ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani lallausan murmushi ya sub’uce mata sam bata yi nadamar hakan ba ita kanta tasan Uncle wani haskene a cikin rayuwarta to me yasa yake wani b’oye b’oye?Lumshe ido tayi sama ta rigaya ta manta da Ma’aruf dake zaune kusa da ita hannun shi taji saman fuskarta ko bata bud’e ba tasan kallonta yake yi…

Dukkan hannuwan shi ya saka ya tallabo fuskarta yayin da ya aika mata da wani yalwataccen murmushi kamar mai rad’a yace “Kin amince dani a matsayin mijinki?ya karashe maganar tare da had’e fuskarsu guri d’aya,

Kafin ya sake magana suka jiyo Muryar Udutti ta shigo tana fad’in “Lah lah papa Me kake yi mata?

Bai d’ago ba haka bai janye fuskarshi ba kusa da tata sae ma kissing da ya bata a saman eyelashes inta yana fad’in “No Wani abu ya fad’a mata nake cire mata.”

Kusa da su ta matso K’arama na kokarin janye fuskarta amma ya riketa sosae a hankali tace “Please Uncle ka daina mana…”

Udutti tace “Abba kamar Muahh! naga ka mata a Idonta!

Still kiss ya kuma mata a idon sannan yace “A Idon ya fad”a ai Udutti.”

Tab’e baki tayi ta juya tana yarfa hannu ta fita da sauri K’arama ta tureshi ta tashi da gudu ta fita daga cikin bukkar… Cak ta tsaya a bakin bukkar tare da dafe kirji tace “Na shiga uku Aunty Sumayya… !

Karaf Udutti ta amshe da fad’in “Me Mami na tayi Aunty Mai kyau?

Kallonta tayi da sauri ashe tana bakin bukkar tana kwalkwalar k’asa tana wasa bata ce mata komae ba ta d’agata suka shige bukkar Inno inda su Ummanta suke…

Ma’aruf kam kud’in da ta aje ya d’auka yana murmushi ya fita a bakin icce ya iske su Ard’o tsaye yana magana da Maitafasa duk da ba fad’a take ba amma tana yi tana watsa mashi hannu a fuska wae kuma hakuri take kuma bashi…

“Allah ya kyauta…”

Ya fad’a tare da girgiza kai ya matsa kusa da Ard’o Kanshi Maitafasa ta koma tana bashi hakuri gyad’a mata kai yake don har ga Allah ta ishe shi da kwaratsi tare da watsa hannu a saman jikin shi…

Kud’i ya ciro ya bata sannan ta tafi tare da rafka masu albarka tana musu faran alkairee ya juya yana fad’awa Ard’o zai tafi zuwa sati d’aya zai dawo ya tafi dasu tun da shima akwae abunda zai yi a katsina wanda yake tunanin zai kai shi sati d’ayan…

Fatan alkhairi Ard’on ya mashi suka rakashi har bakin mota shi da sallau ya shiga har zai tafi Ard’o yace Sallau ya kira su K’arama suyi bankwana kafin ya tafi!shi kanshi Ma’aruf d’in yaji dad’i sae dae bak’in cikin shi d’aya yana iya ganin duka mutanen gidan sun fito suna kallonsu…Haka kam akayi kusan duka mutanen gidan ne a bayan K’arama kamar su aka kira.

Girgiza kai yayi cike da takaici yana kallon K’arama da ta toge tak’i k’ara sowa gurin da yake, A Hankali ya tab’e baki ya mikawa Udutti hannu amma ta makale kafad’a tare da rike hannu inno tana kyafta mai idanu…

Kallon K’arama ya kuma yi suka had’a ido ya kashe mata ido d’aya tare da d’aga masu hannu ya tayar da motar shi, Duk abunda yayi mutanen garin idonsu na kanshi don haka yana tayar da mota suka d’auki gud’a “Ayyyiriri……!!”

【】

Cije baki tayi tare da dafe gefen cikin ta dake ta murd’awa ta kalli Madre tace,

“Madre ina so na tambayeki ne…”

Shiru tayi tana jinjina maganar a bakinta lokaci guda kunyar madre ta dirar mata dan tambayar ta kunya ce…

Cikin kulawa Madre tace “Menene Sumayya?

K’asa tayi da kanta sannan tace “Madre wani yellown ruwa ne ke fitowa ta kasana kuma ya fara wari-wari.”

Da sauri ta kalleta tana fad’in “Yellown ruwa Sumayya a Vagina inki ko ina?

Shiru tayi tana kallon k’asa cikin tsawa Madre tace “Bakya jina ne tun yaushe yake fitowar?

