ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Hehehe wi! Yo an gaya muku hakan nan nake he yasan abin da ya gani jikkina yace iya sona kundai son ba irin mu d’aya ba ahh toh…”

Sake-sake Kundum keyi ta yadda zata gano asalin gaskiya duk da cewar zuciyar ta neman yadda take da zancen Maitafasa. Haka suka ci gaba da zama kullum burin Maitafasa ta kuntatawa Kundum ita kuma tayi tayi takasa gano al’amarin dake tsakanin Hakimi da Maitafasa kasan cewar bata da hanyar da zata ji wani labari daga cikin gidan hakimi…….


“Sannu kinji lauratu Allah ya saukeki lahiya wannan abu yana baki wahala aradu..”

Murmushi kawai lauratu tayi ba tare da tace komai ba bare ta amsa addu’ar da inno kiyi mata sabida tsananin kunya da kawaici. Hafsatuwalle ce ta shigo cikin rumfar zama tayi a can gefe tare da d’aukar gyad’a me b’awo tana b’arewa, inno ce ta kalleta tana fad’in.

“Kunyi magana ne da Ard’o?!”

Hafsatuwalle ta kad’a kai alamar a’a sannan ta kalli inno tace “inno lahiya dai ko inci ba wani laihin nayi ba…??!”

“Baki komai ba, dama batun kud’in sadakin K’arama ne kiga suna da yawa hene yace ko shanu za’a siya mata he a kiwata mata anan..”

Shiru Hafsatuwalle ta kuma yi dama inno tasan ba magana zata yi ba dan haka ta d’ora da cewa,

“Nace mihi a siya dan haka he kiyi tasa musu alheri har Allah yasa itama tazo taga abubuwanta…”

Bata sake cewa komai ba suka ci gaba da hira har lokacin d’ora sanwa yayi kowa ya mik’e dan gabatar da nashi uzurin, haka rayuwar su ta ci gaba da tafiya yau da dad’i gobe babu har tsawan shekar masu d’an yawa…..

{{ }}

Yana zaune a cikin office aiki ne sosai a gaban shi kasan cewar kwana biyu baya nan yayi tafiya zuwa k’asar Cairo, files ne da yawa yana ta faman dubawa wayar shi ce tayi ringing sai da ya mulu sannan ya d’auki wayan, sunan Sumayya ya gani ya d’aga ba tare da yayi magana ba. Muryar K’arama ce ta doki cikin kunnan shi hankali a tashe, da sauri ya fara tambayar ta shima cikin tashin hankali.

“Uncle! Uncle aunty ce gata nan tana kuka watak’il haihuwa zata yi, uncle ka taho dan Allah karta mutu… !

“Okk wait gani nan zuwa ki zauna a wajanta kinji ko.?!”

“Toh.”

Da sauri ya fito daga office d’in parking lot ya nufa mutane sai magana suke mai amma yak’i tsayawa da gudu yaja motar sai gida, yana zuwa upstairs ya nufa da gudu nan ya ga Sumayya a duk’e sai faman yarfa hannuwa take yayin da K’arama ke zaune a gabanta kamar me neman gafara sai kuka take yi itama, k’arasawa yayi tare da rungumo Sumayyan ya mik’ar da ita, kallon K’arama yayi tare da cewa,

“Oya ki ciro kayan baby da nata ku biyo mu hospital yanzun nan keda drive.”

Fita suka yi yayin da K’arama ta nufi inda kayan baby suke ta fara d’ebowa tana sawa cikin wata jaka shi kuwa direct asibiti suka wuce, suna zuwa aka shiga da Sumayya labour room. Ta jigata sosai gashi haihuwa tazo amma ta kasa yi da kanta sabida wajan a tsuke yake dole wannan karan ma aka sanar da Ma’aruf sai ya sa hannu anyi mata aiki dan ceto rayuwar su ita da babyn.

Dole Ma’aruf yayi sign aka shiga da ita, successfully aka yi aikin tare da ciro mata kyakyawan baby boy d’inta sai dai idonshi guda d’aya ya samu matsala dan wani abune ya tattare gurin yayi kamar shuri, Abba ne da Madre dashi Ma’aruf d’in suka shiga ciki nan suka ga yaron wanda shima sai anyi mai aiki an yanke abun.

“Toh likita ina ita mahaifiyar yaron take?!”

Abba ya tambaya yana kallon doctor Al’ameen, furzar da iska yayi tare da fad’in,

“Sorry Alhaji itama tana bukatar yin wani operation d’in co’s akwai problem a gefen mararta wanda hakan yana faruwa ne ta sanadiyar shan magunguna da yawa musamman idan mace nada ciki shima babyn abinda yayi affecting d’inshi kenan… !

