ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan wata hudu ne Ma’aruf ya k’ara tabbatar da warkewarta yace wa Madre zaya maidata gida!Ita kanta Madre din ba haka taso ba ta so K’arama ta zauna da su iya tsawon rayuwarsu saboda yanzu duk wanda zai zauna da K’arama bara ya so ya rabu da ita ba……

Tana goye da Udutti Ya shigo da sallamarshi!kanta na k’asa ta amsa ta cigaba da jijjiga yarinyar!Bisa kujera ya zauna ta juya zata shige d’aki kamar munafuka……

A Hankali yace “Bunkul……”

Da sauri ta juyo ta saki dariya tare da rufe bakinta da hannu !kanta na kasa tace “Uncle dae ba Bunkul ba……”

Dage gira yayi yace “Ashe yanzu kin iya……!
Hannu ta saka ta rufe fuskarta zata tafi ……

HAJJA CE????
&
FEEDOHM????
???????? ABUNDA KE B’OYE……
《Almost True Life Story》

               ????????
                  ????

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM????
&
K.A.S.Precious HAJJA CE????

   *SADAUKARWA……*

HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu

      Page *73-74*


  "Zo nan Ina Auntyn ki……?

Ba tare da ta juyo ba tace “Tana kitchen……”

Tabe baki yayi yace “Zo ki zauna anan ……”

A Hankali ta dawo ta zauna a kasa tare da tallabe yarinyar ta sunne kai k’asa……
Cike da zolaya yace ” Baki fad’a man me na ci ba a waje……”

Still rufe fuskarta tayi da hannu ……
“Kunya ko Hafsah!Good……Gobe zan mayar dake gida kin ji ko!ko a bari sae wani month din bakya son komawa?

Da sauri ta girgiza kai tana fad’in “Ina so mana……”

Dariya yayi mai sauti yace “Kenan kin yarda ki koma ki ci gaba da cin tuwo kullun……”

Murmushi tayi kanta na k’asa !Sumayya ta shigo ta zauna gefenshi tana fad’in “Yaushe ka dawo ban ji ba……”

Kallonta yayi a hankali yace ” Kina can kitchen dama ya zaayi kisan na dawo!Me kike had’a mana naji kamshi ya cika mana gida……”

Far tayi da ido tare da kama hannunshi sannan tace “Daddawa nake soya mana zamuyi kwad’on wainar da Madre ta aiko mana d’azu……”

Mamaki ya hanashi magana na tsawon yan mintina sannan yace “Kwad’on Waina a gidannan Sumayya a matsayin Lunch dina?

Fari ta kuma tace “Ai yaji albasa……”

Tsaki ya saki da karfi yana fad’in “Ba zanci ba gaskia!Zan kai K’arama tawa Madre bankwana ki samar man abunda zanci kafin na dawo……”

Turo baki tayi tana gunguni!banza ya mata yana fad’in “Bata ita ki dauko Hijab Hafsah…”

A Hankali ta juya ma Sumayyan baya ta cire yarinyar amma sae cewa tayi “Ki je da ita mana……”

Kallonta yayi ya tabe baki had’e da girgiza kai yace “Idan ta maki yau gobe bara ki ganta ba……”

Da sauri ta kalleshi tace “Ina zata……?

Kai tsaye yace “Gidansu……”tare da mikewa tsaye……shiru tayi tare da binta da ido kamar mai nazarin wani abu yayin da jikinta yayi sanyi sossae……

Bata ce komae ba ta shiga daki ta dauko Hijab suka tafi!

Bankwana sukayi da Madre sossae ta hada mata yan kayan sawa tare da chocolate masu yawa tace ta bawa yan garinsu tsaraba sannan ta tsinto tsufaffin kayanta tace ta bawa yan garinsu suma!Ita kanta Madre din daurewa kawae take amma har ga Allah bata son K’arama ta tafi!lokacin da ta rakosu harabar gidan ta bawa Ma’aruf 100K din da Abban ya bawa K’arama tace ya biya da ita super market ya mata sayayya!Ma’aruf din yana lura da Madre da ta juya ta goge hawayen da suka zubo mata!A sanyaye ya amshi Udutti dake ta tsala kuka ya shiga motar yayin da K’arama ta shiga itama tare da hade kai da guiwa ta saki kuka mai sauti……

Driving kawae yake amma sam kukan ya hanashi natsuwa!Cikin lallashi yace “Bakya so ki tafiya ne Hafsa……”

Girgiza kai tayi har lokacin tana duke tace “Ina son ganin Ummata da yaya Lauratu!kuma bana so na bar Madre na kuka……”

Shiru yayi yana kallonta sannan yace “Bara ki barta ba kinji ko Hafsa!Zan je wata rana na daukoki ki mana hutu kinji ko……”

Gyada kai tayi a hankali……

“To bar kukan mana Small mom!kina son Makaranta?

