ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ranar da zasu tafi Tun da asuba Sumayya ta saka rigimar wae sae an tafi da Udutii tunda hutu suke Ma’aruf yace bazasu tafi da ita ba amma K’arama sai tace “Uncle Tafiyar da Udutti zai k’ara maka wani nauyi ne?please dan Allah mu tafi da ita…!”
Gyad’a kai kawai yayi sannan aka shirya Udutti cikin irin na K’arama sai kayanta pakistan kalar jah kamar yadda K’arama ta shirya aka zuba mata ‘yan kayanta a cikin jakar K’aramar, har parking lot su Madre da sumayya suka rako su hannun Madre d’auke da Amir, A Gaban mota suka zauna su duka biyun sannan suka d’auki hanyar zuwa Katsina…
Udutti ke ta zuba surutu ita kadai yayin da K’arama ta mayar da kanta jikin window ta lumshe ido kamar mai yin bacci.
Ma’aruf kam daga “Huh” “Uhum” Eh! A’a” yake amsa mata yayin da yake satar kallon K’arama duk bayan second…
Da yake gudu yake yi sosai karfe 2:45pm suka isa Crc ko gidan hakimi baije ba ya d’auki hanyar kauyen su K’arama.
Da sauri ta kalleshi yayin da gabanta ke fad’uwa wanda ta rasa dalilin a hankali tace “Uncle.!”
Cikin kulawa Ma’aruf yace “Na’am Hafsah…”
Shiru tayi tare da sadda kai k’asa Udutti ta saki hamma ganin sun yanka cikin daji tace “papa bush zamu shiga mu kamo lion?”
Kallon juna suka yi shi da K’arama ya sakar mata wani lallausasan murmushi sannan yace ma Udutti “Zaki dai iya kamo lion din ko?
Tabe baki tayi tana kallon K’arama sannan tace “papa kasan film d’in joda?”
Gyad’a mata kai yayi yana kallon hanya tace.
“Yauwa toh Irin Murmushin kake yiwa Small Mom inka!”
Waro ido yayi yana kallonta lokaci guda ya kalli K’arama da ta waro ido itama tana kallonta cike da mamaki sannan ta sunne kai tana dariya k’asa k’asa…
Hararanta yayi cike da sonta sannan ya kalli Udutti dake ta murza point d’in phone d’in shi yace “baki ga tana kama da joda in ba itama…?!”
Kallon K’arama tayi kamar yau ta tab’a ganinta sannan ta saki dariya tana gumtse bakinta dan karta fito sosai…
Suna zuwa garin su Maitafasa K’arama ta runtse idonta tare da kwantar da kanta saman cinyarta Ganin yanayinta ya sashi yin parking a dae-dae kofar gidan Maitafasa kafin su fito mutane har sun kewaye motar…
Udutti ta kalli Ma’aruf tace “papa basu tab’a ganin motor bane?”
Tab’e baki yayi ya juyar da kai ya hango Maitafasa tana kokarin fitowa daga gidan d’aure da d’aurin gaba tana watsa hannun ta a baya duk da baya jin me take fad’a amma ya tabbatar da cewar bala’i take…
A hankali ya kalli K’arama yace “Mu fita ki gyadar da kakarki…”
Saurin d’agowa tayi tana kallon shi da mamaki lokaci guda ta kalli Maitafasa gaban ta yayi mummunar faduwa bata san lokacin da ta rungumeshi ba tana fad’in “A’a Uncle dan Allah mu tafi mu dai karta yi min fad’a…”
Bayan ta ya shafa ya d’aga kai a hankali yana kallon mutanen dake lekowa ta glass suna kallonsu yayi k’asa da kai yace “Ina tare dake Hafsah Bazan bari wani ya cutar dake ba Hafsa!Ki fita ki gyadar da ita ko baki yarda dake Jikarta bace kema?
Shiru tayi tare da d’aga kai tana kallon shi saurin janye jikinta tayi ta matsa jikin door d’in tana kallo waje Udutti da ta matse ta saka hannu ta b’angarenta ta bud’e kofar kafin tayi magana ta fice yayin da Ma’aruf ya bi bayanta shima…
Idonta ya ciko da kwalla ta bud’e kofar a sanyaye ta fito… Gurin yayi d’im suna kallonsu yayin da Maitafasa ta kafeta da ido kamar an tsikareta kuma ta matso kusa da ita ta saka bakin hannunta ta d’ago Fuskar K’arama tana kallo jikinta na rawa…
Sakinta tayi ta koma baya tayi zaman ‘yan bori ta saki wani irin ihu tana fad’in,
“Ta kwarankwatsa wannan yarinyar d’iyar ladona ce!Yau na shiga uku ni Maitafasa…”
Jiki a sanyaye K’arama ta matsa tare da tsugunnawa kusa da Maitafasa ta dafa cinyarta tana kallonta da idanunta da suka ciko da kwalla tace “Kiyi hakuri dan Allah ki tash…”
Wata zabura Maitafasa tayi wadda tasa K’arama firgitar da sae da tayi baya ta zauna a kasa tana kallon Udutti da tayi gurin mutanen tana tambayarsu “Wae me suke kallo a jikinsu?
