ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Hafsatu! Hafsatu!! Oh ni Hafsat yau naga ta kaina wannan wace irin yarinya ce…? Kizo muje a tsaftace ki amma kunk’i…!!!”
Madre nata sababi abinda bata saba yiba koda Sumayya na nan amma yau K’arama tasa sai zagaye take tana bud’e murya. A haka Ma’aruf ya shigo hannun shi rik’e da ledoji yaji Madre sai kwalawa K’arama kira take yi, ya kalleta cikin mamaki tare da tambayarta lafiya,
“Ma’aruf wannan yarinyar anya zan iya da ita kuwa? Yanzu breakfast d’in dana had’awa abban ka kafin naje nasanar mai ta cinye doyar tatass! Sai hakura yayi ya tafi aiki a haka yanzu na,dawo na nemeta na rasa kuma bamu fitaba tare bare nace kin shigowa tayi…”
Kayan ya ajiye shi kanshi yasan ya d’ebo ruwan dafa kanshi,amma so yake ya ceceta kodan albarkacin jinyar da Mahaifinta yayi gashi ita yarinya ce da take buk’atar a temaka mata.
Tare suka shiga nemanta amma ba ita ba labarinta, ita kam K’arama gurin Sumayya ta koma zaune ta tarar da ita tana kallon curin maganin nan da beeba ta kawo mata, tunani take yi akan Tasha ko ta hakura duk da cewar hatta warin maganin sai ya dad’e bebar cikin bak’inta ba gashi babu wani dad’i haka dai taji zuciyar ta na so kawai ta gutsira tana shinshinawa zata kai cikin bakinta taji muryar K’arama na cewa.
“Lalalah idan kikaci daddawa da fulawa sai na gaya mai ince sheda kika kala ci….!”
Sai da k’irjin Sumayya ya buga ganin K’arama yasa ta mik’ewa a fusace tana nunata da yatsanta tace,
“Ke ni ubanki zanci wallahi,shegiyar yarinya mayya kawai toh kurwata d’aci gareta tafi karfinki kuma sai kin bar gidan nan yau aljana kawai…”
K’arama ta kurawa cikin Sumayya idanuwa tana murmushi tare da karkata kanta sai kuma ta fara matsawa gurin Sumayya tana k’ok’arin kai hannunta saman cikin wanda hakan yasa Sumayya yin baya tana zaro idanuwa tana fad’in.
“Idan kika kuskura kika ta6amin ciki ya zube ba aljanu ba yau ko shuri ne a kanki sai na sauke miki shi…”
“Toh ba wasa zan mihi ba.”
“Ba’a so shegiyar yarinya kawai.”
K’arama tace “sheh anyi d’in.”
Tana fad’a sai ga Sumayya a gefen gado a zaune idanuwan ta sun firfito gumi ya fara wanke mata riga,ganin idanuwan K’arama tamkar na zaki yasa cikin ta ya kuma juyawa a haka K’arama ta k’arasa tana shafa cikin da d’an k’aramin hannunta sai b’ab’aka dariya take tamkar mahaukaciya tana cewa.
“Yalo idan ka fito tare za muyi wasa amma hmmm!”
Tayi shiru bata k’arasa abinda zata ceba, sai da ta gama wasan ta a cikin Sumayya sannan tace,
“Na tafi suna can suna jira na.”
A tunanin Sumayya aljanun ne suke jiranta hakan yasa zuciyar ta k’ara hargitsewa tabi K’arama da kallo har tabar d’akin sannan ta kurma ihun a kawo mata d’auki (k’ila ta manta ba kowa a gidan).
{{ }}
A zaune suka ganta wajan step da kufin kunu a hannunta tana sha ta mik’ar da kafarta samb’al tana kad’asu, Ma’aruf ne ya fara ganinta cikin had’e fuska dajin haushin tanajin su tayi shiru ya kalleta yace,
“Bakiji ana kiranki ba shine kika yiwa mutane shiru stupid kawai?!”
“Toh bana zata wanka za’a min ba, ni bana son wanka kuma baza amin ba d’in.”
Tayi maganar tana turo baki tare da rarraba idanuwa,Madre taje ta kamo hannunta amma ta fizge ita a dole baza je ayi mata wanka ba. Cikin azama Ma’aruf yaje ya zata suka je bathroom ya kalli Madre tare da cewa,
“Madre idan bata tsaya ba ki Zane ta marajin magana kawai.”
Yana fad’a yayi parlor ya zauna kan kujera yana jiran fitowar su, Madre ta kalli K’arama baki d’aya idan bata kawo zuciyar imani ba bazata iya tab’ata ba sabida tayi dik’il-dikil da ita ga uban zarni da take yi cikin murmushi Madre tace,
“Idan banda ke mai sunana ai ba’a zama da dauda ki bari ayi wanka kema zakiji dad’i.”
