu ruwan mu daku karku shafa mana *Abunda ke 6oye* har sai randa munkaji gaskiya."
Nan da nan hayaniya ta kaure a cikin gidan Kafin kace me, tuni an watse daga gurin kowa ta kama harkar gaban shi ana ta yada magana lauratu taja hannun mahaifiyar ta suka shiga cikin d’akin Yafindo da aka basu shi. Babu koma cikin sai k’asan ma duk k’asa ce haka suka shiga lauratu ta cire mayafinta ta nunkashi tasa a k’asa sannan ta kwantar da yarinyar akai.
"Umma ya kinka sa sunan jaririyar...?"
Tana hawaye jikinta na rawa ga jini sai zuba yake ta k’arasa gurin jaririyar tana shafa kanta tace “lauratu na sanya mata suna Hafsat Allah shi raya mana ita.”