ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

HAJJA CE????
[22:06, 12/27/2017] +234 806 677 6651: ???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》
????????
????
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????
SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
Wannan shafin naku ne kuma dan jin dad’in ku Ayush, Maman sultan, Mira fodio, Mmn zainab, Aysha b fullbe, haleema Mahmoud, Jidda Adam, Olo asha karatu lafiya
Page *67-68*
Wajan la’asar Sumayya na parlor sai ga beeba ta zo, da murnarta ta tare ta tare da komawa cikin bedroom bayan taja hannun beeba, kallonta beeba tayi a yatsine tana bin d’akin da kallo Sumayya tace,
"Kawata kinsan kuwa wancen magungunan bama su kyau bane? Wallahi nasha wahala yanzu ma na gama shanye na cikin jarkar duk da Yaya Ma'aruf ya hanani shi dan shima ba k'aramar wahala yasha ba."
Sumayya ta fad’a tana yatsina fuska tamkar yanzu ne take shan maganin, beeba ta tab’e baki sannan tace,
"Ni kinga ba wannan zancen ba yanzu ina shi Ma'aruf d'in yake...?!"
Mtww Sumayya taja tsaki tare da turo shi tana cewa,
"Baya nan wallahi beeba ya tashi ya kawo min wata yarinya mayya har d'an cikina take gani,d'azu da tazo kuwa beeba na rantse miki da Allah kusan kashe ni tayi sai da na barta tayi wasa da cikin yan jiran honey nake yi dan wallahi bazai bar min yarinyar nan a gurina ba yar k'aramace salon a barni da raino...."
Beeba dai ta tab’a baki cikin rashin damuwa da maganar ta zuge Jakarta ta ciro wani garin magani a roba k’arama mai garai-garai tana mik’awa sumayya.
"Ga shinan wannan na k'ara ni'ima ne zaki sha shi da ruwan d'umi idan zaki kwanta yana da kyau sosai wallahi."
Cikin murna da d’oki Sumayya ta karb’a tana godiya tare da kankame beeba tamkar zata had’iyeta, bedside drower ta bud’e ta bata wani turare me kyau da tsada beeba ta karb’e ta danna cikin jakarta aranta tana fad’in,
"Zaki gane baki da wayyo Sumayya, cikin ki na b'arewa zan mallaki Ma'aruf cikin ruwan sanyi ke kina nan kina hauka."
Hira suka d’an tab’a tun beeba na saka ran ganin Ma’aruf har aka kusa magrib taka bashi ba alamar sa kawai ta mik’e tayi shirin tafiya.
"Toh uwar biyu ni na tafi sai gani na biyu."
Beeba ra fad’a tana sab’a Jakarta a kafad’a, Sumayya ta biyo bayanta tana fad’in.
"Allah na d'auka sai bayan sallar isha zaki tafi, any way nima na samu nasha magani na nasan kafin ya dawo na kusa jik'ewa daya zo kinga kafin yayi wanka sai ai....."
Beeba tayi saurin katseta ta hanyar cewa,
"Naji nidai kinga tafiya ta." Tana fad'a tayi waje da sauri tun kafin maganar Sumayya ta illatata."
Tana tafiya Sumayya ta koma cikin bedroom d’in, da kyar ta tsaya tayi sallar magrib sannan ta fara kokarin fara amfani da maganin da beeba ta kawo mai, sai da ta fara shiga kitchen ta d’akko kufi ta tsiyayi warm water a cikin Despenser sannan ta koma d’aki. Neman maganin tayi amma sama ko k’asa ta rasa, to ina yake! Ta duba ko’ina babu har hawaye tayi dan bak’in ciki sai kuma tayi saurin kiran wayar beeba tana d’agawa ta fara magana.
"Beeba wallahi banga maganin ba."
"Eh mana duk na duba ban ganshi ba beeba ya zanyin yanzu please do something to me kinji kawata."
"Kai ya ilahi yanzu kenan sai wani satin? To bari dai na sake duba dan wallahi ina son yau muyi har...."
Kafin ta k’arasa abinda take shirin fad’a beeba ta yanke kiran, Sumayya ta kuma mik’ewa tahau neman maganinta.
