ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Beeba ta fizgi hannunta tayi gaba abunta itama Sumayya ta koma ciki tana ta b’acin rai wai yayi wa kawarta wulakanci…….
FEEDOHM????
&
HAJJA CE????
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》
????????
????
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????
SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
Page *81*
Wayar shi ya ciro daga aljihun gaban rigar shi gallery ya shiga ya zubawa wani hotanta ido tamkar yana photocopy d’in shi,shafar screen d’in yayi yana sauk’e ajiyar zuciya a hankali, yafi minta talatin zaune cikin motar yana kallon hotan kafin daga bisani ya rufe wayan ya ajiye tare da fizgar motar yayi hanyar komawa gidan Madre.
Yana shiga wani wrong parking yayi ya nufi cikin parlorn zaune ya gansu a kan kujera mai cin mutum uku gefe da gefe Bassam ne da BarraQ tsakiya kuma K’arama ce tayi shiru tana kallon face d’in phone d’in hannunta, a k’asa kuma a gaban su ikram ce da inteesar suna ta hira dasu zuciyar Ma’aruf ta sake sark’ewa a fusace yama manta dasu Madre a zaune a parlor cikin tsawa yace,
“Your very stupid! Kin tashi anan ko sai na 6allaki, sannan ki d’auki mayafinki ki wuce muje ga aunty d’inki can ashe test zata miki shine baki fad’a ba kika biyo mu…!”
K’arama jiki na karkarwa ta kasa gane inda maganar Yaya Ma’aruf d’in ta nufa ciki rawar murya zata yi magana ya sake had’e rai tare da nuna mata hanyar fita yace,
“Get out or else…!”
Da sauri kamar zata kifa tabar wajan tana matse idanuwa Madre ta kalleshi da mamaki itama a fuskarta tace,
"Ma'aruf ya haka ne! Kwanan nan fa naga ka fara d'aukar zafi abu kad'an ka maidashi babba musamman idan laifin Hafsat ne, shin wani abun tayi maka da zaka dinga yiwa yarinyar mutane tsawa da fad'a?!"
Shiru Ma’aruf yayi tare da rintsa idanuwa ji yake tamkar azo ayi mai dukan tsiya dan yadda zuciyar shi ke turiri, ko samun damar magana beyi ba kawai ya juya yabi bayan K’arama, kafin ya fito har taje gidan sabida gudu tayi dan karma ya tarar da ita wani abun ya biyo baya. A tsaye ya ganta tana dube-duben inda zata hango aunty d’in amma bata ganta ba sai shi daya nufota k’irjinta ya sake bugawa tayi saurin yin baya yazo ya bud’e tashiga.
Suna shiga ciki da sauri Ma’aruf ya janyo K’arama, a cikin k’irjin shi ya sata tare da matseta tamkar zai tsaga kirjin shi ya zura ta, ganin haka ne yasa K’arama sakin kuka yadda bazai jita ba yayin da jikinta ya hau rawa kafafuwan ta suka fara yin sanyi tana neman fad’uwa. Shi kam Ma’aruf ajiyar zuciya kawai yake sauke wa yana shafar kanta a hankali, ya dad’e a haka lafin ya d’ago fuskarta yana kallonta, nan yaga tayi shab’e-shab’e da hawaye jikin shi yayi sanyi ya tallafo hab’ar ta idonta a lumshe cikin sanyin murya yace,
“Lil Mommah why bakya jin magana ta ah? Ko ban isa da keba ne?!”
Bata bud’e idanta ba a haka ta girgiza mai kanta alamar a’a sannan ya kuma kura mata idanuwa musamman lips d’inta wanda take ta faman tsukewa tana tsotsar su yayi saurin tureta daga jikin shi. Tafiya ya fara yi ita kuma tana tsaye a inda ya barta dan har lokacin tsoro ne fal a zuciyarta uncle Ma’aruf ya sauya sosai gashi ta kasa gane inda ya dosa.
Zama yayi akan d’aya daga cikin kujerun parlon jin bata taho ba yasa shi jiyawa yana kallonta,kanta a k’asa tana wasa da k’asan rigarta cikin kasalalliyar murya yace mata,
“Come here Momma…!”
K’arama taji ya fad’a ya kuma juyar da kanshi yana facing t.v, k’arasawa tayi tare da rakub’ewa jikin kujera sai faman sauk’e ajiyar zuciya take, kusa dashi ya muna mata yace,
“Dawo nan tambayar ki zanyi.”
A d’add’are ta tashi kusa dashi ta zauna tamkar za’a ce mata kulle tace cass, hannunta ya kamo yana matsawa a hankali jikin K’arama ya hau rawa sai faman raba idanuwa take yi murya a slow yace.