Still gyad’a kai tayi tare da dagowa tana kallonshi…

Baiyi tunanin kaita super market ba ya wuce da ita gida sannan ya fita yayo mata tsarabar……

【】

Sae da ya fara kaita gidan Hakimi sannan!Shi kanshi Hakimin bai ganeta ba sae da Ma’aruf ya mashi bayani sannan ya ganeta!mamaki yayi sossae ganin yarda ta koma kamar ba ita ba!ko da Hakimi ya tok’aleta da magana shiru tayi tana sinne kai!hadashi da guard akayi sannan suka nufi kauyensu……

Kundum ce ta fara ganin motarsu ta katanga!Da gudu ta iske maitafasa a bukkarta tace ” Mai tafasa bature ya dawo!

Bingil ta fito tana fad’in “Yana ina na buge hege!!

A Tare suka fita sae dae kafin su fita waje har motarsu ta wuce kauyen su Hafsuwalle!Da daurin kirji suka nufi kauyen kamar zasu tashi sama……

Dae dae gidan Ardo motar ta tsaya yayin da Ma’aruf da guard din suka fara fitowa!Mutane suka yi cirko cirko suna zuba ido!Zulai dake wanka ta fito da gudun tsiya jin cewa Baturen da ya dauki K’arama ya dawo……

Fitowar K’arama daga mota yasa numfashin mutanen dake gurin ya sark’e kamar had’in baki suka kira sunanta tare da dafe baki K’a.. K’a.. K’arama…!!!

“Ta shiga engini tayi bilihin (engin bleaching)……”cewar Zulai tana dafe bak. Hafsuwalle kam kusan mutuwar tsaye tayi na ganin K’arama ta canza kamar ba ita ba yayin da Lauratu ta k’araso gurin ta tsaya sae kyarma take son k’arasawa gurinta take tana gudun ta kama K’arama guard d’in dake gurin ya daketa……

Murya a sarke tace “K’arama..!ke ce kuwa?” Murmushi tayi ta juya tana kallon Ma’aruf sannan ta rufe fuskarta da tafin hannunta k’arasawa tayi wajan ta tare da kwantar da kanta bisa kafad’ar Lauratun……

“Ta kwarankwatsa ita ce!K’arama ke ce kika koma haka?!Aradun Allah sak Ladon Maitafasa badaban da bature kika zo ba babu abinda zai hana muce fatalwar ladoce tayi suffar mace……” Cewar Jummai tana tafa hannuwa!

K’arasowar Maotafasa wajan tana fad’in “Kai ku bani guri!Ta k’warank’watsa yadda yasa aka ci mutuncina a birni yau sae na ci……!Shiru tayi tare da kafe K’arama da idanuwa baki sake kirjinta ya tsananta bugawa cikin sarkewar murya Maitafasa tace!

"Ladona……!" ta sulale a wajan ta sume sabida tsabar ganin suffar d'anta lado ajikin k'aramar yarinya. Da kyar aka samu ta dawo hayyacin ta idanunta akan K'arama baki na kyarma tace,

 "Lado na..." Ta fad'a tare da fashewa da kuka ta cigaba da fad'in "Dama shege na biyo Wani a kamani bayan shi sanda akayi iskancin yana kwance ba lahiya?"

Mutanen gurin kam kaurewa suka yi da surutu kasa-kasa, zuwan Ard’o ne yasa Lauratu kama hannun K’arama suka shige ciki yayin da Ard’on ya ja hannun Ma’aruf suka shiga bukkar shi yasa Inno ta kawo mashi fura……

Mutanen gurin kam tsaye suka yi suna maganganu K’asa k’asa……

Godiya sosae Ard’o ya masa sannan ya k’ara da cewa “Ranka ya dad’e duk wanda yaga yanayin Hafsatu ko ba’a fad’a bs ya san ta warke!Mun gode sosae Allah ya kaimu lokacin da zan biyaka alherinka nima.”

Cikin natsuwa Ma’aruf yace “Ameen Baba!Amma nayi wannan abun ba dan a biyani ba……”

Dariya Ard’o yayi yace “Ai ko dole mu biya ka Da Hafsatu……”

Cikin rashin fahimta yake kallon Ard’on sannan yace ” Na gode sosae amma ta ya za’a biyani da ita?ita kanta tana son zama gurin Mamanta bare ace a bani na tafi da ita gaba d’aya ……?”

Cikin natsuwa Ard’o yace “Shin Hafsuwalle zata amri Hafsatu ne?

A Hankali ya girgiza mashi kai alamar a’a!

“To ka gani!ka ga kenan dole mu baka sadakar auren Hafsatu……” Ard’o ya fad’a a hankali.

Da sauri Ma’aruf ya kalleshi bakin shi na kyarma yace “Wace Hafsatu?

Kafeshi Ard’o yayi da ido yana fad’in “Hafsatu K’arama da kamaido mana da ita yanzu!shine kadae zamu iya biyan ka dashi akan taimakon da ka mana akanta……”

Da sauri Ma’aruf yace “Waccen yarinyar?yana nuna cikin gidan da hannu……

Dariya Ardo yayi yana girgiza kai sannan yace “Idan na iya lissafi Hafsatu K’arama na da shekara bakwae!Kenan saura shekaru biyu ta cike Tara!wanda dama a ka’ida shekara tara muke aurar da ‘ya’yan mu!kaga kenan idan na amrar da K’arama yau banyi garaje ba sae ta ida cike shekaru biyun a d’akin mijin ta…!”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button