ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Zumbur Ma’aruf ya mike yana kallon Ard’on kafin ya fita daga d’akin da sauri ya shige mota ……Biyo shi Ard’o yayi yana fad’in “Ka taimaka mana wallahi babu masoyin Hafsatu duk wannan yankin……Sun ce shegiya ce babu wanda zai bari d’anshi ya aureta……”

Da sauri Ma’aruf ya fito ya tsaya gaban Ardo yace “Karya ne ba shefgiya bace !”

Wuf Maitafasa dake jingine tana jiran fitowarsu tace “Idan karya ne kaine Ubanta?

“Idan ina magana kika kuma saman baki wallahi sae na saka an rufe man ke……!” ya fad’a a fusa ce ……

Hayaniyar su ta kuma janyo hankalin Su Lauratu da sauran mutanen gidan suka fito waje……

Watsa hannu tayi baya tana fad’in “Idan baka sa aka kulleni ba ka raina Uwaka!” ta karashe maganar tare da yi mashi dakuwa……

Guard d’in shi ya taho zai kamata amma Ma’aruf ya dakatar dashi “Barta tayi abunda take so zuwa gobe bazata samu damar yi ba……”

Watsa hannu tayi tana tafi “A Barni d’in ta Allah ba taka ba!Kulya Dubu saba’in a kurwar Maitafasa!Nan gani nan bari Maitafasa aniyarka ta bika!ta kwarankwatsa na dad’e da sanin ku duka munahukai ne!An d’auki yarinya ankai birni!an lalata ta !tayo bilihin ta goge (bleaching) ……to me ya hana ka barta acan ka amreta…….?

HAJJA CE????
&
FEEDOHM????
???????? ABUNDA KE B’OYE……
《Almost True Life Story》

               ????????
                  ????

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM????
&
K.A.S.Precious HAJJA CE????

   *SADAUKARWA……*

HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu

      Page *75-76*


   Ard'o da ya kai iya wuya dajin abinda Maitafasa ke fad'a  bai san lokacin da ya kifeta da Mari ba sae gata zaune a k'asa tana bori a Fusace yace "Na gaji da rashin Mutuncin……" Bai rufe baki ba tayi zumbur ta mik'e tare da kwarfa mashi mari shima……

Hafsuwalle kam kuka ta saki a gurin ganin duk bala’in da ake yi akanta ne da d’iyarta yayin da mutanen gidan jikinsu yayi sanyi……

Hannu Ma’aruf ya d’aga zai mareta amma K’arama ta rugo tare da rik’e hannun tana kuka tace “Dan Alla Uncle karka daketa..!”

A Hankali ya mayar da hannun shi k’asa yana kallon Maitafasa……Maitafasa kam ihu ta saki tana fad’in “To Bakar munahuka ki barsa ya dake ni mana!kai kuma asararre yarinya ta hanaka d’aukar mataki!Yi huhuhu!Dangin ‘yan iska, Idan kai kacika d’an Halak ne ka dauke su ka amre Uwar da d’iyar……!”

Kanshi ne yaji yana juyawa don tunda yake bai tab’a ganin kalar masifar wannan matar ba, anya tana da cikakkiyar hankali kuwa?Wani b’angare na zuciyar shi ya tabbatar mashi da hankalinta kawae tsabar jahilci ne kawai..!Ard’o kam hawaye ne suka cika mashi ido A Hankali ya ja hannun Ma’aruf tare da kai shi bakin motar shi ya had’e hannayen shi biyu yace “Ka gafarce mu dan girman Allah.”

Muryar Maitafasa suka ji tana fad’in “Yo ya tsine maka mana me ya shille ni ni Maitafasa?tsohun batau kawae!an dawo mana da bala’i cikin gari, ta k’warank’watsa kai ba d’an halak bane tunda har ka k’asa barinta gurinka ka amreta!wae ni Maitafasa za’a jonawa haushi shine har da tafiya da ita!ashe abun na wohine (wofi) sakarai kawai……”

A Hankali ya juyo yana kallon K’arama dake zaune k’asa tana kuka cikin sanyi murya yace “Hafsah kin san menene aure?zaki iya aurena?na maki alkwarin rayuwa mai inganci!ban damu da kankantarki ba!bazan cutarki da ke ba da yardar Allah.!”

Kamar an d’auke ruwan sama haka gurin yayi tsit!yayin da Maitafasa tayi baya jikake timm ta darshe k’asa baki a bud’e tana kallon Ma’aruf!K’arama kam a razane ta d’ago tana kallonshi yayin da hawayen idonta suka kafe da sauri tace “Uncle Aure irin na yaya lauratu?

Gyad’a mata kai yayi idonshi cike da hawaye tsabar takaici da bak’in ciki……,

Cikin kyarma Ard’o yace “Zaki aureshi Hafsatu ki samu rayuwa mai inganci babu wani kwaciyar hankali a kauyen nan sae wuya da bakin jahilci ……!”