{{ }} {{ }}
K’arama kuwa tun sanda ta haniniyi tuwanta ta d’anyi wasa sai ta sheme akan center carpet tana sharar bacci wanda minsharinta ya hana Madre sakat a cikin parlorn sai tashi tayi tabar gurin ta koma d’aki. Bayan sallar isha Abba da Ma’aruf suka dawo a tare suka shiga ciki K’arama ta fellah da gudu tare da rungume Ma’aruf hannunta duk miya tana shan rumon naman da Madre ta zuba mata gaba d’aya duk ta b’ata mai wandon jikin shi.
"Oh my God small Mom duk murnar gani nace, toh oya muje ciki k'i k'arasa cin abincin ki."
Ma’aruf ya fad’a yana tura keyarta suka koma cikin parlon, abban Ma’aruf yayi murmushi tare da kad’a kai tunawa da yayi shi yaushe rabon da idan ya dawo gida ayi mai Oyo yo har ya manta.
"Sannu da zuwa abban Ma'aruf.!"
Madre ta fad’a tana k’arb’an brief case d’in hannunshi, yana kallonta cikin kulawa yayi murmushi tare da cewa,
"Yau kin samu 'yar hira ko kirana baki gani ba ko?!"
Madre tayi dariya jin abinda yace tana kokarin d’aukar wayar ta tace,
"Kaina bisa wuya ban ga kiranka ba course yarinyar nan hmm Allah dai ya bata lafiya kawai."
"Madre yau ta saki surutu ko?!"
Ma’aruf ya fad’a yana zama cikin d’aya daga cikin kujerun parlorn, K’arama kam komawa tayi ta d’auki boul d’in da ruman ta ke ciki ta dawo kusa da Ma’aruf tana mik’a mai tare da fad’in.
"Kaima muha a tare kaji?!"
Ma’aruf yayi saurin kauda kanshi yana fad’i “no no no, bana sha na koshi…!”
Ta tab’e baki tare da cewa “kai fa ni bani da nono irin na Yaya laulatu kani.”
Tayi maganar tana k’ok’arin d’aga mai rigar ta yayi saurin da kar ta ita yana kallonta suma su Madre na kallonsu suna jinsu tare da yin dariya yace mata,
"Cewa nayi a'a bana sha na k'oshi."
K’arama tace “au to ni bara na shanye.” Ta fad’a tare da kafa kanta yana mata magana amma inaa sai data shanye ruman tas sannan ta kalleshi tana dariya tana sauke numfashi da kyar. Nan Ma’aruf ya sanar da abban shi labarin K’arama tare da d’orawa yana cewa,
"Gobe zamu zo da ya sayyadi zai dubata insha Allah za'a fara yi mata addu'o'i da ruk'iya."
Abba da Madre suka taya shi da addu’ar samun nasara kafin yayi musu sallama ya tafi dan anan zai bar K’arama sabida baya son rigima bare Sumayya ta takurai mai. Yana shiga parlon su sai yaga K’arama zaune kan kujera tana mai wani irin kallo, kalle-kalle ya farayi yana tambayar kanshi da cewa “ta ina ta shigo?! Ganin ba amsa yasa shi nufarta yana addu’a a cikin zuciyar shi.
"Kaga maganin da aka kala kawo mata wai tasha, bata gani ba kuma na d'auke kaga fa na zubar da yaron cikinta ne kuma ni ina son ya fito mu dinga wasa."
Tun Ma’aruf na tsora harya dake ya k’arasa tare da k’arb’ar robar maganin yana dubawa, cikin zuciyar shi tambayoyi ne fal ya kalli K’arama sannan ya wuce bedroom d’in Sumayya a hargitsan shi tamkar iska yana kwala mata k’ira, yana shiga ya ganta kan bedside tayi jigum duk ta lalata d’akin, tana d’agowa taga rubar maganin a hanin shi hankalinta ya tashi ta fara inda-inda ganin yadda ya had’e rai wanda bata tab’a gani a fuskar shi cikin masifar da ba saba yinta yayi ba yace.
"To he'll with you Sumayya..."
