ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Wai gata inji oga.”
Sumayya ta fizgi yarinyar tare da fad’in “dallah can bani ita dama ba son rainanta kake ba mtww aikin banza kawai.”
Shi kam Bala da ya samu ta k’arb’eta sai ya sulale shima yana cewa “kut aikin banza nayi gadinku sannan a wani bani raino dan tsabar son banza da rainin wayo.” Yayi bakin get inda yake zama ya zauna yana sharce gumi.
Kwantar da yarinyar tayi ta koma d’aki ta kuma had’a mata NAN sannan ta dawo zama tayi ta dinga tura mata duk cikin haushi dan Sumayya ta tsani raino (wa iya zubillahi ace ka haifi d’a/’ya a cikin ka amma kana hantarar shi baka son hidimta mai kuma kasa ran jin kanshi a gareka gadai Udutti bata yi sa’ar uwa ba Allah ya rabamu da irin wad’annan iyayan).
Tana bata tana sha ham-ham sabida tsananin yinwar da takeji kafin wani lokaci ta shanye tayi bacci,kayan jikinta dukun-dukun kasan cewar bala kawanta da ita yayi akan tabarmar shi gata duk k’asa baya karkad’ewa amma Sumayya ko ta cire mata haka ta barta tana jin haushi wai duk akan tane bata bari sunyi waya da Yaya Ma’aruf cikin nutsuwa ba…..
{{ }}
Maitafasa na komawa gwadabniya ta fara yiwa kundum tijara wadda ita kam shiru tayi dan tasan tabbas dole sai Maitafasa tayi hakan akan b’oye mata duk wasu abubuwa dake b’oye cikin takaicin bakak’en maganar da Maitafasa ke gayawa kundum tace,
“Wuta balbal Maitafasa idan ki kuma ce min munahika, na sanki sarai a lokacin idan na sanar dake abinda ke faruwa zaki hanasu kusantar juna bayan hi ladon hine yake bid’ar Hafsatuwalle, yo banda toshewar kwakwalwa ai kinhi kowa sannin halayyar Hafsatuwalle amma kika yi mata wannan herrin sabida kinhi kowa son d’a, yo dama ni bani da d’a bare jika hiyasa na biye miki yadda kike so….!”
Kukan kura Maitafasa tayi kan Kundum nan da nan suka kaure da kukawa tamkar yara da gudu su Asibi suka shigo gidan aka b’anb’are Maitafasa daga jikin Kundum sai uban haki suke tsabar ko wacce taji jiki.
“Ta kwarankwatse Kundum kin cuceni hegiya munahuka Allah ya isa tsakanina dake algunguma aradun Allah bazan yahe miki ba….”
“Oho dai ko kina so ko bakki so K’arama jikarki ce, yo ma ai ko maitace toh ajikinki ta gada kwarankwatsa dubu ma kuwa…”
Askwane Maitafasa ta kuma yowa kan Kundum aka tare ta nan da nan ta fara surfawa Kundum zagi taba kwashe mata albarka da kyar aka samu tayi shiru amma cikin ranta ba wai hakura tayi ba sai ta yiwa Kundum abinda sai sa ta kasa bacci ranar.
{{ }}
Washe gari tunda safe Ma’aruf yaje suka yi sallama da Hakimi, kauyan su Hafsatuwalle ya biya yana zuwa suka had’u da Sallau zai fito daga gidan, gaisawa suka yi a mutunce kafin Ma’aruf yace.
“Yauwa Sallau dan Allah ko zan samu ganawa da Umman K’arama?!”
Kallonshi Sallau yayi na ‘yan lokuta yana dariya sannan yace “kwarai ma kuwa me zai hana, bari naje na shaida mata he ka higo..”
Ma’aruf ya girgiza kai alamar toh sannan Sallau ya juya dan sanarwa da Hafsatuwalle zuwan Ma’aruf, zaune ya tarar dasu ita da lauratu da inno suna karin kumallo ya gaidasu sannan ya sanar da Hafsatuwalle sakon Ma’aruf.sai da kirjinta ya buga dan ta d’auka da K’arama ya dawo cikin rawar murya Hafsatuwallen tace,
"Sallau da..da..da K'arama ya dawo?!"
Sallau ya kalli Hafsatuwalle yaji wani mugun tausayin ta na ratsa shi, tsaye ya mik’e yana cewa,
“A’a Umma shi d’aya ne yazo ai yacce min ita tayi gaba zuwa birnin su…”
Ajiyar zuciya ta sauke tare da ajiye farau-farau d’inta, wani kod’add’an hujjabin ta shi ta sanya duk yasha d’inkin zare da allura tayi kofar gida, Ma’aruf na hangota ya k’arasa wajanta suka shiga rumfar Ard’o Hafsatuwalle ta tsugunna tana niyar gaidashi. Duk da cewar a shekaru ya girmeta kawai dai auran kauye ga rayuwar wahala sai tayi kamar wata tsohowa me shekaru, da sauri Ma’aruf ya tsugunna shima suka hau gaida junansu.