Wata wawar runguma Maitafasa ta kaiwa K’arama tare da sakin kukan ‘yan bori tana fad’in.
"Ta kwarankwatsa jikata ce 'yan nan Sak ladona!Na tuba Hafsatu ki yahe man tallahi na yarda ke jikata ce,babu yarda za'ai ki d'auko kamannin Ladona in dae ke ba jinin,shi bace Na yarda aradun Allah duk wani munahurci toh bakar munafukarcan ta had'ashi…"
Cikin gida ta ja hannunta suka shiga nan da nan mutane suka bisu kai kace wani mai mulkinne yaje kauyan.
Abun Allah sae gashi har da Maitafasa aka je kauyen su Hafsuwalle ta saki jiki sosai sai labarin Kundum takewa K’arama wanda tsabar mamaki ya hana K’arama cewa Uffan Ko da suka isa kauyen Ard’o baya nan sae Sallau da suka iske rik’e da d’an yaron da Lauratu ta haifa na biyu da sauri K’arama ta k’arb’eshi tana kallon Ma’aruf da ya kafeta da ido ganin bakin yak’i rufuwa ya sashi murmusa, Udutti kam gurin sauran yaron Lauratu ta nufa suka cigaba da wasansu kamar ta dad’e da sanin su Yayin da Hafsuwalle da sauran mutanen gidan suka k’arbi K’arama hannu biyu biyu saboda sak ta canza tamkar ba danginsu ba ga wani kwarjini da tayi wanda karyar mutum ya iya had’a ido da ita ya fad’a mata ba dad’i…
Ma’aruf kam bukkar Ard’o sallau ya kai shi sannan ya zagaya can bayan gida ya kira Ardo!cikin sauri ya zagayo yana cewa,
“Maraba lale da mutan binni.”
Karo yayi da Maitafasa ta tsayar dashi tana bashi hakuri da yake bai kullace ba sae yayi dariya yana fad’in “Wallahi Allah ba komae.” Yayi gaba ya shige bukkar sa gurin Ma’aruf cikin mutunci suka gaisa ya saka aka kawo mashi dambu da madarar shanu tare da ruwan randa mai sanyi…
Hafsuwalle kam baki yaki rufuwa bama kamar lokacin da yara suka fara shigo da tsarabar da su K’arama suka zo da ita taga mutanen gidan sae washe baki suke suna sakawa K’arama albarka wanda bata tab’a tunanin zasu samu hakan ba a gurin mutanen gidan… Ita kanta K’arama ta saki jiki don har wanke wanke ta taya Zulai yaran gidan kam bata kyamaci kuwa ba acikin su duk da yarda suke duku duku haka take rungumarsu cikin tsantsar mutunci!
Sae kusan Magrib sannan Ard’o ya shigo gidan ya kirata suka koma bukkar sa a tare dashi kafin ya shiga ya hango Udutti tana dambe da jikan zulai akan goriba ya matsa yana rabasu…
Ganin Ma’aruf zaune ya sata komawa gefen shi ta zauna tana kallon shi tace “Uncle Ka ci abincin mu kuwa?
A Hankali ya girgiza mata kai yana waro ido waje…
Cikin kulawa tace “Me yasa?ko baza ka iya cin abincin mu bane?
Gyad’a mata kai yayi yana kallon yarda ta kwantar da kai tana kallon shi…Ga mamakin,shi kuma sae ganin hawaye yayi kwance a idonta yayi saurin ware ido yana fad’in “Kuka Hafsa?Kinga wasa nake duk abunda zaki iya ci zan ci shi kin ji ko?na ci sosae kuma ya man dad’i…ki koya kafin mu koma gida kinga sae ki dinga min ko?ya karashe maganar tare da kanne mata ido d’aya.
Zaman Ard’o ne ya sashi yin shiru tare da barin kallonta…Cikin natsuwa Ard’o ya fahimtar da ita Matsayin Ma’aruf gurinta tunda ya fara maganar kanta na k’asa ta kasa dagowa har sae da ya kai aya sannan ya d’auko sadakin ta da tunda aka bashi gidan hakimi ya zo ya boye ko kud’in bai canza ba ya dan da zai yi mata kiwo ya fasa dan yasan sacesu za’ayi. Ya matso ya mika mata kin karb’a tayi har sae da yace “Hafsatu sadakin mace hakkinta ne ki karb’a dan girman Allah ki rabani da azabar Allah domin cin kud’in Sadaki ba karamin bala’i bane.”
Hannunta na kyarma ta karb’a ta aje k’asa mikewa yayi ya fita ya bar su kadae a hankali ta runtse idonta tana tuno duk abunda ya faru a baya har lokacin da Ma’aruf d’in ya tambayeta a bainar jama’a ko zata aure shi, zuciyarta na harbawa jikinta na rawa ta fara tunani (kenan abunda ya fad’a kwabaki gaskiya ne, amma me yasa aka rufeta, me tasa lokacin da yaya Maryam ta gansu bata gaya mata gaskiya ba sai ma kwana-kwana da tayi mata? Allah kad’ai masani sai kuma su)…