Sannan ya buga rubar a kasa maganin ya bud’e gabaki d’aya ya zube yayi kaca-kaca da d’akin sannan ya nunata da yatsa idanshi yayi jawur yace,
"Idan kika kuskura kikayi abinda yasa cikin nan ya zub'e wallahi Sumayya kin zubar da auranki...."
Yana kaiwa nan yabar mata d’aki tare da bugo mata kofa, K’arama dake tsaye ta lekata tare da fad’in,
"Wullo..."
Sumayya ta jeho mata pillow sai dai be sameta ba K’arama ta dinga mata dariya wadda kesa Sumayya k’ara hasala. Yau kam duk kulaficin ta akan shi bata samu ba dan fata-fata yayi mata yayi kwanciyar shi a nashi d’akin itama haka amma tasha kuka ta tsinewa K’arama yafi cikin d’akinta.
Cikin dare yana bacci yaji mutum a jikinshi yana dubawa yaga K’arama, be wani ji tsoroba yayi mata addu’a sannan ya juya ya kwanta shima……
{{ }} {{ }}
Washe gari tun asuba ya duva yaga bata d’akin yayi addu’a ya fito ya leka d’akin Sumayya yaga tana bacci sannan ya koma ya shiga toilet yayi alwala yayi sallah.
Kamar yadda suka yi sa ya sayyadi ana idar da sallar juma’a suka tafi gidan Madre lokacin itama Sumayya na can takai karar shi, kota kanta be biba ya sanarwa Madre ga liman yazo ina K’arama.
"Tana nan d'akin bak'i na rasa abinda take yi a cikin shi kuma dana leka zan ganta a zaune."
Can ya tafi yana kiranta amma tsit bata amsawa, har ya shiga be ganta ba ya duba bayi bata ciki nan da nan aka hau neman K’arama ba ita ba labarinta har wajan la’asar liman ne ya gano cewar guduwa tayi.
"Ma'aruf sun gudu da ita babu mamaki sunji labarin abinda za'ayi mata shi yasa, amma ka bari zamu san wata hanyar."
Ya sayyadi ya fad’a mamaki ya kusa kashe su a haka yasa aka maida liman suka koma cikin gida nan suka ganta zaune a wajan stairs tana wasa da wata ‘yar tsana tana musu dariya…….
FEEDOHM????
&
HAJJA CE????
[15:42, 12/30/2017] +234 806 677 6651: ???????? ABUNDA KE B’OYE……
《Almost True Life Story》
????????
????
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM????
&
K.A.S.Precious HAJJA CE????
*SADAUKARWA……*
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
Page *69-70*
K'arasawa yayi kusa da ita tare da tsugunnawa ya kura mata ido cikin sanyin murya yace "Hafsa……"
Dariya ta sake tare da wurga yar tsannar sannan ta mike tana daga doguwar rigarta tace ” Baka ganni ba ko……?
“Ina kika shiga?
Kai tsaye tace “Yo bayan kujelu……”
Cikin sanyin murya yace “Me yasa kika boye?Bakya son ki warke ki kuma gurin Ummanki Hafsa……”
Waro ido tayi tare da rike baki tana kallonshi kafin ta girgiza kai tace “Yo wa zaya koma gurin Umman……?
Da hannu ya nuna ta yana kallon yarda ta kafe shi da ido……
“Tallahi ba inda za’ani!kawae in koma na cigaba da cin tuwo kullun ina kwana a buhu? ka raina ni!da k’warank’wasa komin bala’inka bazan bar nan gidan ba sae dae ayi yadda za’ayi……”ta fad’a tana kyafta idanu tare da murgud’a baki……
Dariya ya saki mara sauti sannan yace “Ba yarda za’ayi Hafsa!Indae gida ne kiyi zamanki amma dan Allah idan kinga Malan ki daina guduwa kinji ko……”
Murgud’a baki tana kyafta idanu tare da gunguni ta juya baya……
Shiru yayi yana kallonta kafin ya mike tsaye yaja hannunta……
【】
Dukar da kai yayi yace “Malan ya kake tunanin zamu bullowa wannan matsalar tunda yarinyar bata bari ku hadu kuma ni ban tab’a ganin wannan kalar aljanun ba ko a labari……”