“Kinji ko Madre na gaya miki yarinyar nan bata jin magana, yanzu jibi ta lahanta min yaro na ta kuma janyowa kanta larura biyu a jikinta mtwww..!”

Ma’aruf yaja wani dogwan tsaki tare da fita a cikin room d’in, a reception yaga K’arama da Udutti zaune sunyi kalar tausayi, ko magana beyi musu ba ya wuce gurin mota tare da bud’ewa ya shiga ya zauna bayan ya kifa kanshi jikin steering.

"Udut ina zuwa bari naje wajan uncle na dawo."

Jakar kayan ta tura kusa da kafar Udutti sannan ita kuma ta wuce wajan motar da Ma’aruf ke ciki, saidata kwankwasa kafin ta bud’e ta shiga. Ma’aruf kam be d’ago ba bare yasan ko waye sai muryar ta yaji tana kiran sunan shi, kasa amsa mata yayi illa kawai yana sauraronta ganin haka yasa K’arama cewa.

“Bunkul me aka yi maka?!”

Da sauri ya d’ago yana kallonta cike da mamakin jin sunan shi da ta kira wanda ada shine sunan da take ce mai, k’asa tayi da kanta tana wasa da yatsunta…….

Ana tare masoya

hajjafeedohm lvs u

FEEDOHM????
&
HAJJA CE????
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》

               ????????
                  ????

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????

SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu

INA kike ya hajja Fatee?! Here is your page, kiyi hakuri munyi iya yin mu wajan ganin anyi da yawa abun ya cutura but we promise you next page sai kin gaji da read more…????????????

 Page *82*


 "Mommah said it again please...."

Shiru tayi tana ci gaba da wasan da take yi da hijjab d’in jikinta, komawa yayi yajingina jikin kujera da bayan shi tunani yake yi kala-kala ganin haka yasa K’arama sake maida kanta tana kallon shi cikin sanyin maganarta ta kuma cewa,

“Bunkul me aka yi maka, ko bata haihuba ne?!”

Wani sakaran murmushi yayi na gefen baki tare da numfasawa, ba karamin dad’in jin sunan yayi ba a bakinta. Tada motar yayi tare da figarta suka fita daga cikin hospital d’in, kallon shi tayi cike da mamaki cikin rawar murya take cewa.

“Uncle ban sauka bafa dani ka taho.”

K’in kulata yayi har suka k’arasa gida yayi horn me gadi ya bud’e shiga yayi ciki yana yin parking ya fito tare cikin kallonta yace,

“Biyo ni.”

Kamar jela haka ta bishi suka shiga cikin parlor, kamar rakumi da akala haka ta dinga binshi jikinta a d’ari-d’ari tana tsoran ko yauma wani laifin tayi mai ba tare da saninta ba, hannunta ya kama yana zanta zuwa ciki a mugun tashin hankali K’arama ta fara magana.

“Dan Allah uncle kayi hakuri wallahi yau babu wanda na kula dan…”

Bata k’arasa ba taji ya matseta a jikin shi tare da d’ago fuskarta bakin shi ya zura a cikin nata ya fara tsotsa tamkar mejin yinwar shi(toh waya sani tunda ya dad’e yana b’oye son yin hakan)Lol.

Ya kusa one hour yana abu d’aya wanda har ya kaisu ga zubewa a k’asan tail’s d’in parlorn, K’arama kuwa kuka ta dinga yi mai bayan ya sake ta komawa gefe tayi tana kuka harda birgima tamkar k’aramar yarinyar shi kuwa kasa motsi yayi shi yasa be hanata kukan ba can yaji cikin kukan ta wanda ke k’ara bugar mai da zuciya yaji tana cewa,

“Uncle me yasa kake son lalata min rayuwa ta bayan kasan cewar rayuwar tawa tana hannun Allah tana gurinka? Uncle dama wannan dalilin ne yasa ka hanamin kula ko wane d’a namiji sai kai? Uncle dama irin tarbiyar da ka zab’a min kenan shi yasa ka haramta duk wani mutum indai namiji ne…?!”

Shiru yayi mata yanajin kukanta tamkar saukar ruwan dalma a cikin zuciyar shi, afusace ta mik’e tsaye tana hawaye tare da goge majina da bayan hannunta cikin tsananin kuka wanda yasa maganar tata fitowa a hankali take cewa,

“Uncle why?!”

Cikin sanyin jiki ga wata masifaffiyar kaunarta na k’ara wulakantar da zuciyar shi Ma’aruf yace,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button