ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

【】

“Bala……!!”

Da gudu ya taho ya zube a kasa yana fad:in “Gani ranki ya dad’e……”

Yatsina fuska tayi tace “Kasan sassaken Bedi……?
Da Sauri yace “Eh na sani ranki ya dad’e……”

“Yauwa shi zaka jeka d’ebo min yanzu!”

Mikewa yayi yana fad’in “To Ranki ya dad’e……”
Banza ta masa ta koma cikin gida!mintina kad’an ya dawo rike da bakar leda ya mika mata Udutti ta basa wai ya jijjigata kafin ta gama girki!K’arbar yarinyar yayi ya koma dakin shi da ita tare jib’eta saman tabarmar shi ya ciga ba da bankar tabarshi……

Yarinyar tayi ta juye juye daga k’arshe ta fashe da kuka!banza ya mata amma jin kukan na damun shi ne yasa shi janyo kafafunta ya dawo da ita gaban shi yana mazurai!Ganin ba shiru zata yi ba yasa ya tafka mata duka a kirji yana fad’in “Dan ubanki ki min shiru!banda son banza irin na wannan matar meye na bani wani raino……!”

Yarinyar ta cigaba da kukanta da k’arfi!babu tausayi ya d’auketa tare da tsinkulinta a cinya ya fita d’akin ya yiwa Sumayya sallama daga parlor……

Fitowa tayi da NAN a cup ta mika mashi tana fad’in “Karbi ka bata may be yunwa take ji……”
Idonta ya faka ya kuma tsunkuli yarinyar a cinya ta fashe da kuka yace “Ranki ya dad’e dan Allah ki karb’eta kinga kuka take yi……”

Harara ta watsa mashi tana fad’in “Yarinyar ma baza ka iya rikewa ba!? to je ka yarda da ita kani ko……”
Zai yi magana ta saki tsaki ta juya ta shige abunta!Shima juyawa yayi yana surutai ya koma d’akin ya kwantar da yarinyar a kasa yana fad’in “Baki yi Sa’ar Uwa ba Alqur’an……”

NAN d’in ya d’iba a spoon ya kai a bakin shi yaji da dad’i ai kuwa bai yi wata wata ba ya d’aga cup d’in ya shanye ta tas!bako tausayi……

ALLAH ya nuna mana sabuwar shekara lafiya bada wayun muba ba dabarar mu ba Allah ya nuna mana k’arshenta da rai da lafiya da imani Amin????

HAJJA CE????
&

FEEDOHM????
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》

               ????????
                  ????

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????

SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu

 Page *77-78*

Hakimi ne ya kalli Maitafasa wadda keta faman soshe-soshe tana wuwulk’ita idanuwa yace mata “ke wai ya sunanki ne ma?!”

Mai-tafasa ta sharce majina tana jan wata zuwa cikinta ba tare da tayi magana ba, tunawa da tayi da shegen dukan da taci kwanaki shi ya k’ara rud’ar da ita cikin tsawa bafadan hakimi yace “baza ki fad’a bane sai jikijnki ya gaya miki?!”

Da sauri sukaji tace “Suwaiba….!”

“Toh me yasa baki da hankali ne?!”

Hakimi ya tambaya yana tsareta da idanuwa, ta kalleshi da sauri tana rik’e da habarta cikin tsananin mamaki tace,

“Inji wane shege yace banida hankali? Aradu wuta bal-bal ban yaheba gaduk wanda yace maka wai banida hankali aheeee….”

Bafadan ne ya kuma daka mata tsawa ta hanyar cewa, “ke! Hakimi na tambayar ki kina rashin ladabi? Ana tambayar kine idan kina dashi ki fad’a idanma babu ki fad’a dan asan hukuncin da za’ayi miki.”

Muzurai ta fara yi da idanuwa tana tunanin wanda zata zab’a hankalin ko rashin sa wanda ba zai sa a jibgeta ba, baki na rawa tana kallon Ma’aruf ko zai yi magana taji yayi shiru ranshi a had’e sai zabga mata harara yake bafadan ya kuma daka mata tsawa a rud’e Mai-tafasa ba tare da ta saniba tace,

“Da sauk’i dai aradun Allah Hakimi wani sa’in bana sanin nayi abu sai daga baya, dan Allah kada kasa a dokeni tsofai-tsofai dani….”

Tayi maganar tana matsar kwalla kamar gaske, tsaki Ma’aruf yayi dan yasan karya take kawai ta fad’a ne dan kar a k’ara dukanta, Hakimi ne yayi magana yana kuma kare mata kallo ganin ta kasa zama waje d’aya sai canzawa take.

Hakimi ne ya kuma kallonta da tsantsar mamaki ganin k’irik’iri ta nuna mai cewar tana da matsala a kwakwalwarta, gyaran murya yayi tare da cewa,

“Toh koma dai menene kisa a ranki cewar kece dangin Hafsatu K’arama,an d’aura mata aure yanzu itada Ma’aruf kisawa ranki Hafsatu jikarki ce shi kuma sirikinki ne.”

