ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

"Toh me kike b'oyewa haka?!"
Bata juwo ba tace mai “Toh ai kaya nake sakawa.”
“Uhmm! Shine kike wannan sunkuye-sumkuyan? Idan banda abinki nima me iya saka miki ne, any way idan kin shirya kizo sai muje gurin Udutti d’in tare….”
Yana kaiwa nan ta bar bedroom d’in yana dariya,ita kuwa K’arama tana gamawa ta fito kayan ba karamin amsarta suka yi ba nan ta nemi guri ta zauna tana jiran ya gama su tafi duk ta k’agara taga Udutti ji take kamar ta shekara basu had’uba.
Ma’aruf na kammalawa suka yiwa Madre sallama suka fito, K’arama tace “uncle toh da ka tambaye ni zan iya auranka ka aureni d’in?!” Yayi saurin kamo hannunta cikin nashi ya tsuguna sitin fuskar ta yace “lil Mom kiyi shiru kidena fad’a kar aunty Sumayya taji ta duke ki kinji ko?!” K’arama tayi kasa da kai tare da ware idanuwa tace “Toh uncle, kaga kuma danaga Yaya lauratu naga cikinta kato itama haihuwa zata yi?!” Ma’aruf ya mik’e tsaye suna tafiya yace mata “eh mana.”
Da sallama suka shiga cikin parlorn amma ba kuwa, K’arama ya kalla dake faman lek’e-lek’e yace mata “ina…” Ma’aruf be k’arasa ba ya hango Sumayya ta fito sanye cikin wasu ‘yan iskan kaya tana wani irin tafiya tamkar baza ta yi tafiya a k’asa ba.
“Oyo-yo honey.”
Sumayya ta k’arasa gurin shi tare da ware hannuwa ta tayi hugging d’inshi tana ta faman murmushi, kukan Udutti ne yasa K’arama yin cikin d’akin da gudu tana tsalle, kallan Sumayya yayi tare da cireta a jikin shi yana binta da kallo a hankali yace,
“Kinyi kyau but matsalarki d’aya baki da kunya. Sumayya be dace ace da kika fito kika ganni da yarinyar nan ki k’araso a haka ba, jifa sauran kad’an ya rage a hango pant d’in jikinki idan ma akwai…”
Ma’aruf ya fad’a yana nuna tsagar jikin dugowar rigar jikin Sumayya,tsagar da aka yiwa rigar tundaga k’asa har sama wajan kugunta kad’an ya rage ta rab’e biyu,kirjinta kuwa rabin shi a waje yake ko bra bata saka ba. Jikinta tabi da kallo tana son gano illarta, cikin shagwab’e fuska tana shafar fuskar shi tace,
“Honey ai ni bamu yi da kai zaku dawo da Hafsa ba so yanzu ma bansan da ita kuka shigo ba kuma ni ina son na burgeka ne shi yasa na k’araso.”
Ma’aruf ya kuma jan numfashe tare da kama hannuwanta suka wuce bedroom d’in shi Sumayya sai murna take yi, dama ta riga ta banki abubuwa tayi cushe-cushenta a HQ duk dan farin cikin shi, aikuwa sai da ya biye mata duk kanainaye shi tayi har sai da suka raya ranar.
Sauri yayi ya shiga wanka dan har yau gani yake kamar K’arama na ganin abubuwa idan anyi, cikin shirinshi ya fito na k’ananan kaya jar riga ce me gajiran hannu gabanta anyi rubutu ansa stay with me ya sanya blue d’in Jean’s yayi kayau sosai.
A parlor ya gansu K’arama sai wasa take wa Udutti yarinyar sai b’angula dariya take tana cilla kafafuwa, murmushi yayi ya k’arasa wajan yarinya d’aukar ta yayi a kan cinyar shi ya d’aura ta ita kuma K’arama tayi saurin komawa kusa dashi ta zauna tana wasa da yatsun hannuta,
"Lil Mom yanzu dai kinga Udutti sai ki tashi na maidake wajan Madre..."
Had’e rai tayi tana turo baki batayi magana ba, mik’ewa yayi tsayi tare da cewa,
“Oya tashi kisa hijjab mu tafi sauri nake yi zani wani guri.”
“Uncle ni kabar ni anan nafi son nan gidan wajan Udutti..”
K’arama tayi maganar kamar zata yi kuka dan bata son rabuwa da yarinyar,ganin haka yasa shi mik’ewa tsaye yarinyar ya bata ya juwa ya tafi yana cewa,
"Sha zaman ki lil Mom nan da can duk d'aya ne..."
Wasan ta cigaba dayi mata sai dariya take yi, Sumayya kuwa bata fito ba bacci taci gaba dayi ko wankan ma bata yi ba har Ma’aruf ya dawo wajan karfe 2:30pm, a kwance ya tarar da K’arama k’asan center carpet tayi shiru daga gani gajiya tayi da wasan gefenta Udutti ce keyin bacci hankali kwance, k’arasawa yayi gurinta tana ganin shi tayi saurin mik’ewa zaune tayi k’as da kanta tare da kamo kafar Udutti tana wasa dashi.