Hafsuwalle ta kalla wadda bata san lokacin da ta gyad’a mata kai ba tana rufe bakinta da hannu alamar ta yadda!Mayar da kanta tayi ta had’e da guiwa taci gaba da kukanta……

A Hankali Ma’aruf yace “Ku shiga muje gidan Hakimi……”

Sannan ya nufi K’arama ya sa hannu ya d’agata ya bud’e mata motar ya shigar da ita!Ard’o kam shiga yayi ya zauna shi da Sallau!

Mai unguwa Ma’aruf ya hango yana k’ok’arin k’arasowa gurinsu wanda da alama yanzu ya zo gurin……

Cikin Kyarma Mai unguwa yace “Ka gafarceni Tallahin Allah shanuna ne suka……

Bai K’arasa ba Ma’aruf ya cewa Driver su tafi……Suka tada mota suka wuce da gudu tare da bad’e mutanen gurin da k’urar taya……

Suna tafiya Mai unguwa ya fashe da kuka yana kallon Maitafasa da ta daskare a zaune a gurin don har ga Allah bata tab’a tunanin Ma’aruf zai yadda da gatsan da tayi mai ba kawae tayi ne don ta ci mishi mutunci amma sae gashi shi ya ci mata nata mutuncin ya bad’a mata kasa a ido a bainar mutane……

“Kin cuceni Maitafasa……” Mai unguwa ya fad’a cikin kuka……

Kundum da jikinta yayi sanyi tace “Yau dai kam ABINDA KE B’OYE ya fito hili (fili) Tallahin Allah baki kyauta ba Maitafasa!Idan kin duba da kyau ta k’warank’watsa dubu K’arama jininki ce saboda ga tanan Sak Ladonki!kuma tallahi harta yatsun kafafunta nashi ne!Kuma tallahi ke ni kaina nasan K’arama d’iyar Lado ce domin zan iya rantsewa akan idona aka samu cikin ta, tun lokacin da Hafsawalle na gidan Lado nasha lek’ensu idan suna Rayuwar amre (aure)!Ni kaina ina mamakin su kamar jarababbu!sannan kuma tallahi wani lokacin Ladonki ne ke bukatar Hafsuwalle sae ta taimaka mashi har ya samu gamsuwa tana yi tana kuka tare da kale-kale dan karki isketa…. !

Duk abunda suke haka zan zagaya ta ‘yar kofar dake bayan bukka ina lek’en su ina zagin su sabida ina ganin ai sa bari a samu waraka!Dan Allah Hafsuwalle ki yaheman (yafemin)……”

Ta K’arashe maganar tare da fashewa da kuka mai cike da nadama

Kuka Maitafasa ta saki tana harba k’afafuwa a k’asa tace “Amma kin cuceni Kundum kin ha’ince ni ta k’warank’watsa!me na maki haka a rayuwarki Kundum?”

Mutanen gurin ne suka fara tofa albarkacin bakin su akan lamarin!Wad’anda suka ga K’arama suka fara zuzuta irin kamar da take da Lado yayin da wasu na fad’in har muryasu iri d’aya!Hafsuwalle kam kuka ta saki mai tsuma rai yayin da Inno ta ja hannunta da Lauratu suka shige cikin Bukkar ta……

Maitafasa kam kuka ta cigaba da yi tana harba k’afafu kamar wata k’aramar yarinyar tare da jan majina yayin da Kundum ita ma ke kukan!sauran mutanen kauyen kam suka fara zarewa tare da tofin Allah tsine ga Maitafasa da Kundum……

Ma’aruf Kam suna zuwa gidan Hakimi ya kira Madre ya fad’a mata abunda ke faruwa!Ce mashi tayi a jirasu yanzu zasu biyo private jet ita da Abban shi su zo!sam bata k’yamaci abun ba sae dae addu’ar ta Allah yasa hakan ya zama mafi alkairi Alkhairi……

Hakimi ya tura motar Police a ta fi a d’auko Maitafasa yanzu nan kafin su k’araso!Cikin awa biyu Su Madre suka zo tare da Abbahn Ma’aruf!

Suna isowa suka shiga fadar bayan sun gaisa Ma’aruf ya sake fad’awa su Madre abinda ya faru!Abban shi kam murmushi yayi irin nasu na manya yace “Ma’aruf kam Dan halak ne i sha Allahu zai nuna musu hallacci!ina Uban wannan yarinyar? ina nemawa d’ana Ma’aruf auren Hafsatu……”

Thumb Madre ta masa ya dukar da kai yayin da kirjin shi ke dukan Uku uku!K’arama kam rakub’ewa tayi jikin bango ta had’e kai da guiwa tana hawayen domin duk rikicin nan tasan akanta ake yi gashi har Ma’aruf na zubar da hawaye……

Cikin kankanin lokaci aka d’aura auran Auren shi da K’arama wanda Sallau ya zama waliyinta tare da sadaki dubu dari……

Kallo d’aya zaka ma Ard’o ka tabbatar da yana cikin farin ciki!Sadakin aka bawa Ard’o sannan aka yi duk abunda ya dace tare da sa hannun Hakimi sannan Ard’o da Sallau suka koma kauyen su!Yayin da K’arama da Madre da Abba suka juya katsina suka bi private jet suka koma aka bar Ma’aruf anan gidan Hakimi saboda akwae aikin da zayayi!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button