ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Lauratu tace “amin Umma…..”
[[ ]] [[ ]]
*G*wadabniya *!*.... Sunan dake yi mishi yawo a cikin brain d'inshi kenan, mtww ya saki tsaki yafi sau ashirin ko sunan ya tuna ranshi 6aci yake baran tana idan ya tunu cewar shine zashi can d'in....,
"Ma'aruf ya dai lafiya ko?" Madre ta tambaya bayan ta shigo cikin parlorn daga gani itama daga wajan aiki ta dawo.
"Madre gobe zanyi tafiya zuwa katsina kan wani case da zanje nayi solving d'in shi..."
“Shine Ma’aruf ka zauna kanata faman 6acin rai kai d’aya?” Madre ke fad’in haka tana kokarin zama cikin d’aya daga kujerun da suka k’awata d’akin.
Shiru Ma’aruf yayi yana turo baki ya k’i kuma had’a Ido da ita Madre ta girgiza kai da mamakin shi cikin zuciyar ta tace.
"To ka tashi kaje ka shirya mana ka zauna sai tunani kawai kake yi. Flight d'in nawa zaka bi..?"
A harzuk’e ya tashi tsaye fuskar shi a d’aure ya ce mata “Madre 8:00am.” Yana fad’a be jiraci cewar ta ba yabar parlorn kamar zai tashi sama wajan fita suka yi karo da Sumayya amma ko ta kanta be biba ya wuce part d’inshi.
Bedroom ya wuce ya fa fad’a kan bed tare da rik’e kanshi me barazanar tsagewa sabida tsabar sara mishi da yake yi. Ya kusa 2hours a kwance kafin ya tashi ya koma dressing room ya fara shirya kayan shi. Har aka kira magrib sannan yayi alwala ya wuce masallaci dan gabatar da sallah, ana idarwa ya koma side d’inshi ya ci gaba da shiryawa har ya kammala ya koma parlorn shi ya zauna yana jin tsanar zuwa kauyan.
"Yaya Ma'aruf Madre na kiranka." Sumayya ta fad'a cikin d'ar-d'ar tana kallon shi. "A'm coming."
Yace da ita ba tare da ya kalleta ba, kura mishi idanuwa tayi cike da tambayoyi uwa uba kaunar shi da soyayyar shi dake addabar rayuwarta ya d’ago tare da sauke mata uwar harara ta juya da gudu tabar d’akin.
Ko 2minit bata yiba sai gashi, zama yayi Madre ta dube shi tace, “kazo kayi denner Ma’aruf.” Lokacin abban shi ya shigo duk suka yi welcoming nashi kafin suka wuce dining gaba d’aya.
Tsakurar abincin kawai yake kafin yace “Abba gobe zan wuce katsina akan mai Apf d’in nan by 8:00am jirgin zai tashi.”
“Good my son, Allah ya bada sa’a I know my son is a nice musamman akan aikin shi, Allah ya baka sa’a my son.”
Madre da Ma’aruf suka had’a baki wajan cewa “amin…” Sumayya ta saci kallon shi suka had’a ido ta sakar mai kayataccen murmushi ya harareta tare da mikewa yace ya koshi sannan yabar side d’in zuwa nashi.
Washe gari yana gama shiryawa wajan 7:00am ya fito dan tafiya airport cikin shigar shi ta suit milk color abinka da beauty sai yayi bala’in kyau. Room din Abba ya shiga tare suka fito suka had’o da Madre a kitchen ta fito hannunta rik’e da wata kyakyawar leda ta mika mai suka rakoshi har inda drive ke jiranshi suna ta mai fatan alkairi da samun nasara, jiyayi tamkar karya tafi ya barsu amma Abba ya karfafa mai gwaiwa suna d’aga mai hannu har suka bar compound d’in.
Sumayya kam bata san ya tafi ba sabida tsabar baccin da take yi, sai da ta farka wajan 11:15am sannan take tambaya Madre tace “ya tafi kilama sun sauka yanzu…..”
FEEDOHM��
&
HAJJA CE������ ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》
����
��
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM��
&
K.A.S Precious HAJJA CE��
SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
page 11-12
Tunda asuba Lauratu ta tashi fita tsakar gida ta iske Jummai na surfen geron da za’ayi karin kumallo dashi yau “Gwaggo jumma Ina kwana?ta fada tare da dukawa har kasa
Yatsina fuska tayi tare da tabe wargajejen bakinta sannan tace “Lahiya”
Mikewa Lauratun tayi ta nufi murhu ta debo kakare ta hada wuta sannan ta dauki tukunya ta nufi randa zata debi ruwa……
Da Sauri jummai ta matso tana fadin “Ke ke tsaya ruwan me zaki diba kuma?
