ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Enough Hafsat enough please! Ya kike neman haramta halal kike neman dilmiyar da zuciyata cikin kunci da damu bayan wanda nake ciki yanzu? Idan baki saniba yau ki sani Hafsat you are belong to me yes I mean ni d’aya nine naki kuma ZAN RAYU DAKE koda kuwa bakya so, sannan ke mallaki nace nini kad’ai domin kuwa ni mijinki ne…!”

“Uncle wait! Wait! me yasa kake neman halattawa kanka abunda ya haramta a gareka? Kai nake gani a madadin mahaifina, Allah gatana kaine jigona uncle me nayi maka da na cancanci wannan hukunci? Dan Allah idan mafarki kake uncle ka temakamin ka farka ko zuciyata zata wanke min zargin da nake yi akan ka ayanzu dan Allah….!”

Tayi maganar cikin rushewa da kuka, daga bakin k’ofa suka jiyo muryar Yaya Maryam tana cewa,

“Wacce irin magana nake ji haka K’arama! Uncle d’in naki kike gayawa wannan maganar?!”

Daga can bayan K’arama Ma’aruf ne yake ta faman girgizawa Yaya Maryam kai alamar karta tona mai ABIN DAKE B’OYE banza tayi mai ta ci gaba da maganarta tana nufowa wajan da K’arama ke a tsaye tare da kamo kafad’unta duka biyun tace.

“Ki dena zargin uncle d’inki akan duk abinda zai yi miki domin bazai tab’a wulakantaki ko tuzarta ki, kiyi mai biyayya akan duk abinda ya umarceki akai domin bazai cuceki ba kinji?!”

Shiru K’arama tayi domin ta kasa amsawa taya dan yana marik’in ta za’a ce ta tsaya yayi mata duk abinda yaga dama bayan tasan ilar hakan da kuma harramcin shi cikin addininta ba zai yiwu ba hakan yasa ta fara girgiza kai tana k’ok’arin zame jikinta daga rik’on da Yaya Maryam tayi mata.

Ma’aruf kuwa guri ya samu ya zauna tare da kama kanshi ya rik’e yasan yau asirin shi wajan K’arama ya gama tonuwa tunda Yaya Maryam tazo. Ganin yadda duk ta rud’e ne yasa Maryam saurin yin murmushi tana kallon K’arama tace,

"Kiyi hakuri wannan abun daya faru tsakaninku shirine, mumuka shirya yin hakan nida uncle d'inki akan ya gwadaki ko zaki iya biyewa samarin zamanin nan kinsan uncle d'inki da rashin yadda da maza."

Ajiyar zuciya Ma’aruf ya sauk’e jin abinda Yaya Maryam ta fad’a samun kanshi yayi dajin dad’i ganin bata fad’i gsskiya ba, K’arama kam kunya ce ta rufe ta sunkuyar da kanta tayi tanajin kunyar uncle Ma’aruf d’in Yaya Maryam taja hannunta suka nufi inda yake a kunyace tace,

   "Uncle sorry."

Satar kallon yaya Maryam yayi ta girgiza mai kai alamar yaja aji, aikuwa yayi shiru tare da mik’ewa tsaye yana gyara hannun rigar shi, kallon Yaya Maryam ya kuma yi tare da cewa,

“Sister mu koma hospital d’in nan ko?!”

Yaya Maryam ta kad’a kai alamar toh sannan tayi waje tana jiran su, a hankali ya k’arasa wajan da take a tsugunne d’ago ta yayi ji yake tamkar ya sake rungumeta amma gudun karta fassarashi yasa ya kama hannunta suka fita kanta a kasa ita kam bata ga abinda suka zo yi gidan ba sai ma tashin hankali.

Mota suka shiga suka koma asibitin sanda sukaje an shiga da babyn cikin teater room, ita kuma Sumayya an barta sai ta d’an huta za’ayi mata, gabaki d’aya ta shiga damuwa kuka kawai take yi tana nadamar shan magungunan da tayi ta yi kamar ba’a nuna mata illar hakan.

Satin su d’aya a asibitin inda ya kama ranar suna yaro yaci suna Al’amin suna kiran shi da Amir gashi kyakyawa sai dai idon nashi duk da aikin da akayi an cire abun amma be koma normal ba sai yayi kamar harara garke, Sumayya kam jinya biyu take yi hakan yasa duk ta koma kamar ba ita ba ko tashi bata yi sai dai a temaka mata hakan yasa rainan yaron duk ya koma kan K’arama ko school taje hankalin ta na gida data dawo zata d’auke shi ta goya domin tana masifar son taga tayi goyo tana aiki.

Da yake gidan Madre suka koma hakan yasa ana kula da Sumayya sosai da beeba taje ta ganta dariyar zuci ta dinga yi mata tana fatan Allah yasa ma ta mutu ita kuma sai ta auri Ma’aruf uban girman kai yadda beeba ta samai sunan kenan dan kwata-kwata yak’i sauraronta bare yaji da abinda taje.

Kamar kullum yauma K’arama na zaune a wani corridor kayan Amir take wankewa dan ta hana a bawa kowa ita keyi mishi ta goge mai, gefen ta Udutti ce ke home work tana tambayar ta idan ta bata amsa saita rubuta a haka Ma’aruf ya shigo ya same su. Udutti ya kalla tare da fad’in.

