ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ke aradun Allah ba inda zani,idan kinga nabar gidan ga kwananane ya k’are,kuma kwarankwatsa dubu kika sake cewa ya fita dani zaki sani…. !

Cewar k’arama tana faman yiwa Sumayya wani irin bahagwan kallo wanda yasa silalowar tusa jikaki buttt…!!daga jikin Sumayya dake faman zaro ido tana kallon na k’arama tamkar rik’e mata su aka yi bata san ma ta fito ba.

Wata dariya ce ta kwacewa Ma’aruf wadda be shirya yinta ba,kallon shi Sumayya tayi cikin jin haushi ga k’ara da cikinta keyi tamkar wata me baseer da d’an kanoma ta mik’e a fusace tayi toilet tana kuka mai cike da takaicin su. Tana shiga shi kuma ya samu dariyar ta tsaya sannan ya had’e rai yana hararar K’arama dake ta faman kallon kamar tana nazarin shi ya d’an daka mata tsawa amma ko gezau ba tayi ba hakan yasa shi tab’e baki yana kallonta yace…,

“Ke little daga yau karna sake jin kince ga abinda ke cikin mutum kina jina…? !

Kawar da kai k’arama tayi tare da sauke numfashi tamkar katon namiji sannan ta kalleshi tana share majina sabida sanyin daya bugeta yasanya mata mura tace mai.

“Kai..! Nifa wunya nakeji (yinwa) aradun Allah da a kyauyen mune tuni Umma ko Yaya lauratu sun bani naci….”

Shafa sumar kanshi yayi tare da mik’ewa tsaye yana kallonta itama shi ta kurawa ido kaika rantse cewar mayyar ce sabida har lasar lebenta take tana kwakular tasono idan ra samu ta goge a jikinta….

“Oya jiki ki jirani sai na zo muje kici abincin… !

Ya fad’a dan so yake tabar d’akin ya sauya kayan jikinshi,tashi tayi tsaye tana ka gyara yagaggiyar rigar jijinta ta fita. Da sauri ya zura wando da riga dan karta shigo sabida yasan ba hankali gareta ba,yana kokarin fita Sumayya ta fito sai faman uban nishi take tana kokarin yin magana ya d’auke car key yafita…..

{{ }}

Suna shiga gun Madre suka tarar da ita a kitchen tana had’awa Abba breakfast, Ma’aruf ya zaunar da k’arama a parlor tare da cewa yana zuwa. Kitchen ya nufa yana yiwa Madre magana…

Daga bakin k’ofar ya tsaya yana kallonta,

“Morning madre..!”

“Yauwa Ma’aruf yau da sassafe haka kuma ko wanka banajin kayi a haka..?!”

Ma’aruf ya sauk’e ajiyar zuciya ya k’arasa cikin kitchen d’in ya fara yiwa Madre bayani akan k’arama. Acan parlor kuwa k’arama ce ta kurawa plasma TV idanuwa tana kallon mutane tamkar zasu fito,k’arasawa tayi gurin tana magana tamkar me magana da mutanen gaske tana cewa…..,

“Lalalah toh ku hirhito mana kawai he ku kama ku b’uya? Taga kamar basu jita ba sai ta fara masifa……

“Idan zaku hito ku hito bana son kayya,wayahi kuhito…… !

Karad’in ta yasa suka fito da gudu kafin su tsaya suna k’are mata kallo ita ta juya tana kallon cup d’in hannun Madre da gudu ta karasa tana cewa.

“Zan sha! Zan sha kunu…!!!”

Cup d’in hannun Madre K’arama ta fizgi kofin tare da karawa a damilallan bakinta, sai da ta shanye tatass sannan ta sauk’e kufin tana kallon Madre tare da dashare yalayen hakoranta tace,

“Umma zan k’ara ban kohi ba a gida Yaya lauratu a kwanan shan ruwa take bani farau-farau inha in kohi sannan taha itama…!”

“Allah buwayi… !” Madre ta fad’a tana k’ok’arin komawa cikin kitchen. “Kai baza ka shaba?!”

K’arama ta tambayi Ma’aruf, girgiza kai yayi sannan yace “zan sha ba yanzu ba kema kuma baza ki k’araba sai anyi miki brush da wanka sannan zaki k’aracin wani abun…”

Sumayya tana ganin ya fita taja tsaki mai tsawo,phone d’inta ta janyo tana kiran beeba, ta kusa 6miss call kafin beeba ta d’auka wadda tana zaune bakin gado tana kallon sarkar gold d’in da Sumayyar ta bata. Da kyar ta d’aga tana yatsina fuska kai da ka gani kasan bata son d’agawa.