Karamin hijjab d’inta ta cire mata sannan ta fara k’ok’arin cire mata kaya amma K’arama taki yadda,rigima suke inda Madre ke mamakin k’arfi irin na yarinyar kafin ta fito daga bathroom tayi hanyar parlor tana cewa.
“Yo ina dalili haka kawai yarinya ta dinga hankad’e ni,kai Ma’aruf yarinyar nan bata son wanka kaga yadda ta dinga ture ni tamkar wata babba,toh bazan iya ba ni kam.”
“A’a Madre yarinyar nan dole ayi mata wanka, har wani wari-wari take yi ga zarni tamkar bayin da yake shekaru ba’a wanke ba please Mamana.”
Kallon shi kawai tayi sannan tace, “a’a tashi muje kila idan tana ganinka zata tsaya amma yarinyar akwai iya fad’a.”
Tare suka k’arasa bathroom d’in nan suka tarar da ita ta tatse makilin kaf ta had’a shi da shampoo,conditioner tana kad’asu cikin bukiti.
“K’arama menene hakan? Oh ni Hafsatu…”
Tana ganin Ma’aruf ta fara dariya tana washe mai hak’ora yayi d’an tsaki sannan ya cewa Madre “ku fara idan bata tsaya ba kuma sai na mareta.” K’arama tayi saurin kallon ganin da gaske yakeyi yasa ta bari Madre ta cire mata kaya pant d’in jikinta yayi dikil-dikil duk jurwaye gashi an kulleshi daga gefe Madre tasa hannu ta cire shi da kyar tamkar tayi amai,kanta a cukurkud’e da kyar Madre ta warware shi duk Ma’aruf na tsaye yana kallon su yana jin tausayin ta.
Da kyar aka wanke kan sannan aka yi wanka harda yi mata brush ana yi bakin na jini tamkar an naushe mata shi, cikin towel Madre ta nad’ota tace Ma’aruf ya d’auketa ya kaita d’akinta,sai da ta kwashe kayan takai bula sannan ta bisu d’akin.
Kayan da ya siyo mata aka sa mata amma fur tak’i bari ayi kwalliya,sai a lokacin ne Ma’aruf ya Kara tabbatar da cewar lallai mutum ya d’akko ba aljanaba aljanun kawai ajikinta suke. Tayi kyau cikin doguwar riga ‘yar kanti red da white ne colorn gashin ma tak’i yadda a gyara duk kuwa iya kokarin da Ma’aruf yayi wajan ganin an gyrata amma fur da haka yayi musu sallama yace anjima zai zo idan yaje ya sanarwa da ya sayyadi dan jin yadda za’a farowa lamarin.
{{ }} {{ }}
GWADABNIYA
Mai-tafasa ce a tsakar gida tana ta tsinkar tafasa tana sawa cikin buhu dan yanzu ta gano cewar duk sanda taje ta d’ebo to idanuwan Kundum na kanta tana zargin cewa tana d’ibar mata dan mafi akasari Kundum tafiyin tuwo da miyar tafasa kuma ba siya take yiba hakan yasa take sawa cikin buhu yanzu.
Gefe guda kuma wasu garken tumaki ne da kaji da agwagi da taje ta kwasowa duk wanda be biya ta bashin da take binshi. Asibi ne da Buwale suka shiryo munafunci suka taho gurin Mai-tafasa ta kallesu ta watsar tana gunguni Buwale tace,
“Yoh ke Mai-tafasa ai jama’ar gari aradun Allah suna nan suna hirya miki yadda zaki bi lado d’azu muka jiyo ana shirya yadda za’a yi miki ta bayan gida…”
“Jakar uban nan! Aradun Allah Buwale bana son muna hurci,ni nan da kuke gani ko a cikin birni Hakimi hakuri yake bani bare mutanan kauyan nan,aradun Allah kuma ku fita idona ahe…!“
Kundum tayi saurin fitowa daga d’aki tana gyara zani ta kalli Mai-tafasa tana dukan gefen cinyarta tace,
“Aradu acan binni Hakimi zane ta yayi, nan tazo tana cire kaya mukaga shatin tsumungiya amma tana cewa wai Hakuri ya bata mtw…!”
Maitafasa tayo kan kundum su Buwale suka koma gefe suna kallon su kafin kace me tuni ancika gurin ‘yan team d’in Kundum sunfi yawa sai cewa suke “yauwa kundum yauwa kundum.” Maitafasa na surfa musu zagi baki d’aya tun mutuwar ladonta komai ya kara rud’ata.da kyar kande da lantana ne suka raba dakyar duk sun jigata.
*
Hafsatuwalle kam rayuwa…….
hh
FEEDOHM????
&