ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

????????
????
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM????
&
K.A.S.Precious HAJJA CE????
*SADAUKARWA……*
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
Page *71-72*
Tana shiga ya riketa ya cire mata kaya!Fizge fizge ta fara tana fad’in “Bana so!dazu fa ka man ……”
Daure fuska yayi yace “Ko ki tsaya ko na kifa maki mari!
Murguda baki tayi tace “Sae in rama……”
Bata rufe baki ba ya maretan yace “Oya rama……”
Dafe gurin tayi tana kallonshi sannan tace “Na yafe ma……”
“Allah ya shirya ki……”
Bata amsa ba har ya gama mata wankan ya kama hannunta ya je ya shafa mata mai ya canza mata kaya tare da kashedin karta b’ata kayan jikinta……
【】
“Munahurci dodo mai shi yakan hadiye!Cewar Maitafasa tare da wurgawa Kundum harara……
“Mai jaraba……Yi hoho!Kundum ta fad’a tare da yin taga taga ta fad’a cikin fitsarin shanun dake malale tsakar gidan……
Shewa Maitafasa tayi tare da gwatso tana murgud’a kugu tace “Kowa yasan ke munahuka ce Kundum shi yasa ma k’asa ta kadaki yanzu……!
Kundum kam rike kugu tayi tana cije baki tace “Taimaka man Maitafasa da k’warank’watsa kamar bayana ya kare……”
Yatsina fuska tayi taja majina ta matso tana fad’in “Duk da bana sonki kundum kuma bana son ku mutu ki barni……”
Kama hannun kundum tayi ta d’agata ta mike da kyar tana dafa kugu har suka isa inda suka shinfida buhu suka zauna sannan kundum tace “Nagoda Maitafasa……”
Tsaki ta ja da karfi tace “Komae sae kinyi Munahurci Kundum!meye na tausasa murya kuma?
Banza kundum ta mata tana so ta rike gulmar dake cinta amma ta kasa a hankali ta tab’o Maitafasa tace “Wae Maitafasa……”
A Harzuke ta juyo tace “To Uban me ye kuma kike tab’a man buje?
“Ba Bujenki na tab’a ba!Wae ni kam ina labarin su Hafsuwalle?ta fad’a ahankali tana tsoron amsar da maitafasa zata bata……
Banza ta mata tare da jan dogon tsaki ta kai kwanon fura a bakinta !
“Maitafasa kinji labarin Mijin Buwale kuwa……? ta sake fad’a cike da gulma……
“He ni Maitafasa na shiga uku!Shin ke Kundum idan bakiyi gulma ba baki jin dadi ne?
Tab’a hannu tayi tana fad’in “AA Maitafasa kawae naji ana fad’in wae amre zai k’ara ba tare da sanin buwale ba……”
Tsaki ta kuma ja ta tattara bujenta ta mike ta leka ta katanga ta d’aga murya tana kiran “Buwale……”
Da sauri Kundum tace “Mai tafasa me zaki fad’a mata……”
Banza ta mata ta cigaba da k’walawa Buwale kira har ta leko da daurin gabanta tana fad’in “Lahiya ……?
“Mijinki na nan?Ta tambayeta tana watsa hannu baya……
Buwale tace “Eh Maitafasa lahiya?
Kallon Kundum tayi da tayi mutuwar zaune sae raba idanu take sannan tace “Ku zagayo tare turke za’ayi!
Bata jira komae ba ta koma tayi zamanta tana watsa hannu!Tab’ota Kundum tayi tace “Dan Allah mai tafasa karki fad’a masu!Da k’warank’watsa karya nake babu wanda yace man mijin buwale zaiyi amre!tallahi jiya naga ya sayi hurar yar gambo shine na dauka ko sonta yake……”
Yatsina fuska tayi tace “Ke dae ake ji……!
Sallamar buwale da mijinta yasa cikin kundum sake duran ruwa tayi cikiciki da idanu tana kallonsu……
“Lahiya Maitafasa……?
Watsa hannu tayi tace “Kundum tace mijinki zai kara amre baki sani ba!shine na kiraki ta fad’a maki ubanda ya fada mata!idan kuma mijinki ya fad’a mata to ta fad’a maki meke hadinta dashi……”
Cakuma Buwale ta kaiwa mijinta tace “Aka ce me zakayi?