“Hello beeba…!Na shiga uku wannan maganin a memakwan ya kankaro min mutunci da soyayyar Yaya Ma’aruf sai ma neman rabamu yake beeba wannan maganin zasu lalata soyayyata da mijina d’an uwana… !

Sumayya ta fad’a cikin hasala, beeba tayi murmushi tana kuma damk’ar sark’ar hamnunta,cewa tayi mata.

“Toh Sumy yanzu me kike nufi?!”

“Ki sake kawo min wasu irin na da sunfi kyau dayin aiki,beeba ina son mijina inason kullum ya dinga jina tamkar sabuwa please yaushe zaki kawon sababbi..?”

Sumayya ta fad’a yana jiran taji amsar beeba,cikin dauriya beeba d’in tace mata.

“Toh shikenan naji zan samo miki but! Yanzu wadda take yin na da d’in bata nan tana sokoto amma idan ta dawo zan kar 6omiki….”

“Yauwa beeba thanks kinsan yanzu ina da ciki kuma karki ga yadda Yaya Ma’aruf yake son shi yanzu na k’ara zama abar kaunar shi sosai,inason kishiga ki fita wajan samar min ingantattun magunguna.”

Tunda Sumayya ta furtawa beeba cewar tana da ciki zuciyar beeba ke bugawa ta dinga furta kalmar ciki a cikin ranta. Da kyar ta ce mata “karki damu za’a kawo miki.”

Tana kaiwa nan ta yanke kiran tare da mik’ewa tsaye,yanzu kam maganin da zai 6arar da cikin shi zata nemo cikin ALWASHI ta furta.

“Sumayya sorry wallahi, baki dace da Ma’aruf ba domin ni yafi cancanta daya aura ba ke ba.zan fitar dake na dasa k’iyayyarki a zuciyar shi zaki gane baki da wayyo ke shasha shace wawuya kawai…. !

Kiran Kausar beeba ta hauyi tana d’agawa tace,

“kina ina?
“Ina skull wani abun ne?”

Kausar ta tambaya beeba tayi kwafa tare da cewa “all right idan kin dawo kina free let me know.”

“Ok bye..!”

{{ }} {{ }}

Madre ce tafito ta jere kayan karin kumallon akan dining table tana jin tausayin K’arama dan aljanu basu da dad’i akwai ‘yar kanwarta da suka ta6a shafarta har ta koma ga Allah bata ta6a yin aure ba sabida sun aure ta.

“Madre bari naje na samo mata kayan da za’a saka mata wad’annan sun yake sai uban wari suke yi….!”

Ma’aruf ya fad’a yana k’okarin fita Madre tace mai toh,yana fita ta kalli K’arama dake faman muzurai upstairs tayi dan sanarwa da mai gidan nata cewar breakfast is ready. Tare suka fito da tsananin mamaki suka kalli K’arama dake faman tura soyayyar doya a cikin bakinta Madre ta saki salati tana tafa hannaye tare da cewa,

“Hafsat……. !!!

FEEDOHM????
&
HAJJA CE????
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》

               ????????
                  ????

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????

SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu

 Page *63-64*

“Hafsat… !!!

Madre ta dakawa K’arama tsawa lokacin kuma sun k’arasa wajan,bata ko kulata ba sai faman dannawa bak’inta doyar take. Da sauri Madre ta buge hannun K’arama tama manta da cewar basu ihsan bane sai da Abba yayi mata magana “Hafsat rabu da ita.” sannan tunaninta ya dawo.

“Ka aleta bayan nace mihe inajin yinwa hinefa yace mutaho nan kuma munzo ga abuncin amma wai he anyi min wanka kuma ni banaso…..!”

A hankali Mandre ta k’arasa wajan K’arama wadda ke ta faman zarar idanuwa yatsunta cikin bakinta tana lashewa yau taci abinci mai dad’i da karkad’a kunne.

“Hafsatu ai da kinjira nazo sai na zuba miki amma yanzu gashi kin cinye ta sauran guda uku.”

“Na dena toh shikenan?!”

K’arama ta fad’a tana kallon juck d’in kunu, Madre ta kalli Abba tare da cewa,

“Kayi hakuri alhaji bari na soya maka kwai tunda ta cinye wannan…”

“No kibarshi kawai nayi latti yanzu, yau idan naje nasamu wani abun naci acan, ita kuma a gyarata idan na dawo sai ku sanar dani wacece…”

Yana kawai nan yiyi hanyar fita dama yafito da brief case d’inshi,Madre taje ta raka shi sai da ya tafi sannan ta dawo ciki. Bata ga K’arama ba a dining area d’in hakan yasa ta shiga kiran sunanta tare da dube-duben inda zata ganta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button