“Umma dama tafiya zanyi shine na biyo muyi sallama, insha Allah zan rik’e miki Hafsat da gaskiya da amana, kuma wata rana zaki yi alfahari da ita a matsayin ‘yarki, Umma muna bukatar addu’arki, sannan ina da wata matar harda yarinta guda d’aya……”
FEEDOHM????
&
HAJJA CE????
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》
????????
????
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????
SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
Page *79*
Sunkuyar da kai Umma ta sake yi tana matsar hawaye, ya zata yi dole ta yadda domin zaman K’arama a gurin su shine mafi jin dad’inta da kwanciyar hankalinta, cikin rawar murya tace mai,
“Mun gode Ma’arufu Allah ya saka da alheri ya baku zaman lafiya da duka matan naka, nasan baka son auran K’arama dole aka yimaka kayi hakur….”
Saurin katse ta yayi ta hanyar cewa, “a’a Umma ki dena cewa haka, dama can Allah yayi Hafsat mata tace so babu yadda zanyi ki dena damun kanki.”
Mik’ewa yayi tare da zaro 10k ya ajiye mata kusa da kafarta dan yasan idan ya ce sai tasa hannu toh zasu d’auki lokaci shi kuma sauri yake dan jirgin karfe tara da rabi zai bi, da sauri yabar rumfar jin zata fara mai magiya akan kud’in daya bata,mota ya shiga drive yaja shi zuwa airport be dad’e ba jirgin su ya lula…..
Gidan Madre ya fara zuwa, yana shiga yaji tsit ba kowa a parlor sai ya nufi kitchen dan ya san ba’a raba Madre da shiga kitchen yana zuwa nan ma bata nan. Kanshi ya girgiza sannan ya nufi upstairs nan ya fara jiyo muryar Madre na waya, a hankali ya murd’a handle d’in ya bud’e ya shiga, zaune ya tarar da Madre a bakin gado waya take da Yaya Maryam tana bata labarin auran Ma’aruf da K’arama.
“Bari kawai Maryam ni kaina mamaki nake sai dai ba’a mamaki da ikon Allah,
“Oho ni kaina ban san ta inda za’a fara sanar mata ba kinsan inajin tana bawa kawayanta labari akan duk ranar da Yaya Ma’aruf yayi mata kishiya haka tace ko ita, ko shi ko amaryar sai sun bakunci lahira, bari kawai Maryam ni kaina bansan yadda zanyi da Sumayya ba bari anjima mayi wayar kin ganshi nan ya dawo…”
Katse wayar tayi tana kallonshi duk yayi wuri-wuri kamar marar gaskiya, shagwab’e fuska yayi kamar yadda yake mata idan yaga suna waya da Maryam kamar zasu cinye juna cikin halin gajiya yake fad’in,
“Madre nayi tafiya na dawo amma kinyi min banza sai biyewa ya Maryam kike ina shan wahala.”
Dariya tayi tana k’okarin bashi amsa sai ga K’arama ta shigo d’akin jikinta d’aure da towel tayo wanka kunnanta duk kumfa,kallon ta suka yi daga shi har Madre baki bud’e yayin da ita kuma tana ganin Ma’aruf ta b’oye fuska alamar kunya ta k’arasa wajan Madre tana cewa,
"Nayi wanka."
"Kinga kunnanki kuwa Hafsat? Duk kumfa sai da nace ki bari nazo nayi miki amma waike kin girma bakyaso harda ce min yanzu Udutti za'a dinga yiwa wanka gashi nan ai duk baki fita ba."
Madre ta fad’a tana janyo ta jikinta tare da d’akko cotton bud tana goge mata kumfar, K’arama kuwa bata juyo ba ta fara k’ok’arin gaida shi.
"Uncle ina kwana ina Udutti zanje wajanta."
Yana kallonta ya tab’e baki tare da cewa “ke yanzu duka-duka guda nawa kike da zaki ce an dena yi miki wanka? Lallai ma toh gashi nan duk wankan beyi kauba….”
Ba tare da ta damu ba ta kuma kallon Madre “Ina kayan da zan saka uncle ya kaini wajan Udutti…?!”
"Gasu nan akan gado."
"Wai Madre baza ki sake mata wani wankan ba..?!"
K’arama ta turo baki bata iya kallon shi ba tace, “toh ba sanda ina gidan su Udutti da kaina nake yi ba, kuma shine yanzu za’a dinga yimin,nidai bana so.”
Shareta yayi ganin ita adole a kyaleta ya kalli Madre yace “inajin yinw fa and inason zuwa gida kinsan basu san kwana zanyi ba.”
Mik’ewa Madre tayi bayan ta mik’awa K’arama wasu riga da siket na les dark blue da zanan fari-fari ajiki sannan ta fita tana cewa “gasu nan kisa kai kuma kafito dining gashi nan zan had’a maka.” Ma’aruf yace toh tare da kallon K’arama wadda ta juya tamkar wata babba tana sa kaya bayan ta rufe jikinta da towel d’in, kamar yayi shiru ya fita sai kuma yace,