Da yake tsayyaye ne ya tsinka mata mari tare da fincike rigarshi ya nufi fita yana fad’in “Da nasan wannan shashancin ne tallahi da banzo ba……”
Buwale kam ba zafin marin ya dameta ba !kan kundum ta koma tana dunguri tare da tambayarta wanda ya fad’a mata!shiru kundum tayi tana raba idanu……Tas ta mata sannan ta na hargagi!dunguri kam da mauza Kundum ta shasu !sae da Buwale ta fita sannan maitafasa ta kalleta ta kwashe da dariya……
【】
Tun tsakar dare Sumayya ke labour yayin da kugunta ya matse gam yaki bud’ewa!Asibiti ya kaita amma duk yarda aka so ta haihu da kanta taki yiyuwa saboda maganin da take yawan sha ya matse mata kugu ta yarda bara ya iya budewa ba bare ta haihu da kanta!CS aka shiga da ita cikin sa’a aka fito da Yarinyar ta kyakykyawa sak Ma’aruf sae da duhun da wasu bangarorin na jikinta da yayi kuma duk sanadin maganin matan da take sha……
Sae da komae ya natsa sannan aka kira Madre da Maryam da sauran family din aka fad’a masu !asibitin kam cika yayi kamar anyi shela……
Ma’aruf ya fad’a wa Madre cewa maganin matan da take sha ya hanata haihuwa sosaae Madre tayi mamaki don ita ko da Sumayyan zatayi aure bata dirka mata irin wadannan magungunan ba ……Ce mashi tayi zata wa sumayya fad’a ta daina sha idan ta warke……
kwanansu Uku aka sallamesu!Gidan Madre aka koma da ita ……Kwata kwata Ma’aruf ya fita harkan Sumayya saboda so yake ya hukunta ta aka laifin da take,sossae ta shiga damuwa ta rasa inda zata saka ranta!ranar daren suna ta sami Madre a d’aki tana tambayarta wae ina yaya Ma’aruf duk yau bata ganshi ba ?
Kallonta Madre tayi ta juyar da kai tace “Ki kira wayarshi mana idan ganinshi kike sonyi”
Kamar tayi kuka tace “Ai baya dauka!
Duk da Madre ta san dalilin rashi daukar sai cewa tayi “Kin mashi laifi ne?
Girgiza kai tayi tace “Ban masa komae ba…”
A hankali Madre tace “Bata yiyuwa!
Hannun Madre ta kamo tace “Allah kuwa……”
K’arama ta fad’o tana fad’in “Ba wani karya kike kin masa man!
Kuka Sumayya ta saki tana fad’in “Kin gani ko Madre wae karya nakewa wannan shegiyar yarinyar……”
Daure fuska tayi tana kallon K’arama sannan tace “Zo nan Hafsah ba na hanaki karyata mutun ba!
“Ai sae tayi hakuri……”K’arama ta fad’a tare da ware hannu……
Lokacin Madre ta samu ta ma sumayya magana akan magungunan da take sha!daga farko cewa tayi babu abunda take sha amma daga baya da taga ran Madre ya b’aci dole ta sauko tace tana sha……Sossae Madre ta mata fad’a tare da nuna mata illolin da abun zai janyo mata gaba……
Daga Farko ta dauki fad’an sannan ta tsorata ganin cewa maganin yasa aka mata CS Amma daga baya sae ta fara tunanin idan babu maganin kamar barata yi daraja ba gurin Ma’aruf din!Don haka ta kira Beeba tace ta hado mata wasu……
Ranar suna hidima sossae akayi yayin da yarinya ta ci sunan Madre wato HAFSAH……Suna kiranta da Udutti……Su ihsan sae murna ake an samu Sister……
Watansu Biyu gidan harda K’arama!cikin dan lokacin ne Madre ta farawa K’arama amfanin da magungunan da aka bata!Cikin ikon Allah ta fara rage wasu abubuwan kamar fad’ar abunda mutun yaci sam ta daina!Ga wata natsuwa da ta shigeta.Ga kunya da Allah ya daura mata don ko had’a ido da mutane ba ta yarda tayi saboda kunya!Wani lokacin ma idan Ma’aruf ya shigo gidan kafin ya mata magana zata sulale ta bar gurin!Cikin wata biyu ta warke ras kamar ba ita ba!yayin da jin dad’i da kwanciyar hankali ya tabbata akan fatar jikinta……
Ita kanta Sumayya yanzu tana jin d’ad’in K’aramar saboda kullun tana zaune gurin Udutti tana mata wasa!Idan kaga K’arama na dariya to tana gurin Udutti ne!
Ko da zasu koma gidan Ma’aruf din Sumayya ta kafa naci sae sun tafi da ita saboda Madre cewa tayi a barmata ita ta samu abokin fira……
Kwanciyar Hankali ta sake fito mata da usulinsu na Fulani !Tsaf ta juye kamar ba ita ba Sannan ko kadan bata kama da Hafsuwalle kallo d’aya zaka mata ka gane tsantsar kamar da tayi da MALAN LADO hatta Muryarta da yatsun hannunta duk nashi ne……