A Hankali tace “Yafi Ten month gaskia Madre kuma a tunani na ni’ima ne wallahi to kuma ya fara wari shine nake so na tambayeki dama idan ni’ima tawa mace yawa tana irin wannan warin…?!”

Uban Mari Madre ta bata tana aika mata da wani mummuna kallo kafin tace “Ashe baki da hankali Sumayya?

Dafe inda ta mareta tayi ta saki kuka tana fad’in “Me nayi Madre?

Shigowar yaya Maryam ta hana Madre bata amsa ta mike ta bar masu d’akin Maryam d’in ta tambayi Sumayyan me ke faruwa bata b’oye mata komae ba tace “Wani ruwa ne fa ke fitawa a vagina ina wallahi yellow haka da bayya da wari amma yanzu wari yake sosai shine nake fad’awa Madre ta mareni.”

Girgiza kai Yaya Maryam tayi tace “Amma tun yaushe yake fita Sumayya?

“Kusan wata goma kenan.” ta fad’a kai tsaye tana turo baki

A Hankali tace “Shine baki fad’awa Madre ba kuma ko?Ko shi Brother ya sani?

A Hankali tace “Ban fad’a masa ba don na d’auka ma ni’ima ne…”

Tsaki ta saki ta mike tace “sai ki ta tashi muje je asibiti.” kafin ta shirya ta shiga gurin Madre ta fad’a mata ita dae Madre takaici yasa tace “A Dawo lafiya.” tayi banza da Maryam d’in……

Ko da sukaje asibitin laboratory aka ce taje ayi mata test…wata sister a kace ta d’auki sample d’in dake fitowa sheath d’inta wari-wari gurin keyi da kyar sister in ta d’auka akace su jira kafin result ya fito.

Kusan one hour sannan sister d’in ta fito rike da result d’in ta nufi office d’in wata doctor Safiyya suka bi bayan ta suma…

Ita kanta Doctor Safiyya rasa wace irin cuta ne a Vagina d’in tayi don result ya bada ba infection.. Tambayarta tayi abunda ta ke ji a tare da ita…

Ba tare da damuwa ba tace “Discharged ne kawae sae bleeding da nake kad’an-kad’an wanda is not related to menstrual (Fitar ruwa ko jini wanda baya da alaka da al’ada)……

hajjafeedohm love

HAJJA CE????
&
FEEDOHM
???????? ABUNDA KE B’OYE……
《Almost True Life Story》

               ????????
                  ????

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM????
&
K.A.S.Precious HAJJA CE????

   *SADAUKARWA……*

HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu

      Page *84*


Ba tare da damuwa ba tace "Discharge ne kawae sae bleeding da nake kad'an-kad'an wanda is not related to menstrual (Fitar ruwa ko jini wanda baya da alaka da al'ada)……

A Hankali doctor d’in tace “Kina jin Pain during sexual intercourse?!” (kina jin Zafi yayin saduwa da miji?!”)

Gyad’a kai tayi tace “Eh amma ba kullun ba.”

Kallonta ta kuma yi tace “Pain when urinating?” (Zafi yayin fitsari)!Still Sumayya gyad’a kai tayi doctor d’in tace “Akwae pain in pelvic area?Still gyad’a kai tayi.

Yaya Maryam tace “Menene Matsalar? Natsuwarta ta dai-dai ta sannan tace “It seens kamar Adenocarcinoma (Vaginal Cancer).”

A Tare suka mike suna fad’in “Menene?!” Itama mikewa tayi tace “Please ku zauna Calm down Having these symptoms does’nt always means that you have Vaginal cancer infact these symptoms are more likely to be caused by something, beside cancer like an infection the only way to know for sure what causing these problem is to test you Sister kawae na fad’a ne amma banda tabbaci saboda inda infection ne a first result d’inki zamu gani…!” (Ki kwantar da hankalinki Wad’an nan alamomin basa nufin kina d’auke da cutar daji ta farji, kawae wad’an nan almomin sunfi kama da na wadda ke d’auke da cutar sanyi ne, hanya d’aya ce da zamu tabbatar da abunda ke damunki shine mu yi maki gwaji, kawae na fad’a ne saboda da ciwon sanyi ne da tun a sakamakonki na farko zamu gani).

Su dukan su jikin su yayi sanyi bama kamar Sumayya da ta shiga cikin tashin hankali kawai ta saki kuka tana girgiza kai cike da tashin hankali da damuwa mai yawa. Doctor d’in ta kwantar masu da hankali sosai…

Laboratory ta kuma turata tace a mata Pelvic Exam ,PAP test & Calposcopy a gani… da yake suna da kayan aiki a take nurse d’in ta kwantar da Sumayya aka mata Pelvic exam d’in tare da Pap test suka d’auki sample na cell d’in dake a jikinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button