Dukan cinyarta tayi tana cewa “tallahi Hakimi na yadda da cewar K’arama ‘yar lado nace domin ABIN DAKE B’OYE ya fito hili kamanin shine sak dan dai ita macace amma bazan fasa tsine mata ba domin itace ta cinye min kurwar ladona ba,tsakanina da K’arama sai Allah ya isahh….”

Rintsa ido Ma’aruf yayi yana jin tamkar ya shak’i wuyan Mai-tafasa, girgiza kai kawai Hakimi yayi tare da cewa,

“Tashi ki tafi…”

Cinyarta ta buga da hannu kafin ta mik’e tana gyara zani, Hakimi ta kalla tana gatsine cikin kuluwa tace mai,

“Rankashi dad’e abani na mahin mana kur’anin Allah sisin kwabo bana magani gahe mai-unguwa ba zuwa d’aukata zaiyi ba.”

Ma’aruf ne ya zaro 1k yabata dan yasan kakar K’arama ce hakan yasa ya bata amma badan halinta ba,ganin wanda ya bata ne yasa ko na gode bata ce maiba ta kalli Hakimi tare da washe mai jajayan hakuranta wad’an da wasu suka fara cirewa tace,

“Ranka shi dad’e toh yanzu kuma heyauhe za’a nemeni?!”

Ko kulata Hakimi beyi ba ganinta akwai surutu sai bafaden shi ne ya rakata har bakin kofa tana fad’in.

“Aradun Allah Hafsatuwalle munahika ce, tazo kuma ta haifi mayya gashi nan ta cinye kurwar mahaifinta ta rasa tsuntsu ta rasa tarko ta kare a zaman gidan arna da karuwai oh ni Mai-tafasa Allah gata na nima dan nafi karfinta ne da tuni k’ila ta lasheni…..”

Har aka fitar da ita bakinta be mutuba Ma’aruf yayi tsaki tare da mik’ewa yayiwa Hakimi sallama akan washegari zai dawo,hotel yaje ya kama baki d’aya ya gaji kanshi tamkar zai fad’i dan tsananin ciwo da karad’in Maitafasa.

Wanka ya fara yi sannan yayi sallolin da ake binshi azahar da la’asar, gado ya hau tare da d’aukar phone d’inshi nan ya tarar da miss call wanda kusan duk na Sumayya ne, Madre ya k’ira yaci sa’a ta d’auka, ajiyar zuciya ya sauke tare da kiran sunanta,

“Madre…!”

“Na’am Ma’aruf ya akayi?!”

Kwanciya ya gyara tare da lumshe idamuwa, k’irjinshi banda bugawa ba abinda yake yi da kyar ya samu yace,

“Kun k’arasa ne?!”

Madre tace “A’a muna cikin motar Ma’aruf mun kusa dai,kabi komai a hankali idan ka dawo maya magana kaji ko?!”

“Eh Madre amma bana son Sumayya taji yanzu har sai na dawo.”

Ma’aruf ya fad’a cikin sanyin murya, dariya Madre tayi cikin sanyaya rai tana shafa kan K’arama da tayi bacci tace mai.

“Toh ai ba komai sai ka dawo Allah yayi maka albarka.” Yace amin daga nan ta bama Abba shima yayi mai fatan alkaire tare da addu’ar dawowa lafiya.

Sumayya ya kira bayan sun gama waya dasu Madre, cikin kashe murya tace mai “Yaya tun d’azu nake kiranka kun k’arasa ne ka juyo?!”

“Sumayya… !” ya kira sunan ta cikin janshi, sake kashe murya tayi tana daga kwance akan doguwar kujera tace “uhmm Yaya nah.” Ma’aruf yace “ina Udatti naji ban jiyo motsinta ba ko tayi bacci ne?!”

“A’a wallahi Yaya tana wajan bala tun d’azu,wallahi ta isheni da kuk…..” Bata k’arasa ba taji ya rufeta da fad’a wanda bata tab’a jin yayi ba a rayuwarta.

“Ur not serious Sumayya,jaririyar zaki bawa me gadi ajiya? Wallahi wallahi baki da hankali ‘yarki mace wadda bata son komai ba amma baza ki iya killaceta ba sai dai ki bawa getman? Sumayya kin kasa killace ‘yarki da kanki wanene zai kular miki da ita? Idan bakije kin karb’ota ba yanzu wallahi sai ranki ya b’aci mtwwww… !

Ma’aruf yaja wani katan tsaki kai da kaji shi kasan ankai mutum mak’ura,yatsina fuska Sumayya tayi tare da gyara kwanciyarta. Bata dad’e ba sai ga Bala yayi mata sallama mik’ewa tayi tana hararar sa yayi kasa da kai tare da cewa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button