"Lil Mommah so kike yi na mutu ne."
Da sauri K’arama ta zaro ido tana faman girgiza mai kai cikin tashin hankali, d’ayan hannunta wanda be rik’e ba tasa tana goge kwallar data zubo mata shi kuwa kallonta kawai yake yi soyayyar ta na k’ara azabtar dashi share hawayen tayi sannan tace,
“Uncle menayi?!”
Kamar ya sanar mata gaskiyar ABIN DAKE B’OYE sai kuma ya kad’a kai tare da sakin hannunta, a hankali ta d’ago tana kallon shi suka had’a ido tayi saurin mayar da nata k’asa tana saukar da ajiyar zuciya alamun tayi kuka,
“Uncle ina aunty chegozie d’in, kuma ni wallahi ban san zamu yi test ba bata gaya minba uncle.kuma k’ila mantawa tayi ai yau Sunday kaga bata zuwa sabida tana zuwa church….”
Kwantaccen gashin bakin shi Ma’aruf ya shafa cikin basarwa ba tare da ya kalleta ba yace,
“Eh bata zoba ban san me zance ba shi yasa na fad’i hakan kin wani zauna cikin tsakiyar garadan maza kun manne da juna, toh ni ba irin tarbiyar da nayi alk’awari zan baki ba,
Lil Mommah nasha sanar dake bana son in dinga ganin kina mu’amula da ko wanne namiji, ke ko malaman ku tsakaninki dasu shine su koya miki ko tsawaita yin questions bana son kina musu ko kuma yawan basu amsa idan sunyi muku questions…”
Waro idanuwa K’arama tayi cikin tsananin mamakin Ma’aruf, baki ta toshe da tafin hannunta domin bata ma san abinda zata gaya mai ba, haka suka zauna yana ta janta da hira har dare lokacin da su Sumayya suka dawo, tare suka zo dasu ikram dan anan zasu kwana wajan K’arama koda suka dawo Sumayya bata tambaya ba ko K’arama tayi test d’in sabida ita ‘yar I don’t care ce….
{{ }}
“Iyyyirrrrrrrr! Ahayyyyye!! Nanayeeee!!! Aradun Allah ko duk jikina kunne ne bani yadda da maganar ki Maitafasa, yo kin manta wacece Kundum ne kika zauna kina shirga min wannan uwar karyar?!”
Kundum ta fad’a tana gantsaro bayanta yayin da Maitafasa ta d’auki buta tayi makewayi ba tare da tace komai ba, tana fitowa taga su Asibi da lanto dasu buwale can sai ga baraka itama ta shigo Maitafasa ta fice majina da gefen zani ta k’arasa inda suke zaune da izgilanci tace musu,
“Ku kuma fa haka waya sanar daku cewar na mutu da zaku zo kuna zaman makoki…?!”
Bawale ce tace “haba Maitafasa wane irin makoki kuma muda muka zo miki sannu da dawowa.” Lanto ta d’ora da cewa “ke kam dai kin samu sa’a ana ta nemanki a birni kakarki ta yanke…”
Maitafasa ta kuma fece majina da gefen zaninta, goro ta b’alla taci sannan ta kalle su tace,
“Kunjini da munahika Kundum, aradun Allah nasan irin zaman da zan ringa yi da ita wai daga fad’i mata cewar Hakimi na sona shine ta fara ruwan masifa har da cewa k’arya nake yi! Yo tallahin Allah banda na taka mai birki da sai dai kuji zance a gidajen radio…. !“
Gabaki d’ayan su babu wacce bata razana ba jin furucin Maitafasa, ita kam ta fad’a ta maze tamkar da gaske takeyi nan ta fito da dubu uku tana k’irgawa da wadda Ma’aruf ya bata da kuma wadda ta samu a bakin tasha sai wadda ta tsinta a kofar gidan Hakimi ta dawo a kafa batare da tahawo mashin ba, kallon da taga suna yi mata ne yasa ta cewa.
“Aradu kunga kud’in nan! Toh hine ya bani su wai naci goro kuma ni kwarankwatsa dubu bani auran shi tsofai-tsofai dani… !“
Jikin kundum ne yayi sanyi lokacin da taga kud’in tasan lallai da gaske Maitafasa takeyi dan idan ba haka ba babu inda zata iya samun wad’an nan kud’ad’an masu yawa.
“Aradu da kin sani kin yadda.”
Asibi ta fad’a tana rik’e hab’a Kundum kam bata k’arayin magana ba Maitafasa tace,
“A’a bani yin amre a hekaruna gara kam nayi zamana ni d’aya tunda dai babu lado na uban kowa ma ya mutu aradu.”
“Ni kam dama zai kira ni tallahi ba abinda zai hanani amran Hakimi… !“