“Udut come here… !

Da sauri ta mik’e tak’arasa wajan shi tare da cewa “papa good afternoon how is you’re work?!” Murmushi yayi yana shafa kanta sannan yace,

 "Jeki canza kaya kizo muje park ke da aunty me kyau...."

Kasan cewar haka Udutti ke kiran K’arama tun tana k’arama taji wasu yara na fad’a shi kenan itama ta ci gaba shi har yanzu ta kasa denawa Sumayya tayi fad’an harta gaji itama watarana haka take kiran K’arama dashi. Udutti na tafiya shi kuma ya matsa wajan K’arama ba karamin kyau tayi ba cikin riga da zani kalar atamfar peance green light yayi mata kyau d’inki kirjin nan dai-dai da yanayin jikinta beyi yawa ba sannan beyi kad’anba.

Gabaki d’aya kunya ta rufe K’arama dan tun ranar da abun ya faru bata bari su had’u, ko makaranta da sun shirya zasu gudu drive ya kaisu da taji shigowar shi kuwa zata b’oye dan bata son suna had’uwa kunyar shi take ji sosai.

"Jiki d'akko mayafi muje mu dawo sai ki k'arasa wankin sa kai... *!*"

Da kyar K’arama ta iya magana cikin sanyin muryarta tace,

 "Uncle sai dai kuje kai da Udut ni dana gama karatu zanyi kaga gobe zamu fara zana waec..."

"I said kije ki d'akko hijjab ku ba kya ji."

Tsam K’arama ta mik’e tare da tsame hannunta daga cikin ruwan wankin, kusa da kufar shiga parlorn ya tsaya tana zuwa tad’an tsaya ba tare da tace mai ya matsa ba a tunaninta ko shiga zaiyi sai taga ya d’an matsa alamar ta wuce, hanyar tabi da kallo tasan inda zata wuce toh dole saita gogi jikin shi ita kuma bata so.

"Zoki wuce mana ku nake jira fa."

Ma’aruf ya fad’a cikin basarwa yana latse-latsen waya, a hankali taje ta rab’a amma duk da haka saida ta goge shi tana shiga ya cafko hannunta ya rik’e yana bin ta da wani fitinannan kallo wanda shi kad’ai ne yasan ko na meye.

Bata juwa ba ta fara kokarin kwace hannunta basu zata ba kawai sukaji muryar Sumayya daga nesa.

"Yaya Ma'ar what d he'll is this?!"

Da sauri ya saki hannun K’arama sai wani cika yake yana batsewa had’e gira yayi K’arama ta ruga d’aki zuciyar ta na harbawa dan tasan yau sai taci masifa wajan Sumayya,

  "Yaya wai meke faruwa ne?!"

Ya kuma had’e fuska dan karta kawo mai raini yace,

 "Ko kema fitsarar zaki min kamar yadda itama take son yi min?!"

Ya fad’a kamar da gake, jin abinda yace gashi sai faman kumbura yake yi yasa Sumayya tab’e baki ta nufushi, jikinshi ta fad’a ya d’agota yana kallonta ganin ba damuwa yasa shi cewa,

 "Unguwa zamu rakiya zasu yi min."

Lokacin sun fito Sumayya ta kalli Ma’aruf “zuwa ina kuma?!” Yace “park zamu zan karbo wani sako.” “A can park d’in zaku karb’o sakwan?!”

Juyawa yayi ya fara tafiya yana cewa “Ehh shi yasa ma nace su rakani idan munje su suyi wasa kafin na gama abinda ya kaini, ku kuwuce mota.”

Duk iya kokarin ta na ganin ta gano wani abun bata gane ba hakan yasa tayi musu bye-bye tanajin tamkar aje da ita dan haka kawai bata yadda dasu ba dukkan su.

hafsma’ar

love you all

hajjafeedohm

FEEDOHM????
&
HAJJA CE????
???????? ABUNDA KE B’OYE……
《Almost True Life Story》

               ????????
                  ????

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM????
&
K.A.S.Precious HAJJA CE????

   *SADAUKARWA……*

HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu

      Page *83*

Yawo suka yi sosai ya kaisu gurin shak’atawa da daya duk inda suka je barin su yake yi ya zauna a gefe yana yi musu video cikin jin dad’i.

Hotona kuwa yayi musu shida K’arama yafi ashirin shida ba son yin su yayi amma yau sai da yayi son ranshi, sai wajan karfe 9:00pm suka koma gida da kayan kwalan da makulashen da ya siya musu.

[[ ]]

Cikin d’an lokacin ne ya kasa danne son da yake mata sam ko kad’an baya so ya d’auke idon shi a kanta idan tana guri ga wani irin feelings da yake ji a kanta kamar zai kashe shi !Da yake har lokacin Suna gidan su Madre ya samu ya fad’a mata zasu je garin su K’arama saboda shima zai je aiki a can don haka zai tafi da ita har ya gama aikin sai su dawo tare, bai samu matsala ba gurinta sai ta masu fatan dawowa lafiya, ita ta had’a masu komai na tsarabar da zasu kai masu…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button