"Lil Mom ina auntyn taki take?!"
Shiru K’arama tayi bata yi magana ba ya sake cewa,
“kunci abinci kuwa?!”
K’arama ta girgiza mai kai alamar a’a,mamaki ne ya kamashi direct ya wuce bedroom d’in Sumayya bata ciki ya wuce nashi kwance ya hangeta yadda ya barta haka ya dawo ya tarar da ita wani kolulun takaici ya tsaya mai a makoshi ya k’arasa cikin takaici ya daka mata wata uwar tsawa wadda tasa Sumayya tashi da sauri cikin razani.
“Sumayya wai me kika d’auki aure ne hmm? Kin d’auki aure a matsayin kawai mu kwanta tare duk sanda muke so, baki son cinaba bare shana, Sumayya kinfa haihu yanzu kin zama uwa Udutti tana bukatar kulawarki da tattalinki tarbiyarki ta yadda nan gaba zata ji kanki tayi alfahari dake amma itama baki damu da itaba bayan ke kika haifeta da cikinki a haka kike son nuna min so? You don’t know how to take good care to my child, yanzu kinsan lil Hafsat na gidan nan tana miki raino amma daga ita har ‘yar taki baki san halin da suke ciki ba, toh ki fita kiji ki samar mata wani abun taci…”
Parlor ya koma yana zuwa ya tarar itama K’arama tayi bacci ta manne jikin Udutti, kitchen ya wuce ya dudduba yaga a kwai komai na kayan abinci amma kullum sai dai tayi musu indomei da rana kuma wake da shinkafa, parlor ya koma yana aikin shi cikin laptop cikin shigar English wears ta fito har lokacin haushin fad’an da yayi mata take hakan yasa ta wuce bata kula shiba shima ya shareta.
Kamar ya sani indomie ta dafa ta zubo cikin plate biyu ta kawo parlor, kai da kaga indomie d’in kasan zata yi yaji sabida attaruhun dake cikinta, k’asa ya sauka yana tashin K’arama dan yasan yinwa ce ta sanyata bacci, tashi tayi taje ta wanke baki sannan ta dawo tana cin abincin.
Sumayya ta kawo musu nasu spoon d’aya yaci yature sabida tsabar yaji shi kuma baya son shi, ko ta tambaye shi dalilin da yasa shi kinci kawai ta gyara zaman plate d’in gabanta ta ci gaba da ci, jifi-jifi yana kallon K’arama tana ci tana sharar majina ga ido fal hawaye sabida yaji.
"Lil Mom zaki iya ci kuwa?!
Ya fad’a yana kallon K’arama, tana ci tana bashi amasa, “Eh uncle zan iya.” Kai ya kad’a ya koma yaci gaba da aikin shi duk kuwa da cewar shima yanajin yinwar….
Ana kiran sallar la’asar yabar gidan be dawo ba sai dayayi sallan isha’i, a parlor ya tarar da K’arama goye da Udutti sai faman jijjigata take yi kallon ta yayi tare da bin parlorn da kallo be ga Sumayya ba yace,
“Lil Mom ina auntyn ki take?!”
Kanta a kasa tace mai “suna bedroom d’inta.” Ya kad’ai kai sannan yace “kinyi sallah ko?!”
"A'a."
Ta fad’a sai faman jijiga yarinyar take ita kuma tana waka irinta yara idan ana jijigasu zasu yi bacci,
"Subhanallahi garin yayi aka yi haka baki yi ba?!"
K’arama kamar zata yi kuka sabida yawan tambayar shi tace “ai aunty Sumayyan ce bata fito ba kuna Udutti idan na tafi kuka zata yi fa.”
Zama yayi yana mik’a mata hannunshi yace, “oya kawo ta nan kije kiyi sallah kafin Allah ya konaki da wuta.”
Da sauri taje ta mik’a mishi ita kuma tayi hanyar bedroom d’in da yake a matsayin nata sai da ta kusa shiga ta juyo tana kallon shi tace mai,
“Sallah biyu zanyi ko?!”
Ma’aruf ya kalleta yace “Eh magriba da isha’i sannan kiyi addu’a.”
Shigewa tayi bata jima ba sai gata ta dawo wai ta idar, suna zaune yana tambayar ta yadda tayi sallar su Sumayya suka fita ya kallesu ya watsar yana ci gaba da nunawa K’arama yadda ake yin sallah.
"Ina yini Yaya Ma'aruf?!"
Cewar beeba tana murmushi k’asa k’asa tanajin wani abu na fisgarta game dashi, ko kulasu be yiba suka wuce beeba ranta a b’ace suna zuwa compound tace,
"Kawata wannan mijin naki miskilancin shi yayi yawa, any way ni kinga tafiya ta."
Sumayya tayi saurin riko hannun beeba cikin sanyin murya tace “sorry kinsan shi besan hud’a da mata sai ni kawai kuma kema dan dai besan godun mawar da kike bayar wa bane amma zan sanar mai kiyi hakuri dai.”