“Ummana zan daurawa ruwan wanka……”
Wani kallo ta watsa mata sannan tace “To bada ruwan gidan nan ba wallahi don babu shegen da yace ta haihu acikin mu……”
“Haba Gwaggo Jumma tunda fa ta haihu batayi wanka ba ,dan Allah ki sammani na diba ko ya yane ta samu taji karfin jikinta “ta karashe maganar tana kallon kasa idanunta cike da kwallah……
“Kar ta ji karfin jikinta lauratu!idan abun ya dameki kije ki debo mata a rafi mana ina jin kinsan inda zaki debo mata!Muma mazajenmu suka debo mana don muyi amfani dasu ba dan ayiwa Shegiya wanka ba……!ta karashe maganar tana tada jijiyoyin wuya
Juyawa tayi ta dauki tulu ta fita ba tare da tace komae ba sae dae zuciyarta dake tafasa kamar ta kone……Da tsaki Jummai ta raka tana fadin “Shegu masu abun kunya”
Cikin Sauri ta debo ruwan ta dawo ta sake hada wata wutar har sae da sukayi zafi sannan ta leka bangaren Inno ta aro katuwar ruba ta juye rabi……
Sauran kuma ta zuba a bokiti ta kai ban daki……
Jaririyar ta amsa daga hannu Umman tace “Umma ki tashi kije kiyi wankan na kai maki ruwa a bandaki……”
A Hankali tace “Nagode ……”sannan ta mike ta fita tayo nata wankan……Jaririyar ta saka cikin ruwan ta gasata sossa……
Tana gama mata wankan ta ladeta cikin kallabinta tana kallonta ,Tausayin yarinya ya kamata sosae ganin ko Dan kamfai bata dashi,Daukarta tayi ta goya sannan ta fita daga gidan……
Gidan mai unguwa ta shiga ta tambaya ko akwae Surfe,Cikin sa’a suka bata masara tiya goma suka ce a surfa zasuyi tuwon sadaka da ita ……
Haka ta ja masaran ta koma gida lokacin mutanen gidan sae karin kumallo suke ,Bukkarsu ta nufa ta iske Umman a zaune ba’a kawo mata komae ba ,hawaye taji suna niyyar zubo mata ta fita da sauri tana tambayar Jummai ina abun karin kumallon su……
Matan gidan suka dauki sowa suna fadin “Ashe har abinci gareku bayan abun kunyar da kuka dauko mana “
Wata ta amshe da fadin “Shi kwarton uwar taki bai kawo maku komae ba?ko bai san ta haihe mashi diya ba ?
Jummai ta amshe da fadin “Ke nifa ban yarda da yadda Ard’o ya k’irba yarinyar nan ba! don wallahi kadan yake saka tabaryar a ciki ko diyar bata tabawa”
“Nima wallahi abunda nake son fada kenan,kawae raina mana wayau yayi don ya fahimci shegiya ce……”
Inno dake tsaye tana jinsu ta kira lauratu ta mika mata nata abun karin kumallon ta juya a sanyaye ta koma dakinta ……
Lauratu kam Umma ta kaiwa abun karin kumallon ta juya zata fita ta kira ta tace tazo ta zauna taci ……
Duk da irin yunwar da take ji murmushi tayi tace “Nasha nawa Umma”
Ta dade tana kallonta sannan ta gyada mata kai tana share hawayen da suka zubo mata ,Da sauri lauratun ta fita ta fara surfan masarar ……
Kafin rana ta take ta gama surfewa har an bata kudinta naira d’ari ……Jaririyar ta kwanto tana fadin “Umma ki bata abinci yanzu zan fita da ita……”
Cikin sanyin jiki tace “Ina zaku je Lauratu?
“Umma dan kamfai zan sawo mata da riga a Gwadabniya nan garin ba’a siyarwa……”
“Ina kika samu kudi?
“Umma surfe nayi yanzu”ta fada tana rike kafar Jaririyar……
Shiru tayi tana kallonta har sae da jaririyar ta dauke kai daga MaMan sanna lauratun ta dauketa suka tafi……
【】
Ma’aruf yana isowa aka bashi Guard mace sannan suka nufi Ward din cikin HLuxur……,Focal person suka dauka sannan suka nufi Gwadabniya……Ganin yarda suke keta daji ya sashi sakin tsaki lokaci lokaci ,Bai taba tunanin akwae mutanen da ke rayuwa ba a wannan dajin ……
Saukin suma Hluxury ce ba’a cika gane wahalar tafiya da ita ba don bata raina tudu da gangare ……
Gidan Mai unguwa suka sauka Ma’aruf na cikin motar bai fito ba .Mai unguwar ya leko yana washe jajjayen hakoranshi ,daga mashi hannu kawae yayi sannan ya bude motar ya fito Guard dinshi na a bayanshi……
Gidn Malan Lado suka nufa tare da dandazon yaron da suka zagayesu……Har cikin bukkar ya Shiga ya dubashi sannan ya fito yana karewa ilahirin mutanen dake gidan kallo ……
Uban wari ke fita ta ko’ina ga ruwan da ya kwanta tsakar gida ……Dan karamin tsaki ya sake ja lokacin da Maitafasa ta iso gabanshi tana fadin “Yaro yaya kaga jikin nashi?dan Allah ku taimaka ya warke ko ya dauki Fansa a kan cin amanar da matarshi ta mashi ……”